Almizan :Ziyarar kwamitin Imfaki ya yi armashi a Mafara ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 15 Zulkidah, 1426                 Bugu na 696                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Ziyarar kwamitin Imfaki ya yi armashi a Mafara


Daga Yakub Almafary

A kwanakin baya ne kwamitin neman imfaki na Da’iratul Am na Harka Islamiyya ya kai ziyara garin Talata Mafara ta cikin jihar Zamfara don yin bayanai dangane da sabon imfaki na Naira dari (N100) da ya fito duk mako. Nan take sai haduwar ta rikida aka yi ta kabbarbari da salati ga Manzon (S) da Iyalan gidansa (AS) kamar dai ana wa’azi ne a filin dandalin bara’a.

Shi dai wannan Kwamitin, yana da mutane biyar ne da suke jan ragamarsa da suka hada da Malam Kasim Umar Rimin Tawaye Sakkwato, wanda ya jagoranci tawagar, Malam Mukhtar Sahabi Kaduna, Manajan Darakta na I.M. Publications, Alhaji Hamid Danlami Zariya, Malam Mustapha Potiskum da kuma Malam Abdullahi Danladi.

Mai gabatar da jawabi na farko Malam Mustapha Potiskum, ya yi ta jan ayoyin Alkur’ani mai tsarki da Hadisan Manzo (S) da suke zaburar da ’yan uwa a kan imfaki a fi sabilillah, inda ya yi bayanin cewa Allah yana kira zuwa gare mu da mu yi imfaki da dukiyoyin da ya ba mu, wanda wannan jarabawa ce gare mu, sannan idan mun ba shi zai nunnunka mana ne nunki mai yawa a nan duniya da kuma gobe lahira.

Ya ce, “ai ko da da dako ne, yanko ciyawa ko amfani da irin dabarar dalibai ta tsallake cin abinci a yini, lalle za mu iya yin kokarin yin wannan imfaki don cika umurnin Malam Zakzaky, sannan mu sami falala mai yawa daga Allah.”

Malam Abdullahi Danladi ma ya zaburar da ’yan uwa sosai dangane da wannan imfakin gwargwadon fahimtar ’yan uwan, tare da misalai masu ma’ana da zaburarwa. Ya ce, “sha’anin kudi janibi ne mai matukar muhimmaci a komai, balle a Harka Islamiyya, don dagatu ba ya turuwa sai da kudi. Musamman idan muka dubi zamanin da muke ciki,” in ji shi. A karshe Malam Abdullahi ya yi bayani dalla-dalla mai saukin fahimta, kuma a takaice dangane da duk abin da ya shafi katin alkawarin yin imfakin da yadda ake cika shi da sauran muhimman bayanai a kan katin da aka yi wata uku da kaddamar da shi.

Ya kuma bai wa ’yan uwa shawarar cewa duk wanda ya amshi wannan katin, to ya yi masa adana ta musamman kar ya lalace ko da kuwa bayan shekara ne in ya cika alkawarinsa don Mu’assasatu Shuhada’u ta yi amfani da shi wajen gane mutum ta hanyar cika alkawarinsa bin umurni da imfakinsa.

Manajan-Daraktan kamfanin I.M Publications, Alhaji Hamid Danlami, ya yi bayanin cewa babu abin da dan uwa ya kamata ya yi bayan ya gode wa Allah da ya sanya shi cikin mabiya Wakilin Manzonsa (S) na wannan zamani namu. Ya ce wanda ya yi wa Malam Zakzaky (H) biyayya, to ya yi wa Manzo (S) da Iyalan gidansa biyayya ne.

Saboda haka Alhaji Danlami ya ce, “a nan godiyar da za mu yi wa Allah ita ce mu yi wa Malam Zakzaky (H) biyayya ga dukkan abin da ya umurce mu ta bangaren imfakin dukiyarmu, ba da lokacinmu da ma rayuwarmu don dawowa da martabar wannan addini. Wannan shi ne zai tabbatar lalle mun karba da’awarsa, kuma muna son sa,” in ji shi.

Malam Mukhtar Sahabi kuwa ya caza ’yan uwa da bayanai dangane da muhimmantar da maganar Malam Zakzaky da matsayinta gare mu. Ya ce, “ya kamata ’yan uwa su yawaita sauraron kasetocin jawaban Malam Zakzaky ko da kuwa an yi ‘programme’ da kai, to, ka rika jin kaset din a kai-a kai balle idan ba a yi da kai ba. Sam kar ka bari sati daya ya shige ba ka nemi kaset din jawabin da Malam Zakzaky ya yi ba, in ba ka yi haka ba, to, an tsare ma,” in ji shi.

Malam Mukhtar ya ce, idan wata lalura ta kama dan uwa ta kashin kansa za ka ga yana ta fadi-tashi, ko a zaune ko a tsaye ya nemo kudi don magance ta. “Amma idan lalurar addini ce, sai mu yi tsaye wai ba mu da hali.” Ya ce, “to Malam Zakzaky ya ambata cewa kar mu ce ba mu da hali, ba mu da zuciya dai kawai (ta bayarwa).”

Ya ce ya kamata ’yan uwa mu sani cewa ko addini ya tabbata ba a daina imfaki. Ya ba da misali da Jamhuriyar Musulunci ta Iran da yanzu haka ake kula da masallatai da sadakokin mako da ke taruwa.

Malam Kasim Umar Sakkwato shi ne ya yi gabatarwa a wajen zaman da aka yi a harabar masallacin Juma’a na cikin garin Mafara. Shi ma ya caza ’yan uwa sosai dangane da imfakin da ma sauran imafakoki a Harkar nan.

bayan kammala jawabai, sai nan take ’yan uwa na garin suka rinka gogoriyo wajen amsar katin da ba da sunayensu don yin wannan imfakin.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International