Almizan :Zuwa ga Dana abin kaunata ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 6 Zulhijjah, 1426                 Bugu na 699                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Hantsi:

Zuwa ga Dana abin kaunata

Tun bayan da na rubuta wani rubutu mai suna “Hanyoyin da za ka bunkasa tunanin yaronka,” nake ta samun sakonin karbuwar rubutun sosai daga makaranta. Wannan ya ba ni karfin gwiwar zakulo wani hasken don sake wani yanayin sharhin wanda zai sa mai yunkurin tarbiyyantar da dansa ya yi shi a cikin nasara.

Shaikh Hasan Saffar

Wannan rubutu na tsamo shi ne kacokaf daga wata wasika da Amirul Muminin Ali bin Abi Talib (AS) ya rubuta wa dansa Imam Hasan (AS) mai suna; “ZUWA GA DANA.” Na yi amfani da wani littafi da aka buga da Turanci a kan wannan wasikar mai suna “My Dear Son,” wanda Ali A. Behzadina da MD Salwa Denny suka fassara daga asalin rubutun na Larabci zuwa Turanci, sannan ‘Islamic Academy’ da ke 3 Rapsey Street St Clair Trinidadwi WI suka buga, suke rabarwa kyauta a duniya.

Ka sani babu babban jari a rayuwa irin shawarwari da nasihohin magabata tsarkaka, maganganunsu arziki ne wanda babu inda za ka same shi sai a wajensu, Ubangiji ya hore masu sirrin boye da na bayyane, balle Sayyidina Ali (AS) wanda Manzo (SAW) ya ce, “ni ne birnin ilimi, Ali ne kofar shiga.”

Ka sani tarbiyyar yaronka kamar tarbiyyar al’umma ne, kuma kula da tarbiyyar wani abu ne mai motsawa da canzawa, yana jariri wanda aka haifa yau akwai abin da ya kamata ka yi masa, yana kara girma kana kara nuna masa sabon abu, kuma kana canza yanayin yadda kake horas da shi.

Ba za ka gushe kana yi masa jagora ba har sai ka bar duniya. Wannan wasika duk da na kawo ta daki-daki a nan na tsakuro dan kadan ne daga ciki. Allah ya ba da ikon wani ko wasu su fassara ta, watan wata rana su kawo ta duk a ALMIZAN, kuma a buga ta a matsayin littafin da duniyar makaranta Hausa su amfana, amin.

“Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Manzo (SAW). Ya dana abin kaunata ina son ka sani cewa girma ya zo mani ga rashin koshin lafiya, mutuwa na gab da ni a koyaushe.

“Wannan ya kara mani haramar cewa in kara sanar da ’ya’yana da na kusa da ni abin da na sani na rayuwa, darussa da hakikanin gaskiya don sanin ya rayuwar duniya take? Hakika a shawarwarina za ka samu maganganu wadanda za su yi maka jagora a rayuwarka mai kyau a wannan duniya, sannan lahira ka sadu da Ubangijinka kana farin ciki.

“Dana abin kaunata, ka amshi shawarwari na gaskiya, ka kuma aikata su. Duk abin da za ka yi ka yi a tsakaninka da Allah da zuciyarka cikin tsarki da ikhlasi. Dana abin kaunata, ka rika nazari da sanin daukakar wasu al’umma yadda suka yi tashe da yadda suka ruguje, yi tunani a kan matsalolin da suka fuskanta da nasarori da suka samu. Darussan rayuwarsa da me ka amfana da shi? Me zai ma amfani a rayuwarka?

“Dana abin kaunata, kar ka yi magana a kan abin da ba ka sani ba, kar ka yi zargi ko tsammani, kar ka yanke hukunci a kan abin da ka jahilta, kar ka gina ra’ayi cikin abin da ka san ra’ayinka yana iya zama ba daidai ba.

“Dana abin kaunata, kar ka fuskanci abin da sam ba ka da tabbas a kai, gara ka hakura da ka jefa kanka cikin hatsari ko gangancin abin da ba ka san ya yake ba. Dana abin kaunata, ka yi gwagwarmaya a duk inda ya kama domin daukaka kalmar Allah. Idan ka hakikance da gaskiyarka kar ka ji tsoron komai, kar ka kula da zancen mutane ko damuwa da kila a yi maka dariya.

“Dana abin kaunata, ka nemi samun ilmin addini. Ka nemi san fikihu. Duk wani aiki na addini, ka tabbatar da ka san shi kafin aikata shi. Dana abin kaunata, ka koya wa kanka shirya mafuskantar kowace irin matsalar rayuwa, masifu da bala’o’i da ke cikinta, a kowane yanayi kar ka dogara da kowa a lamurranka, sai Allah.

“Dana abin kaunata, ka sani ilimi mai amfani shi ne wanda aka yi aiki da shi. Komai mutum ya sani ko ya ji, in ba aiki ya zama banza. Don haka yi aiki da duk abin da ka ji, ina gaya maka.

