Almizan :Maniyyata 5800 ke jiran tsammani a Kano ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 6 Zulhijjah, 1426                 Bugu na 699                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Maniyyata 5800 ke jiran tsammani a Kano

Daga Ali Kakaki alikakaki2001@yahoo.com


o.
i

   

Ya zuwa shekaran jiya Laraba, cikin maniyyata 15,000 da za su tashi daga shiyyar Kano, mutum 9200 ne kacal suka samu isa kasa mai tsarki, sauran maniyyata 5800, daga jihohin Bauchi, Katsina da kuma Kano, suna kwana a sansanin alhazai da kuma filin jirgi suna jiran tsammanin isowar jirgin da zai kwashe su zuwa kasar Saudiyya.

AL-MIZAN ta ziyarci sansanin alhazai na shiyyar Kano da kuma filin jirgi, inda ta samu zantawa da wasu alhazan da suka fito daga jihar Katsina su duba uku, wadanda suka kwana uku a filin jirgin sama suna jiran isowar jirgin da zai kwashe su. Sun koka kwarai da gaske a kan halin da suke ciki na watsi da su da Hukumar alhazai ta jihar Katsina ta yi, suna kwana a filin Allah Ta’ala.

Ko da AL-MIZAN ta nemi jin ta bakin daya daga cikin manyan Hukumar alhazan jihar, sai aka ce suna gida Katsina a wannan lokacin, amma ta samu mai bai wa Gwamnan jihar shawara a kan kafofin yada labarai, Mal. Nasiru Abdul a kan korafe-korafen mahajjatansu, sai ya ce, “kamar yadda ka bukaci ka ji halin da alhazanmu suke ciki, a gaskiya alhazanmu an kawo su nan filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da saran suna zuwa za a kwashe su zuwa kasa mai tsarki, amma sai aka samu tsaiko, domin kamar yadda ka sani ne ana da tsaiko na kwasar maniyyata daga nan Nijeriya zuwa kasa mai tsarki.”

A bangaren alhazan jihar Bauchi kuwa, a cikin mutum dubu uku an dauki mutum 346, sauran mutum 2654 suke jiran tsammanin a zo a kwashe su, a inda wasu daga cikinsu suka shaida wa AL-MIZAN halin da suke ciki na damuwa da rashin tabbacin tafiyarsu zuwa kasa mai tsarki.

AL-MIZAN ta tattauna da Amirul hajj na jihar Bauchi, Alhaji Tanko Ibrahim Jalam, Kakakin majalisar dokokin jihar a kan halin rashin tabbas da alhazan jihar suke ciki, sai ya ka da baki ya ce, “kamar yadda ka gani, kuma kamar yadda ka tambaye ni, alhazan jihar Bauchi mutum 3105 ne gaba dayansu.”

Ya ci gaba cewa, a cikin ikon Allah wannan jarrabawa da muka samu ta matsalar daukar alhazai ba karamar masifa bace a kan dukkan musulmin Nijeriya. Abu ne wanda ya kamata a ci gaba da addu’a, sannan kuma ya zama darasi ga shugabanninmu wadanda hakkokin gudanar da wannan abu ya hau kansu, musamman Gwamnonin jihohi.”

A bangaren jihar Jigawa, su kuwa tuni suka gama isa kasa mai tsarki, suka bar yayarsu jihar Kano a baya da kimanin mahajjata dubu 1050 suna jiran tsammanin a zo a kwashe su zuwa kasa mai tsarki.

Alhaji Baffa Cinade, babban Jami’in hukumar alhazai ta kasa shiyyar Kano, a zantawarsa da AL-MIZAN ya bayyana mata cewa suna da alhazai dubu goma sha biyar daga shiyyar Kano, kuma zuwa wannan rana ta Laraba sun kwashe mutane dubu goma sha biyu zuwa kasar Saudiyya, kuma cikin yardar Allah za su kammala kwashe sauran maniyattan kafin cika wa’adin rufe filin jirgin sama na Sarki Abdul’aziz da ke Jiddah.

Ba za mu bar Alhaji daya a kasa ba

In ji Amirul Haj

A ranar Litinin da ta gabata ne Amirul Haj na bana, Sanata Ibrahim Nasiru Mantu ya tattauna da Editocin wasu jaridun Hausa guda hudu kan dambarwar da ke tattare da aikin hajjin bana da kuma dambarwar siyasar da ta daibaibaye jiharsa ta Filato da kasa baki daya. A yau dai ga hirar da aka yi da shi a kan aikin hajji, matsalolinsa, mafitar da yake gani da yadda za su tarbi gaba. A mako na gaba insha Allah kwa ji karashen hirar kan matsalolin siyasar jihar Filato da ta kasa baki daya. A sha karatu lafiya.

