Almizan :Da'awar Malam Zakzaky ta taimaka mana ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 29 Zulkidah, 1426                 Bugu na 698                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Da'awar Malam Zakzaky ta taimaka mana


In ji Shaikh Ibrahim Gajale Gombe

Wani shahararen Malamin Darika Tijjaniya, wanda ke unguwar Pantami a garin Gombe mai suna Shaikh Ibrahim Gajale ya bayyana da’awar Malam Zakzaky da cewa ta taimaka wa ’yan Darika Tijjaniyya wajen wayar da kan al’umma kan su waye Iyalan gidan Annabi (Ahlul Baiti).

Malamin ya yi wannan tsokacin ne yayin da wasu sashin ’yan uwa suka kai masa ziyara a gidansa da ke Pantami karkashin jagorancin Shugaban Halkar Pantami, Malam Abubakar Pantami.

Tun da farko Malamin ya shawarci ’yan uwa Musulmi da suka ziyarce shi da cewa su kara yin riko kam-kam da Iyalan gidan Annabi. Malam ya ci gaba da cewa, yin riko da Ahlin gidan Annabi shi ne riko da Musulunci.

Daga nan Shaikh Ibrahim Gajale ya fadi silsilar wasu Waliyai, wanda kuma ya ce dukkansu sun hadu ne a wajen Imam Ali (AS) da Fatima (AS). Haka kuma ya fado tarihin wasu daga cikin Imamai, inda ya yi dogon bayani kan falalarsu da kuma yadda suka fuskanci gallazawa daga wajen mahukuntan zamaninsu, musamman irin musiba da bala’in da Imam Husaini ya fuskanta a hannun Yazidu dan Mu’awiya. Daga bisani ’yan uwa sun yi wa Shaikh Gajale tambayoyi, inda shi kuwa ya ba su amsa mai gamsarwa. Daga cikin tambayoyin wani dan uwa ya tambayi Shehin Malamin shin ko yaya zai kwatanta da’war Malam Zakzaky (H) da ta Shaikh Ahmadu Tijjani (RA) ganin yadda dukkansu sun yi riko da Iyalan gidan Annabi da kuma Jikokin Annabi? Sai Malamin ya kada baki ya ce, “da’awar Malam Zakzaky (H) da ta Shaikh Tijjani jirgi daya ne ya dauko su, domin kamar yadda Malam Zakzaky (H) ke alfahari da Jikokin Annabi, haka shi ma Shehu Tijjani ke alfahari da su.”

Ya kara da cewa, akwai ma inda Shehu Ahmadu Tijjani ya yi tawassuli da Jikokin Annabi guda 11. Ya ce kuma wannan shi ne babban abin da ke alamta cewa Malam Zakzaky waliyyi ne domin duk wani Waliyi, to takamarsa Jikokin Annabi.

Don haka Shaikh Ibrahim Gajale ya yi addu’ar fatan alheri ga ’yan uwan da suka kai masa ziyarar, yana mai cewa wannan (ziyara) karantarwa ce irin ta Annabawa.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International