Almizan :Jiragen saman Nijeriya ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 15 Zulkidah, 1426                 Bugu na 696                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Jiragen saman Nijeriya

Sun zama Akwatunan gawa

Daga Musa Muhammad Awwal

A halin da ake ciki dai za a iya cewa jiragen saman Nijeriya suna neman su zama akwatuna ne kawai na gawa ganin yadda hadarin jirgin saman yake neman ya zama ruwan dare a kasar nan.


.

Wani bincike ya nuna cewa daga shekarar 1960 zuwa yau, an sami hadarin jirgin sama kimanin 39, wanda kuma aka yi asarar rayuka fiye da dubu daya.

Na baya-bayan nan dai shi ne wanda ya faru a ranar Asabar da ta gabata na kamfanin jiragen sama na SOSOLISO wanda ya fadi a Fatakwal, kuma mutane 109 suka rasa rayukansu, akasarinsu dalibai ’yan wata makaranta da ke Abuja, Loyola Jesuite College.

Da yake wannan abu yana da yawa ba za mu iya kawo su duka ba. Amma dai akwai wadanda ba za mu taba mantawa da su ba.

Misali a kwana-kwanan nan ba a jima ba aka yi mummunan hadarin jirgin na kamfanin bELLVIEW wanda ya fadi a kauyen Abi cikin jihar Ogun, inda duk mutane 117 da ke cikin jirgin suka rasa rayukansu.

Haka kuma akwai wanda ya faru a Kano, wanda ya fado a kan gidajen jama’a inda aka yi asarar rayuka da daman gaske.

Akwai kuma mai ban tausayin da ya faru a Sakkwato, inda wani jirgin mahajjata ya fado yayin da ya zo sauka bayan ya dawo daga Jiddah, wanda shi ma duk mahajjata sama da 400 da ke ciki suka rasa rayukansu.

Duk wadannan hadarin, da ma wasu da dama, ana ta’allaka faruwarsu ne a sakamakon jiragen da ake shigo da su kasar nan wadanda wasu ke zargin cewa ba masu lafiya ne ba. Ana shigo da su ba tare da an yi cikakken bincike a kan lafiyarsu ba.

Yawancin wadannan jirage sun fi shekara 25 da kerawa. Kuma sun zama bola a kasashen da aka kara su. Amma irin su ne aka tarkatowa ake kawo wa kasar nan. bai kamata mu zama jujin zubar da tsofaffin jirage ba, “Akwatunan mutuwa,” kamar yadda wani Minista ya taba yi masu suna.

A halin da ake ciki dai wasu da dama sun sauya daga shiga jiragen sama a kasa saboda tabarbarewa lamarin.

Sannan kuma irin wannan yawan samun hadarin jirgin zai iya samar da rashin aminci ga shigowar baki ’yan kasar wajen zuwa kasar nan, musamman masu san shigowa don kafa wasu masana’antu ko wasu harkokin hada-hada wanda zai zama asara ne ga ’yan kafa.

Saboda haka ne ake da bukatuwar cewa ya kamata a yi wani habbosa don ganin an inganta harkokin sufuri a kasar nan. A kula da jiragen sama da ake shigowa da su kasar nan wadanda su ma a turance suka zama ‘death Trap’.

Akwai wani lokaci da filin saukan jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Legas ya lalace, wanda sai da jiragen sama na kasar wajen masu sauka a filin suka yi barazanar janyewa daga filin, sannan kwanan nan aka gyara filin.

Wannan kenan ya nuna cewa gwamnatin kasar nan ke da alhakin duk asarar da ake yi ta wannan fanni saboda halin ko-in kula da take nunawa.

Wani abin lura kuma shi ne son zuciya kawai ake nunawa a kasar nan ba neman gyara ba. An cire Alhaji Isa Yaguda daga Ministan sufurin jiragen saboda laifin wai shanu na ratsawa ta filayen jiragen saman Fatakwal, kuma hakan na haddasa hadarin jiragen.

Nan da nan aka nada Farfesa babalola borishade, wanda kuma yau da nada shi an sami hadarin jiragen sama munana har guda uku, amma shi ba a ce ci kanka ba. Shi kuma bai yi fushi ya yi murabus da kansa ba.

A wata sabuwa kuma Shugaban gwamnatin farar hular Nijeriya, Cif Obasanjo ya dakatar da babban Sakatare na Ma’aikatar sufurin jiragen sama kasar nan, Mista T.D Oyelade da Daraktan tsare-tsaren na Ma’aiktar, Mista Esai Dangabar.

Haka kuma Obasanjo ya dakatar da kamfanonin jiragen sama na SOSOLISO da CHANCHANGI Airlines daga sufurin jiragen sama a kasar har sai an tabbatar da lafiyar jiragensu. Kuma mako guda ne aka ba su don wannan aikin tantancewa.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International