> Almizan:Yadda aka kashe wasu Hausawa a Aba ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 15 Zulkidah, 1426                 Bugu na 696                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Yadda aka kashe wasu Hausawa a Aba

Daga wakilinmu

“Mu hudu ne aka tare mu, ukun aka rataya masu taya a wuyan kowannensu, ni kuma babu tayar da za a rataya mani, sai wani daga cikinsu ya garzaya ya dauko fetur ya watsa mana suka banka mana wuta. Lokacin da zafin wutar ya ishe ni, sai na ruga kan titi na sake faduwa. Abin da zan iya tunawa kenan; sai dai kawai na gan ni a asibiti.”


Wadannan kalamai masu ban tausayi sun fito ne daga bakin wani bawan Allah mai suna Malam Sabo Marafa, wanda ya sha da kyar daga hannun makasa matasan Ibo a garin Aba, inda suka kashe jama’a da dama tare da sace dukiyoyi na miliyoyin Naira.

Jaridar WEEKLY TRUST ta watan Disamba 10-16/2005 ne ta je garin na Aba ta yi bincike na musamman a kan wannan lamari.

Malam Sabo ya ci gaba da cewa su dai wadancan ukun da aka rataya masu taya sun kone kurmus. Ya ce kuma lokacin da aka tare motarsu sun ga wadansu gawawwaki. “Na tabbata su ma an kashe su ta hanyar da aka kashe abokan tafiyata,” in ji shi.

Malama Sabo ya bayar da labarin yadda aka tare su. Ya ce ya shigo mota daga Jos zuwa Fatakwal ne. Suna zuwa Expressway na Aba sai aka tare su aka bincika su. “Ni da wadansu mutane uku da suka shigo daga Okigwe ’yan Arewa, aka tilasta mana mu fito daga motar,” ya ce.

Malam Sabo ya ci gaba da cewa suna saukowa daga motar, sai aka fara dukan su, aka tasa keyar su zuwa gefen hanya. Ga ’yan sanda a cikin motar, amma ba su tsinana masu komai ba. Daga nan aka rataya masu tayar aka kona.

To, amma Malam Sabo ya yi kukan cewa shi fa nan asibitin da yake hankalinsa ba kwance yake ba, domin ba ya iya barci, ga zafin ciwo, sannan ga tunanin cewa wadannan makasa za sa iya biyo shi asibiti su kashe.

Don asalin Karamar Hukumar Toro a jihar bauchi, Malam Sabo, ya yi roko ga gwamnatin jihar bauchi da taimaka ta dauke shi daga wurin ta mayar da shi gida ya yi jinya a can.

Ita kuwa wata matar aure mai suna Hajiya Kande Ubale cewa ta yi suna zaune, sai suka ji ihu ya yi yawa, kuma yana dufaro wa wajen su. Saboda haka ita da mijinta sai suka fito domin su ga ko me ke faruwa. Suna fitowa ashe matasan har sun riga sun shigo cikin gidansu.

Daya daga cikinsu ya nufi mijin da wani katon karfe zai kwantsama masa a kai. Sai na yi ta maza na rungume shi muka fadi a kasa tare. Daga nan sai wasu suka shiga duka na da mijina.

Ta ci gaba da cewa sun bincike dakinmu gaba daya sun kwashe mana kudi N73,500 VCD Janareto, mashin da lasifikar masallacinmu.”

Hajiya Kande ta kara da cewa ita da maigidanta sun sami munanan raunuka a kafa kafin a kai su asibiti.

Su dai wadannan matasa sun rinka tare babban hanyar Expressway ta Aba din ne suna tare motoci suna bincikawa tare da fitar da duk wani dan Arewa suna kashewa ko jikkatawa.

Shi dai wannan rikici ya samo asali ne a sakamakon wani labari da jaridar THISDAY ta rubuta a shafinta na biyar na ranar 19 ga watan Nuwambar da ya gabata cewa Kungiyar Musulunci nan ta NASFAT tare da hadin bakin jami’an tsaro na shirin kashe wani Shugaban Kungiyar MASSOb, Cif Uwazuruike, wanda yake tsare a hannun jami’an tsaro saboda laifin cin amanar kasa.

bayan da labarin ya bazu ne, sai wadannan matasa na Ibo suka hadu suka far ma wasu unguwannin ’yan Arewa na Aba, wato inda ake ce wa Ama-Hausa, suka jikkata da dama tare da sace masu dukiyoyi.

babban Limamin masallacin Juma’a na garin Aba, kuma Shugaban Hausawa na garin, Malam Idris bashir ya shaida wa jaridar TRUST din cewa a wannan harin dai an kashe wasu mahauta biyu tare da sace masu gasasshen namansu mai yawan gaske.

Ya ci gaba da cewa maharan sun ranta a na kare tun kafin ’yan sanda su isa wurin, don ba a kama kowa daga cikinsu ba.

Wani mai shagon sayar da kayan wuta, wanda kuma shagonsa ke kallon unguwar ta Ama-Hausa, Mista Chuka shaida wa jaridar cewa su wadannan maharan ’yan Kungiyar MASSOb ne, domin ya ji suna reja wakokin ’yan MASSOb din a lokacin da suka kai harin.

