Almizan :Editoci ku tsare gaskiya ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 29 Zulkidah, 1426                 Bugu na 698                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Gwamnoni 30 masu neman Obasanjo ya zarce a karo na uku

Daga Musa Muhammad Awwal

Duk da cewa tsarin mulkin kasar nan sashe na 137 (b) da 182 (b) na 1999 ya bai wa shugaban kasa da gwamnonin jihohi daman su yi mulki sau biyu ne kawai shekaru har hudu kashi biyu, to amma sai ga shi a makon da ya gabata Gwamnoni 30 cikin 36 na kasar nan suna rattaba hannun kan amince wa Obasanjo ya zarce a karo na uku wanda hakan su ma zai sake ba su dama su sake danawa.


Bincikenmu ya nuna 'yan majalisa ne kawai tsarin mulki bai takaita masu mulki sau biyu kawai ba, za su iya yi fiye da sau biyu.

Saboda haka wannan tsarin mulki da ya yi wa Shugaban kasa da Gwamnonin tarnaki shi ne ake kokarin a canza wa fasali ta yadda za a gyara shi yadda zai ba Obasanjo damar ta-zarce a 2007.

Duk da halin kunci da ake ciki a kasar nan, a tarukansu daban-daban Gwamnonin sun sha alwashin cewa samun goyon bayan haka daga Majalisar tarayya tare da samo gagarumar goyon baya daga 'yan majalisun jihohinsu kan wannan batu.

Wani bincike da ALMIZAN ta gudanar ya nuna cewa ba banza ba Gwamnonin ke neman zarcewa a shekara ta 2007 din.

Wani babban dalili da binciken ya gano shi ne cewa su dai Gwamnonin suna matukar jin tsoron hukumar nan ta EFCC wacce Nuhu Ribado ke shugabanta. Saboda haka suna ganin cewa muddin suka samu suka zarce a 2007, to za su tsallake kamun wannan Hukuma, tunda in suna mulki suna da kariya ta musamman, kuma shi Ribado mulkinsa zai kare ne tare da na Obasanjo.

Saboda haka ne suka ga babu yadda za su kauce wa kamun Nuhu Ribado in ba sun sami sake darewa a 2007 ba.

Gwamnonin sun shirya wannan abu ne da soma bi ta majalisun jihohinsu ta yadda za su shawo kansu su mara wa wannan shiri baya na sake tsarin mulkin kasa wanda zai ba Obasanjo da Gwamnoni damar zarcewa.

To sai dai kuma wannan yunkuri nasu zai yi wuya kamar yadda Sanatoci da sauran 'yan majalisar tarayya 'yan Arewa suka dauki aniyar taka wa Obasanjo burki a wannan matakin.

Gwamnonin da ba su amince da wannan mataki ba sune Gwamna jihar Legas Bola Tinubu, na jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau, Gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru Bafarawa, Gwamnan jihar Abia Orji Kalu, na jihar Anambara Cif Chris Ngege da kuma na Adamawa Boni Haruna.

Duk sauran Gwmnonin da ba wadannan ba, to sun rattaba hannu a goyon bayan zarcewar ta Obasanjo.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International