“Dana abin kaunata, shekaruna na rayuwa wadanda suna gab da zuwa karshe, na yi amfani da su sosai. Na karanci yadda wasu a baya suka rayu. Na ga yadda ayyukansu suka kaya. Na yi imani sosai a kan ayyukansu da kudurorinsu. Na karanci abin da suka bari da kufansu. Na natsu sosai da yin iyo ga ayyukansu, tarihinsu sai da ta kai na san su kamar na yi zamani da su. Na san yadda suka yi nasara da yadda suka fadi. Na gano cewa nasara har abada tana tare da rayuwar da aka yi ta da zuciya daya da ikhlasi da kuma yin zurfin tunani a kan duk wani aiki da mai aiki zai aikata. Na lura ba rayuwa mai hatsari sai wadda aka yi cikin mugun nufi da hatsari, sai wadda aka yi cikin mugun nufi da aikata sabo.

“Dana abin kaunata, kar ka taba bari shakku ko karayar zuciya, ko ki, ko so maras hujja ko tushe ko turaddadi ya gurbata maka zuciya da tunani, ya sa ka ginu a wani ra’ayi batacce. Dana abin kaunata, duk abin da ka sanya a gaba, farko ka dogara ga Allah da neman ya yi maka jagora. Sannan ka fuskanci abu gaba-gadi bisa shawarwarin da nake ba ka.

“Dana abin kaunata, ka sani duk wanda zuciyarsa ba tsaye take ba, duk wanda ya bari tunaninsa ya gurbace, to zai ta fanganniya ne a duhu babu makama, zai zama kamar rakumi ne da ke fama da cutar dundumi.

“Dana abin kaunata, ka sani wannan duniya tana tafiya ne a wani yanayi a kan duk abin da ka aikata, shi za ka gani sakamakon aiki. Shi ne ke bin rayuwar mai aikin, mai kyau yana da mai kyau, mummuna da mummuna, sharri da sharri. Duniya na tafiya tsakanin farin ciki da bakin ciki, damuwa da walwala.

“Dana abin kaunata, maganar gaskiya ita ce, nasarar rayuwa na tattare da wadanda suka fahimci ya duniya take, suka kuma dauke ta a cewa wuri ne wanda a koyaushe za ka iya wucewa, kamar matafiyi da ya yada zango ya huta ya wuce.

“Dana abin kaunata, duk wanda ya fahimci abin da ya aikata shi yake bi, ya kuma yi aiki da wannan, ya gama samun zaman lafiya a rayuwarsa.

“Dana abin kaunata, a mu’amalarka da mutane ka dauki kanka a babban Alkali wanda ke hukunta kansa da kansa. Kar ka yi wa kowa komai, sai abin da kake so kai ma a yi maka. Ka yi fatan alheri ga kowa kamar yadda za ka yi a kanka. Ka ki wa (jama’a) abin da kake ki wa kanka.

“Dana abin kaunata, kar ka zalunci mutane, kar ka yi masu karya, kar ka danne su, ka zama mai tausayi da jinkai a gare su. Dana abin kaunata, kar ka aikata wani hali wanda ka san yana cutar da wasu ko yin sa yana bata masu rai da munanawa. Ka yi abin da yake farin ciki gare ka, kuma ga jama’a.

“Dana abin kaunata, kar ka yi maganar mutum a bayan idonsa, yadda ka san in gabansa ne ba ka iya maimaitawa ba, ka fadi alherinsa da ka sani. Dana kar ka yi maganar abin da ka san cewa abin da ka sani a kai kalilan ne, ko kuma ba ka san komai ba. Ka guji gulma ko bata sunan wani, yadda ka san kai ma ba za ka so haka nan ba.

“Dana abin kaunata, ka sani tafiyarka ta wannan duniya ba wata mai tsawo bace, amma tana da wahala da cin rai, ga sarkarkiya da santsi. A kanka ga kaya mai wahalar gaske da kake dauke da shi. A tafiyar kana bukatar guzuri sosai. Ka sani taka-tsantsan dole ne a wajenka.

“Dana abin kaunata, ka sani Ubangiji da ya halicce ka, ya kuma halicci duniya da abin da ke cikinta, yake kuma juya ta, ya ba ka cikakkiyar damar ka roke shi bukatarka, kuma ya yi alkawarin zai amsa maka; don haka kar ka yi baya a rokon nasa.

“Dana abin kaunata, ya zama ka sa a zuciyarka cewa Allah ne kawai ya san sirrin komai na bayyane da na boye. Don haka ka zabi mafi alheri in har ka roke shi. Ubangiji na iya amsa bukatarka, in ita ce ta fi alheri, yana kuma iya jinkirtawa in wannan ne mafi cancanta. Kar ka damu ko matsu idan ka yi rokon, ka ce sai ka samu biyan bukata nan take.