TAMBAYA: Wani mai karanta jaridarmu daga Benin ya nuna damuwarsa kan cewa yau saura kwana biyu a rufe filin saukar jirage na Saudi Arebiya, amma ko rabin alhazan kasar nan ba a kwasa ba, a matsayinka na Amirul Haji na bana wane tabbaci za ka bai wa Maniyyatan kasar nan?

SANATA MANTU: Na farko ba gaskiya bane cewa ba a kwashi rabin Maniyyatan kasar nan ba, an riga an dibi mafi yawan Maniyyata. Wadanda suka rage suna da yawa, amma ba su fi kashi 40 na yawan Alhazan kasar nan ba baki daya. Kamar yadda ka sani ne cewa kwanan baya jiragen Kabo ne kawai ke aiki, wasu jiragen ma da aka samu, sai aka zo aka gurguntar da su, domin ana cewa ba su da wasu cikakkun takardu. To amma bana saboda sammakon da aka yi na kafa membobin hukumar Alhazai, wanda ake kiran su “National Committee on Haj,” mun roki Gwamnati cewa wannan wadanda suka yi aikin na bara a bar su su ci gaba, domin sun ga abubuwan da suka faru bara. Duk da cewa mutum na nasa Allah na nasa, in ba haka ba, a nawa ganin kokarin da aka yi, ban zata za a sami cikas ko matsala ta ko anini ba. Amma abin takaicin shi ne ba bambancin wahalar da aka sha bara wajen daukar Alhazai da kuma yadda ake ciki a yanzu. Sai dai bambancin da aka samu shi ne daga lokacin da Gwamnati ta bayyana sunana na zama Amirul Hajji na wannan shekarar, to sai na mayar da Ofis dina can Hukumar alhazai don in gane wa idona ina ne ake samun kurakurai.

Da, ya kamata mahajjata su fara tashi ranar 17 ga watan jiya, bayan da na zo sai na ce a fara ranar sha biyar ga wata. Ka ga muna da doki da kuma burin cewa bana za a ga mun gama daukar mahajjata kafin ma lokacin da aka ba mu tunda mun yi saurin kwana biyu. Ni da kaina na tafi Sakkwato na yi sallama da alhazan farko wanda suka tashi ranar 15 ga wata. Wannan na nufin kenan ya kamata a ce yau da muke yin wannan magana ba sauran Maniyyaci ko daya a kasar nan saboda wannan burin. To sai da aka fara kamar abin arziki daga baya kuma sai aka zo aka fara gosilo.

Sannan na gane cewa farashin daukar Alhaji daga Nijeriya zuwa kasa mai tsarki, duk duniya ba wadanda suke biyan karamin kudi daga kasarsu zuwa kasa mai tsarki kamar Nijeriya. Sudan dai tafi kusa da Saudi Arebiya, amma daga Sudan zuwa Saudi Arebiya ya darar ma Dala 1000. Mu kuma a nan daga Legas zuwa Saudi Arebiya muna biyan Dala 950 ne, daga kuma Arewa Dala 900 ne daidai. To in daga Sudan za a biya Dala 1200, to mu nan ya kamata ya fi haka.

To abin da zai ba su wadannan mutanen su iya aiki shi ne suna jira sai mutanen sun nemi jirage sun gama kwasar nasu alhazan kafin a zo nan a kwashi masu saukin kudi. Shi ma wannan yana daga cikin abin da yake kawo mana cikas, in ba haka ba, da duk kamfanonin jirage za su yi ta rige-rigen zuwa nan Nijeriya saboda yawan jama’armu. Amma za ka ga kasashen da alhazansu ba su wuce 10,000 zuwa 50,000 ana kokawar zuwa wajensu saboda ribar da mai jirgi ke samu a wajensu.

Wannan shi ne babbar matsala, wato ba ma iya biyan farashin da masu jiragen za su zo Nijeriya su dibi jama’a. Inda farashinmu yana da kyau da kowa zai taho nan ne, domin muna da Maniyyata 60,000.

To bana abin da ya faru su Hukumar Alhazai na Tarayya sun shirya a kan cewa za a dauki Alhaji daga Legas a kan Dala 1,200; daga Arewa kuma kan Dala 1,050. To me zai zo ya faru? Da suka tura wadannan kamfanonin, sai suka sake wata yarjejeniya da wadannan Hukumomin Alhazan na jihohi. Cikin wannan yarjejeniya har da rage kudin jirgin, ya dawo kasa. Ya zama a Arewa sun yarda a kan Dala 900, a kudu kuma Dala 950.

