Almizan :Rudami a shari'ar Saddam ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 15 Zulkidah, 1426                 Bugu na 696                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu


Rudami a shari'ar Saddam

Daga Hasan Muhammad


Ranar Litinin din makon jiya ne aka ci gaba da sauraron shari’ar da ake yi wa hambararren Shugaban Iraki, Saddam Husain bayan da a farko lauyoyin da ke kare shi suka fice daga zauren kotun don nuna rashin jin dadinsu da shawarar da Alkalin kotun ya yanke ta kin saurarensu. Sun kuma bayyana damuwarsu dangane da halascin kotun.

Alkalin da ya jagorancin zaman kotun, Rizgar Muhammad Amin ya fusata lauyoyin ne lokacin da ya hana su su yi magana don bayyana fahimtarsu ta cewa “ita kanta kotun,” a cewarsu, “haramtacciya ce.” Amma daga baya Alkalin ya bar su sun yi magana bayan da aka dawo daga hutu na minti 90.

bayan dan gajeran lokaci da aka saurari shari’ar kafin janyewarsu har sau biyu, jami’an kasar sun ce suna fatan kwanaki hudu da za a yi ana sauraron karar zai bai wa shaidu 10 da ake da su damar bayyana gaban kotun kafin a sake dage ta don ba da damar gudanar da zaben da za a yi ranar 15 ga watan Disamba.

Daya daga cikin lauyoyin, kuma tsohon Ministan shari’a na kasar Katar, Najib Al-Nuemi, ya bayyana shakkunsa kan halascin kotun. Shi ma tsohon Antoni-janar na kasar Amurka, Ramsey Clark, ya fada cewa, “matukar ba a yi adalci ba a shari’ar, to za ta raba kan kasar Iraki ne a madadin ta hada kanta.”

Daga nan sai ya yi kira da a kara tsaurara matakan tsaro ga lauyoyin Saddam bayan da aka kashe wasu lauyoyin nasa biyu a makon da ya gabata.

Masu aiko da rahotanni sun ruwaito cewa an sami rudani a yayin zaman kotun, inda lauyoyi suka rinka yi wa Alkalin kotun ihu, shi kuma yana daka masu tsawa. Shi kuwa gogan naka Saddam sai guna-guni yake yi a inda yake tsaye yana fuskantar tuhuma.

Lokacin da aka dawo zaman kotun, Alkali Amin ya tabbatar da cewa kotun za ta karbi rubutattun bayanai ne kawai a matsayin shaida, yana mai barazanar cewa in har lauyoyin suka sake fita, to zai nemi sauyin su. Shi dai Saddam da dan uwansa barazan Ibrahim al-Tikriti sun yi wasu kalamai na jaddada kaunarsu ga Iraki da kuma yin tir da sojin mamaya.

Hambararren Shugaban na Iraki tare da wasu mukarrabansa bakwai suna fuskantar tuhuma ne dangane da zargin da ake yi musu na kashe musulmi ’yan Shi’a a garin Dujail na arewacin Iraki bayan da ya gano wani shiri na yunkurin kashe shi a shekarar 1982. Kuma in har an tabbatar da wannan zargin, suna iya fuskantar hukuncin kisa.

Shaida na farko da ya fara bayyana a gaban kotun, Ahmad Hasan Muhammad al-Dujaili, ya fada cewa an tsare mutane da daman gaske a wancan lokacin kuma da dama daga cikinsu an kashe sune. “Wani abin tausayi, domin har da mata da yara aka kama aka tsare,” in ji shi. Haka kuma ya fada cewa ya ga wasu daga cikin makwabtansa da ya

tabbatar an kashe su.

Kimanin shaidu goma ne aka gayyato don su ba da shaida a kan kisan na Dujail kuma da damansu an bukaci da su boye kansu don saboda dalilai na tsaro.

A yayin da yake kare kansa daga zargin da ake yi masa na kashe mutane 148 a garin Dujail a shekara ta 1982, Saddam Husain ya yi watsi da dukkan zargin, tare da cewar wata makarkashiyar juyin mulki ce mutanen garin suka bukaci shirya masa, “kuma duk Shugaban kasar da aka yi wa yunkurin juyin mulki, ya zama wajibi a kansa ya dauki matakan hukunta wanda ke da alhakin makircin,” in ji Saddam Husain.

A yayin da mai shari’ar ya bukaci dakatar da Saddam lokacin da ya ke bayani, tsohon Shugaban ya mai da masa martani da kakkausar harshe, cewa shi fa ba ya tsoron hukuncin kisa, a game da haka, a bar shi ya barje guminsa dalla-dalla a game da abubuwan da ya sani cikin wannan harka.

bayan sa-ín-sar da aka yi tsakanin Alkalin da Saddam Husain, an dage shari`ar har zuwa ranar 21 ga wannan watan na Disamba da muke ciki.

A yayin da aka dage shari’ar da ake yi wa Saddam Husaini, an ci gaba da samun tashe-tashen hankula a cikin kasar, inda aka ruwaito cewa sojojin Amurka 14 suka rasu sakamakon wasu hare-hare guda uku da aka kai masu a kasar ta Iraki.

Mafi muni daga cikin hare-haren shi ne wani harin bam da aka dana a gefen hanya a kusa da birnin Falluja, wanda ya halaka sojojin Amurka 10, sannan 11 suka samu raunuka.

birnin Falluja dai ya kasance wani dandalin wani mummunan gumurzu tun bayan kifar da gwamnatin Saddam Husain shekaru biyu da rabi da suka wuce. To amma a ’yan watannin nan zaman lafiya ya dawo a birnin. Sauran sojoji hudu kuma sun mutu ne a wasu hare-hare daban-daban da aka kai masu.

A halin da ake ciki dai, da yawa daga cikin shugabannin siyasar Amurka na kira ga Shugaba bush da ya janye dakarun kasar daga Iraki.

A kuma can yamma da birnin bagadaza sojojin Amurka da na Iraki sun kaddamar da wani farmaki a kan masu fafutika.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International