Almizan : A Takaice kai Tsaye: Na M.M Awwal, Ta GSM,0803 451 4693 ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 6 Zulhijjah, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
A Takaice kai Tsaye: Na M.M Awwal, Ta GSM,0803 451 4693

NEMAN KARIN BAYANI KAN FIM DIN DANFODIYO

Assalamu Alaikum. Bayan sallama irin ta addinin Musulunci ina son in yi tambaya dangane da wani abu da na karanta a jaridar ALMIZAN. Tambayar tawa ita ce dangane da Fim din Danfodiyo. Na ga a lokacin da ake kaddamarwa kun yi batun hannun jari. Kuma na ga kun yi batun wanda zai shiga. To batun wanda zai shiga din shi ne ban gane ba. Don Allah ina neman karin bayani.

Daga Yahaya Salisu Dala (yahayadala@yahoo.com)

Ka duba i-mel dinka mun zo da karin bayanin. –Editan Shafi.

DON ALLAH KU TAMBAYAR MIN ALIYU SALEH

Assalamu alaikum. ALMIZAN don Allah ina so ku tambayar min Aliyu Saleh, wai shin Abu Mus’ab Al-Zarkawi yana rikiduwa ne, ma’ana yana canza kama ne?

Daga 0803 964 2196

SHUGABAN ’YAN SALLAFIYYA NA GUMEL SUNNAR KENAN?

Assalamu alaikum. Shugaban ’yan Sallafiyya na Gumel mun ji Kwamishinan kudi na jihar Jigawa ya biya maka Hajji, har ka mika hotunanka. Wannan ita ce Sunnar? Gaskiya, Malam Mansur Amir din ’yan uwa Musulmi kai ne mai kare Sunna, domin mun ji ka guji hajjin Kwamishinan kudi na Jigawa. Allah ya saka da alherinsa.

Daga Muhammad Gumel 0802 692 5458

KU YI MANA ALMIZAN TA TURANCI

Assalamu alaikum. Don Allah ku yi mana ALMZIAN ta Turanci, don gaskiya jaridar tana da farin jini kwarai da gaske. Saboda haka na ga ya dace ku rika yi mana ta Turanci, domin amfanin wadanda ba sa jin Hausa.

Daga Ishak Adamu Oando S/S. Samaru Zariya jihar Kaduna 0802 917 2184

Tana kan hanya, amma ta sakar sama.

SHAWARATA GA WAMAKKO

Assalamu alaikum. Ina da shawarar da zan bai wa mataimakin Gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Aliyu Magatarka Wamakko. Da zai daure da ya nemi gafarar ’yan uwa, da kuma Jagoran Harkar Islamiyya kan abubuwan da suka yi masu, maimakon ya ce zai kai ALMIZAN kara a kotu. Da zai yi haka da sunansa da ya baci ya gyaru. Muna rokon Allah ya karya azzalumai, amin.

Daga Sani Ibrahim Muhammad Zariya 0805 705 3920

INA JINJINA GA SHAIKH ZAKZAKY

Assalamu alaikum. ALMIZAN don Allah ku isar min da sakon gaisuwata da jinjina ga Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky bisa gwagwarmayar jaddada addinin Musulunci da yake yi, Allah ya taimaka, amin.

Daga Abdul Razak M. Gora 0805 803 9023

GEORGE BUSH MENENE ABIN YI?

ALMIZAN ina so ku ambayar min Shugaban Amurka George W. Bush cewa menene abin yi yanzu, tunda Iran tana gina wasu karin cibiyoyin makamashin nukiliya don amfanin jama’arta? Ya kara tura masu binciken makami mana?

Daga Ado Waziri 0805 775 7294

SAI DAI MU YI WA SHUGABANNIN ALLAH YA ISA

Assalamu alaikum. Mu dai mutanen Nijeriya sai dai mu yi wa Allah godiya, sannan mu yi wa shugabannin kasar nan Allah ya isa, domin sun kwashe mana dukiya sun kai waje sun boye.

Daga Musa Husain (musahsn@yahoo.com)

JANAR BUHARI YANZU MUN GANO

Buhari lalle sai a yanzu muka san makasudin zuwanka Amurka a kwanakin baya. Mun gano ka je neman goyon bayansu ne bisa kan ta-zarcen Obasanjo.

Daga 0802 469 5099

ABIN DA KUKA SHUKA, SHI ZA KU GIRBA

Assalamu alaikum. Ina kira ga duk wani mai mulki da ya ji tsoron Allah, ya yi wa jama’arsa aiki, in kuwa ba haka ba, zai ji kunya duniya da lahira.

Daga 0803 613 8658

SHUGABA BAI GANE ANA KIN SA BA?

Ina ’yan Nijeriya masu ido da kwalli, ku duba ku gani lalle wannan Shugaban namu ya cika summum-bukumun tunda bai gane talakawansa suna kin sa ba.

Daga 0806 556 9999

SHAWARA GA GWAMNATIN KATSINA

Assalamu alaikum. Shawarata ga gwamnatin jihar Katsina kan rashin aikin yi ga matasa. A soke ba da aikin kwangila ga tsaffin ma’aikata da wadanda ba ’yan jihar ba wadanda aikinsu bai zama tilas ba. Hausawa na cewa, ‘sai an kau da wani wasu ke samu.’

Daga Mansir Katsina 0802 794 8976

SHIN DA GASKE NE KUWA NUHU RABADO?

