Almizan :Muhimmancin daren Arfa: ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 6 Zulhijjah, 1426                 Bugu na 699                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Tare da, Abubakar A. Almizan 0803 701 4341

Muhimmancin daren Arfa:

Dare ne mai albarka. Shi ne daren munajati (wato ganawa) da Allah (T), samun biyan bukata, karbar tuba, amsar duk wata addu’a, haka kuma ladar duk wata ibadar da aka yi a wannan dare, to daidai yake da ladar ibadar shekara 170.

GA KADAN DAGA CIKIN AYYUKAN

Karanta wannan addu’a kamar yadda aka ruwaito, duk wanda ya karanta ta za a yafe masa dukkanin zunubbansa. Ga farkon addu’ar “Allahumma ya shadida kulli najwa wa maudi’a kulli shak’wa wa alima kulli khafiyyat….” Addu’a ce mai tsawo sai a neme ta a cikin Mafatihul Jinan da sauransu.

Ana so mutum ya karanta ‘Tasbihatul ashrat’ kafa 1000. Shi ma a duba a Mafatihul Ji nan, dss don karin bayani.

A karanta wannan addu’ar: “Allahumma man ta’abba’a wa tahawwan…” har zuwa karshe. Shi ma a duba Maftihul Jinan don ganin cikon addu’ar.

Akwai ziyarar Imam Husaini da ake yi a wannan rana don samun kariya daga sharrin wannan shekara.

ABU NA GABA SHI NE: Falalar ranar Arfa: Ranar Arfa na daga cikin manya-manyan ranekun idi ita ce ranar da Allah (T) ya kira bayinsa ya zuwa ga yi masa da’a da bauta masa ga alkawarin samun baiwa da kyawawan abubuwa daga gare shi.

A wannan rana Shaidan yana kaskance ne fiye da duk wani lokaci. A ranar ce ake so kar ka nemi wata bukata wajen kowa face Allah (T). Idan an yi bincike za a ga cikakken bayani game da ayyukan wannan rana.

Allah (T) ya taimake mu, ya kare mu daga sharrin duk wani mutum ko aljani, amin.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International