Ba wani laifi a game da wannan domin kowa na neman sauki ne, to amma wannan sai ya zama mana wahala, domin a yau din nan da muke magana, Gwamnan jihar Oyo da ya ga zai bar Alhazansa a tasha, kun san Oyo garin musulmi ne, ya nemi mu ba shi izini, kuma mun ba shi ya dauko jirage. Yanzu haka kowane mutum yana biyan Dala 1,550. Kun ga wajen karin Dala 600.

To da ya yi wannan tsari, jirage a guje suka zo suka kwashe mutanensa. Don haka sai muka roke shi da wannan tsarin nasa, don Allah da Annabi ya kwashi Alhazanmu na Osun, Ondo,Ogun, Lagos har ma da Edo. Don haka zuwa gobe ba za ka tarar da Alhaji ko guda ba a kasa, saboda farashin da suka ce za su biya.

TAMBAYA: Ta yaya za a sami cikon kudin?

SANATA MANTU: Da Oyo ta yi niyyar biyan wadannan kudaden, amma Shugaban kasa ya ce, a dai dibi Alhazai su tafi ko nawa ne, alabashi a rubuta a takarda, shi ya san yadda za a yi. Ni kaina nan na yi karambani irin wannan, da yake Shugaban kasa ya yi mana hannunka mai sanda, na ba su izinin su je su kawo jirgi 747 wanda zai dauki mutum sama da 500 a lokaci guda.

Kamar yadda kuka sani kullum mune kadai kasar da Hukumomin Saudi Arebiya ba sa sanin ainihin yawan Alhazanmu sai sad da aka ce za a tafi Arfa. To Allah ya taimake mu wannan karon mun yi abin da wuri, daga ranar 27 ga watan 9 da ya wuce an rufe karba. Bana ne muke da ainihin yawan wadanda za su tafi aikin Hajji, in dai ba wani ya mutu bane.

Yanzu na fadi matsaloli, bari kuma in dawo kan abin da yake a kasa a yanzu. Akwai mutane wajen dubu 25 wadanda ba su tashi ba, amma daga shekaran jiya da na mai da Ofis dina can, ba ma tashi sai wajen asuba sannan mu dawo gida, kullum ana daukar mutane dubu takwas kowace rana, maimakon dubu biyu-ukun da ake dauka a da.

Mun sami takarda daga kasa mai tsarki cewa ranar 4 ga wata za a rufe filin jirgi, amma duk jirgin da ya sauka bayan wannan adadi za a ci shi tarar Riyal 200,000. To sai muka yi lissafin farashin da wannan kamfani suka ba mu domin za mu dauke su a kan awa-awa ne, sai muka ga cewa bai wani asara da za a yi, in ma an yi asara bai wuce dubu hamsin ba kowane jirgi. Kuma idan za mu biya wannan tarar, har zuwa ranar Arfat za mu iya kai mutane. Saboda haka ba ni da shakkar cewa ba za mu kai dukkan mutanenmu ba idan aka yi amfani da wannan tsari. Idan Allah ya so ya yarda babu mutumin da ba zai je ba. Da ni zan tashi yau zuwa Saudiyya, amma na riga na bari cewa ba ni kadai da mebobina ba, har Hukumomin DPA da NCH da duk mutumin da wannan aiki ya shafa da Ministan harkokin waje, ba mai tashi sai mun ga tashin Alhajin karshe. A takaice dai in Allah ya yarda ba za mu bar kowa a kasa ba.

Abin da mutane suka dauka shi ne idan aikin Hajji ya yi dadi, to Amirul Hajji ne, idan kuma bai yi dadi ba, to shi ne; musamman ma rashin dadinsa, domin idan ya yi dadin, ba mai yabawa. Idan ba yanzu ba, da ai Sarakuna ake bai wa Amirul Hajji. Kana ganin wane Basarake ne zai yi irin wannan dawainiyar da muke yi, ya je nan ya je can, kamar yadda muka yi bara a Makka? Idan muka fara zagayen tanti na alhazai, sai mun zagaya har asuba muna yi. Duk a kafa muke yi. Sai ka ga saurayi matashi ya kasa, mu mu yi gaba. Duk muna yin wannan ne don mu ga lafiyar Alhazai. Idan muka sami marar lafiya sai mu tafi asibiti mu duba shi. In mun je sai ka ga Larabawan sun kara kulawa da shi.

