Almizan :An sake gano tarin gawawwaki a Iraki ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 29 Zulkidah, 1426                 Bugu na 698                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu


An sake gano tarin gawawwaki a Iraki

Daga Aliyu Saleh


Wasu ma'aikata masu aikin tona inda za a sa fayil din ruwa a tsakiyar garin Karbala mai tsarki ranar Talata sun sake tono wasu tarin gawawwakin jama'a da aka jima da kashe su.

Kamar yadda ma'aikatan da suke aiki a Ma'aikatar ruwa ta Iraki suka bayyana, mutanen da aka samu sun hada da maza da mata da kananan yara. Likitoci da 'yan sanda sun ce an gane mutanen ne daga irin suturun da ke jikinsu.

Rahotannin da muka samu sun tabbatar da cewa tuni har wasu daga cikin dangin mutane sun fara gane 'yan uwansu, duk da kuwa da dama sun zangawaye sai dai kasusuwa.

Manema labarai a garin na Karbala mai tsarki sun tabbatar da cewa ana jin wadannan gawawwakin suna daga cikin dubban daruruwan jama'ar da Saddam Husaini ya karkashe a 1991 jim kadan bayan kammala yakin Tekun Fasha bisa zargin da ya yi masu na cewa sun yi masa bore.

Tun bayan da Amurkawa masu maye suka kawar da Saddam Husaini dai ake ta samun tafka-tafkan ramuka cike da gawawwakin mutanen Iraki, galiban a garuruwan Shi'a da Kurdawa da ke Arewa, wadanda ake jin an kashe su ne saboda rashin yarda da suka nuna da gwamnatin ta kamakarya.

A wani labarin kuma, sama da mutane dubu 100 ne suka yi wani jerin gwano a Iraki ranar Talatar nan suna Allah wadai da mamaye masu kasa da Amurka a yi.

Kamfanin dillancin labarai na ASSOCIATED PRESS ya ce, masu jerin gwanon, da suka hada maza da mata, sun rinka rera taken hadin kai ga mutane Iraki; “Ba Sunni, ba Shi'a, sai hadin kan kasa kawai.”

Da ake zantawa da Abdul Hamid Abdul Razza, 45, daya daga cikin masu jerin gwanon cewa ya yi, “mun fita wannan jerin gwanon ne domin mu nuna rashin yardarmu da sakamakon zaben da ake cewa an yi a Iraki. Muna so mu tambayi gwamnati da kuma Hukumar zabe ta kasa cewa; ina kuri'un da muka kada suka tafi? Wa ya sace su?”

A wani ci gaban kuma, Cibiyar dakarun mamaya na Amurka da ke Iraki, sun ba da labarin cewa mutane takwas ne suka rasu sakamakon wani yunkuri da suka yi na arcewa daga gidan yarin da ake tsare da su a Arewacin Iraki a jiya Alhamis.

Mai magana da yawun dakarun mamaya, Sajen Keith Robinson ya ce mutane takwas din sun rasu ne sakamakon musayar wutar da suka yi da jami'an da ke kula da gidan yarin.

Sajen Keith Robinson ya ce, mutane 16 ne suka yi niyyar arcewa daga gidan yarin bayan sun kwace makamai masu yawa sun yi wa masu gadin yarin ruwan wuta. Ya ce daga cikin mutane takwas din da suka mutu akwai sojan Amurka daya.

Wani mai magana da yawun Ma'aikatar tsaron Amurka, Bryan Whitman ya ce, wannan kurkukun da aka yi wannan dauki-ba-dadin ba yana karkashin kulawar dakarun mamaya na Amurka bane. Ma'aikatar Shari'a ta Amurka dai ta horar da sama da wadoji 300 na Iraki..

A baya dai an sha samun abubuwan kunya ga fursononi da sojan mamaya na Amurka suka aikata a kurkukun da ke fadin kasar. Ko a farkon wannan makon ma sai da Jakadan Amurka a Iraki, Zalmay Khalilzad ya ce an samu rahoton aikata abubuwan kunya sama da 120 a gidajen yarin Iraki.

Wasu masu kula da yadda al'umura suke gudana suna ganin wannan boren da aka yi a gidan yarin Iraki kitsa shi aka yi, musamman da yake ya zo kwanaki uku bayan Amurka ta ki yarda da neman izinin kula da gidajen yarin kasar da Hukumomin Iraki suka yi a farkon wannan makon. Sojan mamaya na Amurka dai suna tsare da mutane sama da 14,000 a gidajen yara daban-daban da suke Iraki.

A wani ci gaban kuma kamfanin dillacin labarai na ASSOCIATED PRESS a Iraki ya ce daga shekaranjiya Laraba an kashe sama da sojan mamaya na Amurka 2,172 tun bayan mamaye kasar da suka yi a cikin watan Maris na shekarar 2003. Rahoton ya ce daga cikin wannan adadin, 1704 an kashe su ne a bakin daga.

Sojan mamaya na Amurka na baya-bayan nan da aka kashe sun hada a Sajen Dane O. Carver, 20, a garin Khalidiyah da Sajan Dominic R. Coles, 25 a garin Bagadaza. Tuni dai iyalan wadannan sojojin na Amurka da ke Iraki suke ta godo da Bush ya dawo masu da 'ya'yansu gida.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International