“Dana abin kaunata, ina kara nanata maka ka rike abu uku a tunaninka na kullum a rayuwar barci da farke. Sune, za ka mutu, ayyukanka, sai kuma rayuwarka bayan mutuwa. Dana abin kaunata, kar ka rudu da kyale-kyalen duniya, ko kuma dagawa da takawa dai-dai da wadanda suka dogara da rayuwar duniya ke yi.

“Dana abin kaunata, kar ka nemi duniya ido rufe, kar kuma ka ce ta kowane hali sai ka mallaki duniya.

“Dana abin kaunata, ka sani masu neman duniya ido rufe kamar karnuka suke. Kar ka zama kamar wasu dabbobi marasa hankali ko marasa basirar kansu.

“Dana abin kaunata, kar ka mika kanka ga bukatar zuciya da sha’awa da son ranka, kar ka dogara ga bukatarka da neman dole sai burinka ya cika. Wadannan su ke kai mutum su baro.

“Dana abin kaunata, ka yi hankali, kar ka mai da kanka bawa ga kowa, Ubangiji ya halicci da ne mai ’yantaccen rai, kar ka kuskura ka sayar da ’yancin nan naka ga kowa.

“Dana abin kaunata, ka kula ba wata riba da za ka taba samu idan ka banzantar da kanka, ka wulakanta mutunci da zumuncin da Allah ya yi maka, ka kaskantar da kanka ga wani mutum.

“Dana abin kaunata, ka sani babu wani kwanciyar hankali ko jari ga dukiyar da aka samu ko mulki wanda aka samu a haramtaciyyar hanya.

“Dana abin kaunata, ka sani dan kadan wanda Allah zai ba ka bisa yardansa ya fi amfani da biyan bukata da mutunci fiye da mai yawan da aka tara ta hanyar da ba ta dace ba, “lomar arziki ta fi kabakin tsiya.”

“Dana abin kaunata, ka kula da kare abin da ka mallaka, ya fi ka rika bin wasu su ba ka abin da suke da shi.

“Dana abin kaunata, abin da ka samu na guminka a hanya madaidaiciya komai kadan dinsa ya fi amfani da mai yawa da ka tara a haramun.

“Dana abin kaunata, ka kula ba wanda zai iya rufa maka asiri fiye da kai kanka. Mai yawan surutu yana tare da kura-kurai a rayuwarsa; wanda kuma ya fi yawan tunani da nazari ya fi yawan hangen nesa da dacewa ga nasara.

“Dana abin kaunata, ka rika shawartar abokinka, shawarwari na gaskiya ko da kuwa ba zai so ba. Ka yi nisa da abokantaka da mikiyin abokinka, domin abokin naka na iya zama makiyinka shi ma.

“Dana abin kaunata, ka iya sarrafa kanka a lokacin fushi da bacin rai, domin wannan yana haifar da da mai ido, in hankali ya dawo.

“Dana abin kaunata, idan za ka yanke dangantaka da abokinka, kar ka tsinke ta kwata-kwata, ka bar dan wani abin da zai rage a tsakaninka yadda za ka iya kulla shi ko da ya dawo don ci gaba da mu’amala da kai sosai.

“Dana abin kaunata, duk mutumin da yake maka kyakkyawan gani ko kallo kar ka bayar da shi, kar kuma ka aikata abin da zai sa ya canza tunaninsa. Kar ka yi neman asirin laifuffukansa. Kar ka kuma cutar da mai yi maka kirki.

“Dana abin kaunata, ka rike duk wata dangantaka da sahihan mutane, ka rika tarayya da masu hikima, malamai da masu neman sani. Dana abin kaunata, ka sani dangantakar da ta fi karfi wadda babu irin ta wadda ba ta yankewa ko tabuwa ko girgiza ita ce dangantakar mutum da wanda ya halicce shi - Allah.

“Dana abin kaunata, wani lokaci masani ko mai hikima na iya kasa cin nasara ga wani abin da ya sa a gaba, ko wani makasudi yake son cimmawa. Amma dolo da jahili suna iya cimma abin da suke so.

“Dana abin kaunata, ka kula da ’yan gidanka da kyau, ka nuna masu kauna, girmamawa, domin su kamar fiffike ne da kake takawa ka tashi sama, kuma su kamar hannaye ne masu taimakon ka, su kuma taimaka maka a duk fadanka. Su za ka dawo gare su in kana cikin matsala.

“Dana abin kaunata, bayan na ba ka wadannan shawarwarin, na amanantar da kai ga Allah Madaukakin Sarki. Zai taimaka ya kare ka, ya kuma nuna maka hanya a wannan duniya da lahira. Ina addu’a a gare shi ya kare ka da kiyayewarsa a nan da gobe kiyama.”

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International