Almizan :Za a karbi Markaz ta Katsina ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 6 Zulhijjah, 1426                 Bugu na 699                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Za a karbi Markaz ta Katsina

A wani jawabin gargadi da ban magana da Shugaban Asusun Harka Islamiyya, Mal Kasimu Umar Sakkwato ya gabatar a zauren taro, Multi purpose Hall da ke filin Samji a garin Katsina, ya ce babban Kwamitin asusun Harka Islamiyya ya ba ’yan uwa na Katsina watanni uku rak da su kammala sabuwar matsuguninsu (markaz) da ake cikin ginawa a yanzu, ko kuma Kwamitin Asusun daga Zariya ya karbe Markazin ya isar, ya kuma zama mallakinsa.


Umurnin hakan ya biyo bayan kiki-kaka da tafiyar hawainiyar da Asusun Da'iratul Amm II yankin na Katsina ke yi ne, wanda ya janyo aka ba su rata don su kammala gina Markazin tasu kafin a ci gaba da yunkurin aiwatar da asusu na Amm II a yankin na Katsina.

Shi dai wannan katafaren ginin Markazin, wanda ko shakka babu bai da na biyu a duk fadin kasar nan a inda ’yan uwa musulmi almajiran Malam Zakzaky suke, ya kunshi masaukin Malam Zakzaky (H) da masu rufa masa baya idan ya zo garin na Katsina, sai matsugunin Wakilin ’yan uwa na garin Katsina Malam Yakub Yahya da iyalansa. Sauran kashi 1\2 na filin kuwa ya kunshi wani katafaren markaz da ke tare da Madrasa (wurin ba da karatu) da dakin komfuta da ke daura da ita Madrasa din.

Sauran filin da ke tattare da Markazin kuwa dakunan aje motoci ne da dakunan Harisawa.

Injiniya mai kula da ginin, Malam Hamisu Imam ya ce a yanzu ginin na bukatar Naira miliyan tara don kammaluwa, bayan ya lashe sama da Naira miliyan goma a baya.

A yanzu dai kule ne ga dukkan ’yan uwa na Katsina na ganin yadda za su ceci wannan matsugunin nasu daga kwacewa da babban Kwamitin Asusu na harka Islamiyya ya ce zai yi.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International