> Almizan:Za a kwashe Mahajjatan bana kuwa? ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 29 Zulkidah, 1426                 Bugu na 698                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Za a kwashe Mahajjatan bana kuwa?

Ganin 'yan kwanaki kadan suka rage Hukumomin Saudiyya su rufe filin saukar jiragen sama na Sarki Abdu'aziz da ke Jidda alhali Alhazan Nijeriya na jibge a sansanoninsu da ke fadin kasar, ya sa wasu Alhazan suka fara fargabar za a iya kwashe su duka kuwa?


Sai dai a lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi bayan wani taro da ofishin jakadancin Saudiyya da ke Nijeriya ya shirya a shekaranjiya Laraba, jagoran Alhazan Nijeriya, Sanata Ibrahim Mantu ya ce za a kwashe dukkan Alhazan da suka biya kudinsu ta hannun Hukumar Alhazai ta kasa.

Wani bincike da ALMIZAN ta gudanar a fadin kasar nan ta tarar cewa daga cikin Alhazai sama da 59,000 da suka biya kudinsu ya zuwa jiya Alhamis 12,000 kawai aka iya kwasa zuwa kasar Saudiyya.

Sanata Ibrahim Mantu ya dora alhakin wannan tsaikon da aka samu a wuyan kamfanonin jiragen saman da aka dora wa alhakin wannan aiki na jigilar Alhazan da kuma Hukumomin Saudiyya da suka fito da shirin yin biza ta Sakar Sam a (Intanet).

Kazalika Sanata Mantu ya tabbatar da cewa matsalar da aka samu kuma ta kara tsananin ne sakamakon kasa samar da wadatattun jiragen da za su yi jigilar alhazan da kamfaninon da aka dora masu alhakin jigilar suka yi.

Sai dai kuma kamfanonin jiragen saman Kabo Air, Knights Airline da International Trans Air da suke aikin kwasar Alhazan sun bayyana cewa matsalar ba da gare su take ba. Sun bayyana cewa akwai wani abu da ke tafiya ba daidai ba a tsakanin Hukumomin Alhazai da kuma gwamnatin kasar Saudiyya.

Hukumon Saudiyya dai sun tabbatar da cewa ranar 4 ga watan Junairun 2006 (kwanaki biyar masu zuwa) za su kulle filin saukar jiragen, kuma sun ce ba za su daga wa kowace kasa kafa ba idan har suka kulle. Da ma dai a an sha kara wa Nijeriya lokaci bayan a kulle don ta kai sauran Alhazanta da ba su kwashe ba.

A yayin da Alhazai suke cikin tashin hankali da damuwa da kuma zullumin ko za a kwashe su zuwa Saudiyya ko a'a, babban Daraktan gudanarwa na kamfanin Kabo Air, wanda kuma shi ne kamfanin da zai kwashe mafi yawan Alhazan da za su je Saudiyya, Alhaji Aliyu Aminu, ya ce, ba wani Alhaji da zai yi saura ba a kai shi wajen sauke farali ba.

Shugaban Hukumar ta jihar Kano, Alhaji Baffa Mustafa, ya ce wannan tsaikon da aka samu a kwasanAlhazai ba komai bane face kaddara, “mun gama duk shirin da ya kamata, amma kuma sai muke samun matsaloli ta inda muka zata da kuma ta inda ba mu zata ba,” in ji shi.

Da muke zantawa da shi kan wannan matsalar ta kwashe Alhazai da aka saba samu duk shekara, Shaikh Yakubu Musa Kafanchan, ya ce son zuciya da rashin tsoron Allah ne, “in dai ana so a yi maganin wannan matsalar sai an fid da son rai don a yi aikin da gaskiya.”

Shaikh Yakubu Musa Kafanchan ya ce, “idan ka dauki Hukumar Alhazai da kuma shi aikin Hajjin, ka kwatanta shi da Hukumar wasanni da kuma shi kansa wasan yadda gwamntoci suke ba shi muhimmanci, za ka gane cewa maganar aikin Hajji da Hukumar Alhazai ba a a dauke su da muhimmancin ba.”

Shaikh Kafanchan ya ce a wajen neman wanda za a damka wa Hukumar wasannin Nijeriya kullum ana lura ne da wanene dan wasa, ko kuma mai sha'awar harkar wasanni saboda wasannin su bunkasa, “amma harkar aikin Hajji da kuma hukumar hajjin sai a dauko wadanda ba su da masaniyya a harkar, kuma wadanda ba su da sha'awa da hakar, sai da kawai wani dalili na biyan bukatar wasu.”

Ya ce matsawar ana so a warware wannan matsalar tilas ne a mai da harkar jigilar alhazai da kuma duk wani abu da ya shafi Alhaji a hannun kungiyoyin addinin Musulunci da ake da su, “domin ita gwamnati ba ta damu da addininmu ba. Mu lura da abubuwan da suke faruwa a sauran kasashen musulmi kamar Indonesiya, Pakistan da Malesiya mana.”

Shaikh Yakubu Musa Kafanchan ya nuna damuwarsa matuka a kan yadda ake bai wa wasu kamfanonin aikin jigilar Alhazai a Nijeriya duk da kuwa an san ba su da ko fiffike, “wannan son zuciya ne irin na hukumomin Nijeriya, amma a sauran kasashen duniya ba haka ake yi ba.” Ya ce, “me zai hana a bai wa manyan kamfanonin zirga-zirgar Alhazai na duniya da suka yi suna wajen gudanar da wannan aikin ba tare da wata matsala ba?”

Da dama daga cikin Alhazan da muka zanta da su a sansanin Alhazai da ke Mando Kaduna sun nuna damuwa da bacin ransu dangane da yadda Hukumomin Alhazai na jihohin da suka fito suka fara watsi da al'amarinsu tun daga nan gida, “muna jin tsaron halin da za su shiga idan mun je can kasar Saudiyya. A wajen tafiya ma ba a kai mu a kan lokaci ba, ina kuma ga wajen dawowa? Mu dai sai abin da Allah ya yi,” in ji Malam Muhammad Arab, maniyyacin da yake jiran a kai shi Saudiyya.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International