Almizan :Ba za mu yarda Obasanjo ya zarce ba ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 15 Zulkidah, 1426                 Bugu na 696                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Ba za mu yarda Obasanjo ya zarce ba

In ji Kungiyar Izala ta kasa

Kungiyar Izalatul bidi’a wa Ikamatu Sunna ta kasa bangaren Kaduna, ta jadadda matsayinta na kin yarda da duk wani shiri da ake yi na yi wa tsarin mulki kwaskwarimar da zai bai wa Shugaban gwamnatin farar hula, Cif Olusegun Obasanjo damar zarcewa a kan mukaminsa.


A jawabin bayan taro da Kungiyar ta fitar bayan taron wa’azi na wuni uku da ta kira a filin masallacin Idi na Sultan bello da ke Kaduna a karshen mako, Izala ta ce a ta kowane hali ba za ta taba yarda da duk wani shiri na sake bai wa Obasanjo damar ya zarce ba.

Da yake bayani ga mahalarta taron, Shaikh Yakubu Musa Hasan Kafanchan ya ce, Kungiyar za ta sa kafar wando daya da duk wani mutum daga nan Arewa da yake goyon bayan wannan shirin na zarcewar Obasanjo, “ba za mu yarda ya zarce ba. Za mu ci gaba da cewa ba mu yarda ba. Kuma ta kowane hali za mu yi wa al’ummar Musulmi bayani da kada su yarda wannan gwamnatin ta kafirci ta sake zarcewa.”

Shi ma da yake yi wa ALMIZAN karin haske bayan kammala taron, daya daga cikin jiga-jigan Kungiyar na kasa, Shaikh Sa’idu Alhasan Jingir, ya bayyana cewa; “makasudin shirya wannan taron shi ne domin mu tunatar da junanmu, mu kuma sada zumunci a tsakaninmu, mu kuma shaida wa duniya cewa duk wani rade-radi da ake yi na maganar ta-zarce, Kungiyar Izalatul bidi’a wa Ikamatu Sunna ba ta ciki. ba ruwanta da abin da ya shafi ta-zarce.”

Shaikh Alhasan Sa’idu Hasan Jingir, ya yi watsi da jita-jitar da ake bazawa cewa ba su yarda da shirin sulhun da Dakta Ahmad Gumi ya bullo da shi ba. Ya ce, “wa zai ce ba ya son sulhu, bayan Allah ya ce sulhu shi ne alheri, kuma ya ce ku ji tsoron Allah ku sulhunta tsakaninku? Ya kuma za mu ce ba ma son sulhu bayan kuma mun san Allah ya ce a yi? Muna son sulhu, muna goyon bayan sulhu, kuma muna kira a kan sulhu, mun tara jama’armu don sulhu, sannan muna gaya masu magana a kan sulhu. Muna kwanciya da tashi da batun sulhu. Muna bukatar a yi sulhu. babu wani dalilin da zai sa mu ce ba ma son sulhu. Sai dai a bi hanyar da ta dace.”

Shaikh Jingir ya ce, duk wata matsala da aka samu a sakamakon yunkurin sulhun Kungiyar Izala da aka yi, ya biyo bayan wani shiri ne da wasu mutane suka shigo da shi cikin al’amarin da wata manufa, “wasu sun shiga (wannan al’amarin) da nufin su ci wa wasu Malamai mutunci, mu kuma a matsayinmu na manya wadanda aka kirkiri Izala da su, muka ga cewa ba mu yarda ba, dole ne duk abin da za a yi, a yi shi gwargwadon yadda ya dace da shari’a. Kada a ci mutuncin wani, kuma kada a tsangwami wani. Sannan kuma mun ba da sharudda. Idan za a yi sulhu tsakanin mutane biyu, sai kowanne yana nan a wajen ko da wakilinsa. Wadannan sune dalilan da mu muke a kai. Amma idan an bi wadannan har gobe muna kan a yi sulhu.”

Shi kuwa Shaikh Abubakar Imam Ikara, ya bayyana wa ALMIZAN ne irin nasarorin da ya ce taron nasu ya samu. “Wannan taron da muka yi ya ci nasara kwarai da gaske, saboda dalilai da dama. Kafin mu zo wannan wa’azi an yi ta watsa maganganu wadanda ba su yi daidai da shari’a ba. Amma yanzu duk wanda ya halarci wannan wa’azin, ko ya saurari abubuwan da aka fada, idan ya je ya yi wani abu wanda ba daidai ba, da gangan ya yi domin ya samu shiriya.”

Wata nasara da wannan taron ya samu, kamar yadda Shaikh Ikara ya bayyana shi ne, “wasu suna dauka kamar Malaman wannan Kungiya (Izala) kansu ba a hade yake ba, yanzu duk wani Malami a Kungiyar nan an gan shi a nan, ko da ka ji sunansa a wani waje yanzu muna tare a waje daya. Ashe wannan ya nuna Malaman dukkansu a dunkule suke, masu fadin ba sa tare, sune ba su fahimci Malaman ba.”

