Almizan :Mata na tururuwar shiga Musulunci a Turai ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 6 Zulhijjah, 1426                 Bugu na 699                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Wani sabon rahoto ya nuna cewa:


Mata na tururuwar shiga Musulunci a Turai


Mata a kasashen Turai sun bayyana abubuwan da ke jan hankalinsu suke shiga addinin Musulunci har suke tururuwar shigarsa. Dalilan nasu sun hada da yadda addinin na Musulunci ke mutunta mata, sabanin al’adunsu na kasashen Turai da ke mayar da matan tamkar kayan biyan bukatun sha’awar maza.

Wani rahoto da mujallar ‘THE CHRISTIAN SCIENCE MONITOR’ ta buga, ya tabbatar da haka a Talatar makon jiya. Mujallar wadda ta gudanar da binciken kwakwaf don gano dalilan da suke sanya mata Turawa suke rungumar addinin Musulunci a daidai lokacin da Musulmi ke shan matsi a karkashin shirin yakin da Turai ta daura da Musulmi mai suna ‘yaki da ta’addanci,’ ta nuna yadda hukumomin tsaro da mahukunta a kasashen Faransa, Amurka, Ingila, Sweden da Jamus suke nuna damuwa da yadda matan ke kwarara suna rungumar Musulunci a kasashensu.

Wata budurwa mai suna Mary Fallot da ta karbi addinin Musulunci shekara uku da suka wuce, bayan tambayoyin da ta rika yi wa kanta kan darikar Katolika da take bi tun tana yarinya, ta nuna damuwa kan yadda ake sanya mata ido tun bayan da ta Musulunta. Ta ce, “a wajena addinin Musulunci sako ne na soyayya ga bani Adam, kuma wanda ke cike da rungumar kowa da hakuri da kuma zaman lafiya.”

Lokacin da aka tambayi Mary Fallot, ko musuluntar da ta yi yana da alaka da batun soyayya ne, sai ta ce, “lokacin da na shaida wa abokan aikina cewa na musulunta, abin da suka fara tambaya shi ne, ko ina da saurayi Musulmi? Ba za su taba amincewa da cewa na musulunta ne don radin kaina ba.”

Ta ce, “a gaskiya na gamsu da yadda addinin Musulunci ke kusanta mutum da Allah. Babu wata sarkakiya a addinin Musulunci, addini ne da komai nasa ke da saukin fahimta. Ina neman hujja, mutum na bukatar dokoki da dabi’un da zai bi a rayuwa. addinin kirista bai ba ni irin wadannan dokokin ba.”

Wata Malama a Jami’ar Birmingham da ke kasar Birtaniya, Haifa Jawad, ta ce, ba kamar a baya ba da mata ke musulunta don su auri maza Musulmi, “a yanzu matan suna musulunta ne saboda gamsuwa da Musulunci.”

“Mata da dama suna nuna lalacewar dabi’u da tarbiyya a tsakanin Turawa a matsayin dalilansu na rungumar Musulunci”, in ji Dakta Jawad, wadda ta kara da cewa, “suna sha’awar daidaita tsakanin maza da mata da kula da su da ke kunshe cikin addinin Musulunci.”

Wasu kuma abin da ke burge su game da Musulunci shi ne irin yadda addinin ke ambaton maza da mata a al’amura da dama. Van Nieuwkerk da ta nazarci matan Jamus da suka musulunta ta ce, “Musulunci ya bayar da kula sosai kan batun iyali da rawar da uwa ke iya takawa a tsakani. Mata ba kayan biyan bukatar jima’i bane kawai a Musulunci.”

Wata Baturiya da ta musulunta, Sarah Joseph ta ce, “daukacin matan da suke musulunta suna kokarin samun saukakakkiyar rayuwa ce wadda ta yi nesa da ballagazajjiyar rayuwa irin ta Turawan Yamma.”

Wani labarin da muka samu kuma ya nuna cewa, manyan limaman cocin Katolika (kadinal-kadinal) da dama sun gargadi matan kasar Italiya su guji auren maza Musulmi bayan da suka lura ana samun karuwar mata kiristoci a kasar na auren maza Musulmi.

Italiya dai ita ce Cibiyar Darikar Katolika ta duniya, kuma Shugaban Darikar da aka fi sani da Fafaroma yana zaune ne a birnin Rum, hedikwatar kasar. Jami’an cocin sun ce a daidai lokacin da yawan Musulmin kasar Italiya ya doshi kai wa mutum miliyan guda, an samu kulluwar aure tsakanin mata kiristoci da maza Musulmi dubu 20 a shekarar 2005 da ta gabata.

Wannan ya nuna an samu karuwar matan kiristoci masu auren Musulmi da kimanin kashi 10 bisa 100 kan na shekara ta 2004. Cocin na Katolika dai yana da al’adar tattaunawa tsakaninsu da sauran addinai, ciki har da addinin Musulunci.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International