Na bayar da shawara a majalisa na kafa Hukumar alhazai, haka kuma a daya majalisar Dakta Bugaje ya bayar da irin wannan shawarar. Saboda haka daga wannan shekarar da za mu shiga Hukumar za ta yi zaman kanta sai kungiyoyin Musulunci kamar Jama’atu Nasril Islam da Supreme Council for Islamic Affiars da sauransu. Idan an yi haka ina ganin za a sami nasara, saboda ma’aikatan za su zama na dindindin, ba wai a dauke ka sati biyu-uku ba.

TAMBAYA: Wannan shirin duk na tafiya ne, to maganar dawowa fa?

SANATA MANTU: Abin haka yake ka san duk wanda ya tafi a karshe, to shi ya kamata ya dawo a karshe. Bayan haka za mu tuntubi Saudiyya domin su suna da jirage da yawa. Kai bari dai in gaya maku gaskiya, abin da ke damun wannan aiki shi ne ‘Corruption’ (cin hanci da rashawa). Ka san shi Balarabe ba zai bayar da cin hanci ba. Don haka tilas ne a sami kwamfanonin da suke da gaskiya, wadanda idan aka yi alkawari da su za su zo karfe sha daya, to sha dayan na yi suna sauka a kasar nan. Don haka dole ne mu yi kokari muga an kau da wannan daga aikin Ubangiji.

TAMBAYA: Ka yi maganar cewa Alhazan kasar nan ba sa biyan kudi kamar yadda ya kamata, to amma a da mun san cewa Gwamnati na rage wa masu jirage kudin mai da kuma na sauka har da na fakin, wanda wannan ragi kuma sai ya koma kan Alhazai din, shin ko Gwamnati ta janye wannan ragin ne?

SANATA MANTU: Wallahi ba a janye ba. Shugaban kasa ya yi shela shekarar da ta wuce cewa ba za a sake yi mana afuwa a kan wannan ba, to amma a yanzu an janye na mai, amma mun yi kokari mun ce, to ai ko allura za ka yi wa mutum, ba za ka ba shi allurar da za ta yi masa lahani ba. To sai aka janye na mai kenan, amma har yanzu farashin manmu yafi na ko’ina arha a duniya, saboda haka sun fi son su sha mai a nan. TAMBAYA: Bisa bayanin da kayi na farashi tsakanin nan da kuma wasu kas ashen, wannan na nufin cewa masu shirin tafiya a shekara mai zuwa su yi tsammanin farashi mai tsada kenan?

SANATA MANTU: To, ba ma son mu yi wa mutane mummunan albishir, amma idan mutum yana son ya zama mutum, sai ya yi abin da ya dace. Muna magana da wani Likita ya ce duk wanda ya auna jininsa ya hau a Kano. Wallahi mutanen Bauci da muka je, kowa jininsa ya hau, musamman wanda bai taba zuwa ba. Kasan kuma muhimmancin zuwa Hajji ga musulmi.

Ina ganin ba wai irin mugun kari na riba ba domin wannan aikin Allah ne bai kamata Hukumar da za mu kafa sabuwa ta zama abin nan ba, amma ban san ko ka taba zuwa Malesiya ba? Tabun Hajj ita ce kamar ‘National Hajj Commision nasu. Sune Hukumar da ta fi kowacce Hukuma kudi a kasar gaba daya. Saboda iya tsarin da ke tafiyar da abin. Su a can tun mutum yana dan karamin yaro yana aiki kowane wata yana dan tara kudI domin kafin ya mutu ya tafi Hajji. Wani zai yi shekara biyar yana tarawa wani zai yi shekara goma yana tarawa kafin kudinsa su kai. Su kuma suna nan suna juya kudin a wasu hanyoyi wanda zai kawo masu riba.

Saboda haka da lokacinka ya yi ba wani abu, za ka tafi. Suna da kwamfuta da kayan aiki. Sun san cewa lokacinka ya yi za ka tafi. Nan da shekara goma ma sun san cewa ga wanda zai tafi da sauransu. Idan ka je Malesiya za ka ga ginin Ofishin Alhazai shi ne ginin da ya fi tsawo a kasar. Ina jin cewa ya kai hawa talatin da wani abu. Idan ka je can za ka ga Musulunci yana da tsafta da komai da komai. Mun san cewa nan muna da damar yin haka idan aka dauki masu gaskiya da rikon amana.

Komawa babban shafinmu        Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International