“Yin taron da aka yi lafiya aka tashi lafiya shi ma wata nasara ce,” in ji shi, “musamman da yake hakan ba shi ne burin wasu ba.”

Ya bayyana ’yar hayaniyar da aka yi a wajen taron, inda har wasu mutane da ba su gamsu da abubuwan da ake yi ba suka dan yi jefe-jefe da duwatsu a cikin kwaryar taron, da cewa ba wani abu bane, “domin duk lokacin da ka tara kwakwale suka yi yawa zai yi wuya a yi abin da yake daidai. Sad da aka zo, wasu sun dauka an zo ne a mai da martani, ko a zagi wasu, ko a bata wa wasu. ba su san abin da ake nufi ba, sai suka yi garaje, suna ganin kamar an fusata a kansu ne, za a zo a baje koli a kansu, amma ba su san ba wannan ne manufarmu ba, shi ya sa suka dan tagaza ta yadda za a san sun zo,” in ji shi.

Da yake mai da martani game da zargin da wasu suke yi masu na cewa sun ki halartar taron sulhun da Dakta Ahmad Gumi ya kirkiro, Shaikh Abubakar Imam Ikara cewa ya yi; “Dakta Ahmad Gumi ba shi ya kirkiro sulhun wannan kungiya ba, akwai Gwamnoni da Sarakuna guda hudu, da suka hada da na Dutse, Kazaure, Suleja, birnin Gwari da Hadeja, duk sun yi yunkuri a kan wannan shirin sulhun tuntuni. Kuma idan ana maganar sulhu a dauke ta daga cewa wane ne ya kawo, don magana ce ta Allah. A Musulunci bayan kalmar shahada ba abin da ya fi haduwar mutane waje daya muhummanci, don haka duk inda wasu Musulmi suka rabu, duk Musulmin kirki ba zai ji dadi ba, ba zai so ba. Wannan shi ne gaskiyar magana. Wannan kiran da Dakta Ahmad ya fara, kira ne na Allah, kira ne da wasu manyan mutane suka riga shi farawa.”

Don haka ya yi watsi da zargin da wasu suke yi na cewa sun kauracewa taron sulhun da ake yi, ya ce, “ba mu taba kauracewa neman yin sulhun da ake yi ba, an yi taruka har a wajen kasar nan sau biyu, kuma da mu aka yi, wannan da ake yi mun nado wakilai mun tura su wajen, kuma Musulunci ya yarda da wakilci.”

Sai dai duk da haka ya ce, ba yadda za a yi su yarda da wani shirin sulhun da aka kira shi a karkashin makiya Kungiyar Izala, wadanda suka san sun dade suna yi mata zagon kasa, “kai idan kana da hankali, ba wai sulhu ba, ko shawara za ka nema gun makiyinka? Wanda ya dauko makiyinsa ya ce ya yi masa sulhu, ai ya ce ne ya kara fadan. Duk mutanen da ke wannan hayaniyar ba ’yan Izala bane. ’Yan Izala wannan rabuwar ta dame su, amma dama wasu Izala ta dame su sun rasa yadda za su yi da ita, suna neman ta ina za su gama da ita?”

Ya ce a iya saninsa Izala ba ta rabu gida uku ba kamar yadda wasu suke yadawa, “Izala tana nan yadda ka san ta. Malamai ne kawai za su iya raba Izala su falle su ci gaba da wa’azinsu na daban, kuma ba wani Malami da ya yi haka. Har yanzu Izala tana nan a dunkule kamar yadda aka san ta. Wannan abin da ya faru ma ya kara mana karfin gwiwa ne, yanzu ne ma za ta kara hadewa waje daya.”

Shi kuwa Shaikh Abubakar Gero Arugungu cikin fushi ya ce, a shirye suke su ce wa duk wanda ya ce masu kule cas. Ya ce, “ba wani boye-boye ko noke-noke (ni basakkwace ne, kai tsaye nake maganata) duk wanda ya taba mu za mu rama. Mun daina yarda wasu suna ci mana mutunci da sunan nuna adawa da abin da muke yi.”

Shi dai wannan taro ya yi karo da wasu matsaloli, musamman da yake wadanda suka shirya shi, wasu mutane ne da wasu suke ganin kamar sun yi wa Dakta Ahmad Gumi tawaye. Shaikh Abubakar Gero ya ce, su ba su yi wa Dakta Ahmad tawaye ba, sai dai wasu maganganu da ya yi ne da kuma ayyukansa ne suka ce ba su yarda da su ba. “yanzu don Allah an yi mana adalci kenan, mu da muka yarda za mu zo taron sulhun a ci mana mutunci, amma kuma a lokaci guda a yi biris da sauran wadanda ba su ma yarda za su zo taron sulhun ba?” ya tambaya.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International