Ganau din ya ci gaba da cewa wadannan maharan sun isa wurin ne a matocin bas guda hudu shake da mutane, wasunsu suna dauke da kwafin jaridar THISDAY din da ta buga labarin, suna waka suna fadin cewa “za mu kasha ku kafin ku kasha mu!” Ya kuma ce kusan dukkansu baki ne don bai ga wani da ya sani a cikinsu ba.

A wancan asibitin da aka kawantar da Sabo Mafara kuwa, jaridar ta WEEKLY TRUST ta ruwaito cewa akwai ’yan Arewa da dama a asibitin masu raunuka daban-daban.

A asibitin akwai wani Adamu Ciroma, wanda shi ma daga bauchi yake wanda kuma yaron mota ne Tirela. An kashe direbansa kuma an lalata motar.

Akwai wani direban tanka kuma mai suna Alhaji Muhammad Sabo daga bakin Kura a jihar bauchi, amma shi ya tsira da raunuka, amma an lalata motar tasa.

Akwai direbobin tanka da dama wadanda aka kasha, wasu kuma da yaran motarsu sana kwance a asibiti suna karbar magani; amma duk motacinsu an farfasa su.

Wannan ne ma ya sa Kungiyar direbobin tanka ta kasa yin wani zaman makoki a ranar Litinin da ta gabata, inda ta umurci duk wani direban tanka ya zauna a gida kada ya fita aiki don nuna juyayinsa.

Shugaban direbobin tanka na jihar Kaduna, Kwamared Nuhu Muhammad, ya shaida wa Wakilinmu ta wayar tarho cewa sun yi haka ne don nuna juyayinsu ga ’yan uwan nasu. Ya kuma yi fatan cewa gwamnati za ta yi wani abu a kan wannan lamari.

Jaridar ta ruwaito Kwamishinan ’yan sanda na jihar Abia, Mista Adanaya Gaya yana tabbatar da aukuwar wannan lamari, inda ya ce an kashe mutane biyu. Kuma ya danganta aika-aikar da cewa aiki ne na zauna-gari-banza masu neman wata dama ta yi wa jama’a wasoson dukiyarsu.

ba a taru aka zama daya ba, domin wata runduna ta matasan Ibo din karkashin jagorancin Shugaban Kungiyar direbobin motocin haya, NURTW na jihar Abia, Kwamared Azubuke Asuso, sun fafari wadannan maharan sun kama wasu da dama, kuma sun mika su ga ’yan sanda.

Malam Idris ya shaida wa jaridar cewa hatta wasu kayayyakinsu da maharar suka sace, wadannan matasan sun kwato masu, kuma sun mayar masu da abinsu.

Malam Idris ya ce wannan Shugaba na NURTW ya taimaka masu matuka, “akwai shirin da aka yi za a rushe mana masallaci. Wannan bawan Allah, Mista Azubuke ya sanya yaransa suka tsare masallacin har sai da ’yan sanda suka zo. Haka kuma ya sanya wasu yaransa nasa su tare unguwar ta Ama-Hausa, inda Hausawa suka fara gudu, domin su tsare wajen. Ya ce mutanemu su zauna su bude shagunansu. Jama’arsa sun tsaya a wajen har sai da ’yan sanda suka zo suka karbi kula da lafiyarmu,” in ji Malam Idris.

Malam Idris ya ce Msita Azubuke ya ba su lambar wayarsa ya ce da zarar sun ji kyas, to su buga masa waya su sanar da shi.

Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa a kan lamarin, Shugaban musulmi ’yan kabilar Igbo a garin na Aba, Alhaji Musa Nyakarandam ya bayyana wannan lamari da cewa aiki ne na zauna-gari-banza jahilai.

Ya ce sun ce suna son biafra, su ’yan biafra ne, to haka ake yi? Ta hanyar kashe Hausawa ko musulmi za su samu biafran?

Ya ci gaba da cewa, “ba za ku taba samun a saki Uwazuruike da hanyar kashe wasu mutane ba. Wannan ma zai iya tabbatar da zargin da ake yi masa ne.”

Shi ma Gwamnan jihar ta Abia, Orji Uzoh Kalu ya kai ziyarar gani da ido a unguwar ta Ama-Hausa, inda ya tausaya masu. Kuma nan take ya karyata rade-radin da ake yi cewa wai ana rikici a Arewa ana kashe Ibo.

“Na yi wa duk Gwamnonin Arewa 19 waya, sun tabbatar mani da cewa babu wani rikicin a jihohin nasu. Ina mamakin yadda mutum zai dauki makami kan dan uwansu haka siddan. Wannan abin takaici ne,” in ji Gwamnan.

Gwamnan ya kuma tabbatarwa da Hausawan cewa an yi wani gagarumin shiri don tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyinsu. Don haka sai umurce su su ci gaba da harkokinsu, su sanar da ’yan sanda duk lokacin da suka ji wani abu.

Nan take kuma ya bayar gudummawa ga wadanda abin ya shafa na N300,000, shinkafa buhu 35, barguna 70, man gyada da kwanukan cin abinci.

Wani mai suna Muhammad Abdullahi daga garin na Aba wanda ya bugo waya a ofishinmu ya yi kira ga shugabannin Arewa da su kasance cikin taimakon su kowane lokaci, ba sai a bari sai an gama jikkata su ba.

A halin da ake ciki dai komai ya lafa a garin na Aba, kuma kasuwanci ya ci gaba kamar yadda aka saba.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International