> Almizan:Tsakanin Gowon da Obasanjo ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 6 Zulhijjah, 1426                 Bugu na 699                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Musayar zafafan kalamai

Tsakanin Gowon da Obasanjo

Jan kunnen da tsohon Shugaban mulkin soja na Nijeriya, Janar Yakubu Gowon ya yi wa Obasanjo game da take-taken da yake yi na neman zarcewa a karo na uku a kan mukaminsa ya jawo ka-ce-na-ce tsakanin fadar Shugaban kasa, da kuma mutumin da ba a faya jin suna asakala da gwamnati mai ci ba.


Shi dai Janar Yakubu Gawan ya ja kunnen Obasanjo ne game da yunkurin ta-zarcen da yake yi a jawabinsa da aka karanta a madadinsa a wajen taron mutanen tsakiyar Nijeriya (Middle Belt) da ya gudana a Abuja a makon jiya, inda ya shawarci Cif Olusegun Obasanjo da ya guji neman yin ta-zarce, ta hanyar neman wa’adi na uku a kan kujerar mulki, matakin da tsarin mulkin Nijeriya bai yarda da shi ba.

Janar Yakubu Gowon mai ritaya ya ce, tilas shugabanni su guje wa kwadayin ci gaba da yin mulki, domin yin hakan zai sa jama’a su tunzura da su.

Tsohon Shugaban mulkin sojan, wanda ya kwace mulki a 1966, amma sojoji suka yi masa juyin mulki a 1975 bayan da ya bayyana shirin ci gaba da yin mulki fiye da ka’idar da ya tsayar tun da farko, ya bayyana rade-radin da ake yi na neman zarcewar Obasanjo a matsayin wani abin takaici. Ya ce ya kamata Obasanjo ya dauki darasi daga kurakuran da shi (Gowon) din ya yi, da kuma wanda Janar Babangida da Janar Sani Abacha suka yi, inda suka nemi neman zarcewa, amma hakarsu ta gaza cimma ruwa.

A lokacin da yake mai da martani kan wadannan kalaman na Janar Yakubu Gowon, mai taimaka wa Cif Obasanjo na musamman kan hulda da jama’a, Cif Femi Fani-Kayode ya fadi a wani taron manema labarai da ya kira a Legas cewa; Janar Gowon bai kai matsayin da zai bai wa Obasanjo irin wannan shawarar ba.

Cif Femi Fani-Kayode, ya ce, a matsayin Gowon bai cancanci ya ba da shawara irin wannan ba, “domin ana bayar da shawara ne a lokacin da mutum ya aikata wani abu da ke nuna yana da niyyar aikata abin da kake shawartar sa kada ya yi.”

Mai magana da yawun Obasanjo ya ce, “duk cikin mutanen da suka mulki kasar nan cikin kakin soja mutum biyu ne za su iya bayar da shawara kan dimokuradiyya da hanyoyin kafa mulkin dimokuradiyya, wato Janar Olusegun Obasanjo da Janar Abdulsalami Abubakar, domin su kadai ne suka sauka cikin dadin rai suka mika mulki ga farar hula a lokacin da suka yi alkawari.”

Ya ce, amma ba za a iya kwatanta haka ga Janar Babangida ko Abacha ba, “ina mamakin yadda mutumin da bai bar mulki lokacin da ya dace ba, mutumin da ya kara wa kansa wa’adin mulki har aka kifar da shi, shi ne yanzu zai dawo yana cewa wadansu kada su kara wa’adin mulkinsu.”

Ya ce, Janar Obasanjo a lokacin da ya yi mulkin soja a 1979 ba tilasta shi aka yi ya bar mulkin ba. “Domin Janar Murtala ne ya yi alkawarin mika mulki ga farar hula, amma da Obasanjo ya gaje shi sai ya tabbatar da cika alkawarin mayar da mulkin.”

Cif Femi Fani-Kayode ya ce, “amma sai ga shi mutumin da aka fatattaka daga gadon mulki, wai shi ne zai zo yana bayar da shawara ga wanda ya bar mulki bisa radin kansa, musamman a daidai lokacin da wannan mutumin bai fito ya ce yana son ci gaba da zama kan kujerar mulki ba. In kana son ka shawarci Shugaban kasa, yana da kyau ka yi da kyakkyawar niyya.”

Jita-jita ta bazu a gari cewa Obasanjo yana da niyyar yin rub-da-ciki kan karagar mulkin Nijeriya a bayan wa’adinsa ya cika a watan Mayun 2007, kodayake makusantan sa na ta kore yiwuwar haka.

Kodayake Cif Obasanjo ya ki ya fito da bakinsa ya musanta wannan rade-radi ko kuma ya gaskata su, amma kuma kalamun baya-bayan nan daga bakin wasu shugabannin jam’iyyar PDP da kudurin da wani kwamitin Majalisar Dattijai ya gabatar, sun nuna alamun cewa akwai wata kumbiya-kumbiyar da ake shirin yi ta kawar da tanadin wa’adi biyu kan kujerar mulki daga tsarin mulki, abin da zai share wa Obasanjo fagen sake yin takara.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International