Almizan :Sojoji sun aukawa 'yan uwa a Kaduna ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 29 Zulkidah, 1426                 Bugu na 698                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Sojoji sun aukawa 'yan uwa a Kaduna

Da sanyin safiyar ranar Juma'ar da ta gabata ne wata tawagar hadin gambizar jami'an tsaro na sojojin sama da na kasa da 'yan sandan Mobayil da jami'an Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, (NDLEA) suka dirar wa Markaz, wato gidan Amir na 'yan uwa musulmi na Kaduna da ke Zangon Shanu, T/wada Kaduna, Malam Muhammad Mukhtar Sahabi, suka jikkata wasu 'yan uwa biyu bayan wata fafawa da suka yi, kana daga bisani suka yi bincike a cikin gidan Malamin.


.

Su dai wadannan jami'an tsaro sun dira Markaz din ne jim kadan bayan kammala sallar Asuba ta ranar Juma'ar, a wani abu da suka sabayi na kai samame don kame masu shaye-shayen wiwi da sauran miyagun kwayoyi.

Ita dai Markaz din tana makwabtaka ne da wata makarantar firamare wacce ta zama sansani na mashaya wiwi da sauran miyagun kwayoyi, kamar yadda jami'an tsaron suke zargi.

Wannan harin zuwa Markaz shi ne karo na biyar, duk da sun san cewa 'yan uwa ba mashaya wiwi bane ballantana wani abu mai kama da haka.

Wannan hari na baya-bayan nan, kamar yadda Malam Muhammad Mukhtar Sahabi ya shaida wa Wakilinmu, ya kasance ne bayan da jami'an tsaron suka biyo mashayan, sai suka bi suka wuce ta wajen Markaz din a guje, su kuma jami'an tsaron na zuwa daidai Markaz, suka sami wasu ba'adin 'yan uwa suna jin dumi, sai kawai suka fara dukan su.

Malam Mukhtar ya ce shi yana jikin masallaci sun mana magana da wani dan uwa, sai kawai ya ji ana hayaniya, yana lekawa sai ya ga sojoji suna ta dukan 'yan uwa, “sai na je ina tambayar me ya faru? Ina Kwamandan naku ya yi mani bayanin me ke faruwa?” In ji Malamin.

Shi ma daya daga cikin wadanda aka jikkata a wannan hari, Malam Muhammad Sani Sarkin Malamai abin da ya bayyana wa Wakilan namu kenan. Ya ce bayan da Malam Mukhtar ya yi masu bayani, ya ce kowa ya saurara, sai kawai sojojin nan suka rufar masa (Sarkin Malaman) da duka suna kokarin so kwantar da shi, amma Allah bai ba su sa'a ba, “sai suka buga mani bindiga kai har suka fasa mani kai, ka gani,” ya nuna wa Wakilinmu.

Malam Muhammad Sani ya ci gaba da cewa bayan da kura ta lafa ne, sai Kwamandan ya nemi zai binciki gidan Malam Mukhtar. Bayan Malam ya yi masa wasu 'yan tambayoyi ne sai suka shiga gidan suka gabatar da bincikensu. Ba su dai sami komai ba.

Saboda haka sai Sarkin Malaman ya ce shi yana mamakin irin wadannan abubuwa, yadda kawai jami'an tsaro za su bushi iska su rinka kawo wasu hari haka siddan “wannan fa shi ne karo na biyar, har akwai lokacin da suka taba kashe mana mutun hudu,” ya ce.

Sarkin Malaman ya ce Malam Mukhtar ne linzaminsu, don haka idan wadannan jami'an tsaro suna kawo hari lokacin yana nan, to ranar da suka kawo harin in ba ya nan fa?

Ya kara da cewa bai kamata su rinka fakewa da mashaya wiwi suna kai masu hari ba, “hatta makiyinmu ya san ba ma shan wiwi ko wata kwaya, to menene na kawo mana hari?” Ya tambaya.

Shi kuwa dayan da aka jikkata, Malam Usman, cewa ya yi bayan da aka gama fafatawa a nan, sai jami'an tsaron suka kama shi suka sanya shi a mota suka tafi da shi.

Malam Usman ya ce ba su dire da shi ko ina ba sai ofishin jami'an tsaro na “strike force” da ke hanyar Mando, suka hada shi da mashaya wiwin da suka kama, suka yi masu jina-jina. Bayan da suka gama jikkata shi ne, sai suka wuce da shi ofishin NDLEA da ke Zariya. Amma ya ce a can Zariya ba a yi masa komai ba.

Mun tambayi Mal. Usman ko sun zarge shi da laifin shan wiwi ko wata kwaya? Sai ya ka da baki ya ce “a'a ba su zarge ni da shan kwaya ba, amma wai suna zargi na da laifin 'Rioting,' wato tayar da hankali, wai na yi fada da su.”

Ya aka yi Usman ya samu aka sako shi? Sai ya ce Shugaban Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu ne, Alhaji Garba Attahiru, bayan ya bi kadun abin da ya faru, ya bi har Zariya ya karbo belinsa.

Dama tun a ranar juma'ar da abin ya faru ne, bayan da Shugaban Karamar Hukumar ya ji, sai ya je gidan Malam Mukhtar din domin jin abin da ya faru, amma lokacin da ya je bai sami Malamin ba saboda ya tafi garin Lokoja zai yi wa'azi a can.

Daga nan ne sai Alhaji Garba Attahiru ya bi labarin har ya karbo belin Usman daga hannun jami'an NDLEA a Zariya.

Wakilinmu ya nemi jin ta bakin Shugaban Karamar Hukumar ta Kaduna ta Kudu, Alhaji Garba Attahiru, amma ya ce ba zai ce komai ba. Sai dai ya gode wa Allah da abin bai kai ga asarar rayuka ba.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International