Assalamu alaikum. Nuhu Ribado ka ce za a dauki matakin tsige duk Gwamnan da aka kama yana sama-da-fadi da dukiyar jama’a yadda aka yi da Gwamnan Bayelsa. In da gaske ne a fara daga kan Shugaban kasa mana, ko shi ya fi karfin doka ne? Ku ji tsoron Allah dai.

Daga Abba Badeggi 0806 580 7990

AHMADINAJADI DON ALLAH A BIYO TA ZARIYA

Ahmadinajadi don Allah idan an tashi share kasar Isra’ila a biyo ta Zariya wajen Jagoranmu Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) domin tuni muka shirya.

Daga 0806 961 3516

…AHMADINAJADI ALLAH YA SAKA DA ALHERI

Dakta Ahmadinajadi Allah ya saka da alheri, don maganarka ta sa Sharon (LA) hawan jini, yanzu ga shi nan yau ba lafiya, gobe sai cuta. Allah ya kara masa.

Daga Balarabe Misau 0802 799 1358

MUSULMI MU HADA KAI

Idan fada da bidi’a ya gagara kuma ya rarrabamu, to mu daddawo. Dama fada da kafirar Hukuma ne kawai mafita, kuma shi zai hada kanmu insha Allahu.

Daga Danjuma El-Bilal B/Ladi Jos 0806 580 0656

REDIYON NAGARTA INA SHIRIN KOWANNE ALLAZI….?

Gidan Rediyon Nagarta kun ba mu kunya. Ina aka kwana da shirinku na Kowanne Allazi…, dama a cikin shirin kuke kiran shugabanninku ku yi hira da su.

Daga 0805 976 3220

ALLAH YA BARKU DA ALZARKAWI DA OSAMA

Mai wannan lamba na ga ra’ayinka, Allah ya bar ku da Zarkawi da Osama. To mu ma mun ce maka amin. Sannan kuma wai ka ce wai ’yan Shi’a ba sa fada ba kafirci sai Musulunci. To sai in ce ka ji tsoron Allah. Shi Zarkawi a hare-haren da yake kai wa a Iraki su wa yake kashewa? To mu dai mun ce Allah ya bar mu da Manzon Allah da Iyalan Gidansa, amin.

Daga Gambo Katsina 0802 689 4453

’YAN PDP BA MU YARDA DA TUBANKU BA

’Yan PDP da suka fice suka kafa MDD da MRD ba mu manta da rawar da kuka taka a 1999 da 2003 ba. Don haka ba mu yarda da ku ba.

Daga Al’amin Dass 0806 211 2880

YA BATUN RUWAN SHA NA GARIN TIGA?

Mun ji Karamar Hukumar Bebeji tana ikirarin ta kashe kudi har Naira miliyan 12 kan harkar ruwan sha a garin Tiga, to amma fa mu duk da wadannan kudade da aka ce an kashe ba mu gani a kas ba, saboda haka muna kira ga gwmanatin jihar Kano da ta gaggauta bincikawa.

Daga 0805 348 3156

KIN GAMA LAFIYA JAGORAR JARIDUN HAUSA!

ALMIZAN ga ta kowa ta ki ta yi wuyar gani. An buga an bar ki, domin ke dashen Allah ce mai wuyar tugewa. Ina gurguwar jaridar nan ta Kinkinau a Kaduna? Za ku gama yada irin naku sharrin ku sulmuya. Ba za ku iya ja da ginin da Shaikh ne ya dora harsashensa ba. ALMIZAN ce ta tattataro masu karanta ta a Kudu da Arewa. Izalawa, Darikawa da Shi’awa duk suna rububin saye. Aminu Bara’a ya ce ku bi a hankali kowa zai sami nasa kwafen. Ina Musulmin Nijeriya ku taro ga muryarku. Rebaren ko Pasto fadi ra’ayinka mai ma’ana duk a buga a cikin ALMIZAN.

Daga Abdullahi Gambo Katsina 0802 679 4453

ALLAH YA KARA ZAFIN CIWO GA SHARON

Duk mai kaunar Annabi da Iyalan Gidansa (SAW) ya ce, amin ga addu’ar Allah ya kara tsananin zafin ciwo ga Sharon (LA), ya kashe shi, ya jifa Jahannama, amin.

Daga 0806 211 2880

HABA BURAZUN MINNA!

Yanzu a ce yaron Malam Hasan Gimba ya rasu a rasa wanda zai aika da sakon ta’aziyya ta ALMIZAN?

Daga Attahiru Garba Kano 0802 324 6387

SHARIFAN JIHAR KANO KU TAMBAYI HAKKINKU

Assalamu alaikum. Sharifan jihar Kano kada ku yi kauron baki, ku tambayi Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau hakkinku da Allah ya ce a ba ku daga cikin baitulmalin jiha tunda shari’a ta kankama a jiha. Daga Jinjiri Sani Goron-Dutse Kano 0802 692 4111

SANI SAMI MUSULMI NE KUWA?

Assalamu alaikum. Ina so in tambayi Sarki Zuru, Sani Sami, shin ko shi Musulmi ne? Domin maganar da ya yi a BBC cewa Shehu Danfodiyo ma bai sha da dadi ba a Zuru, ya sa nake tambayar shin Sani Sami Musulmi ne kuwa?

Daga Muhammad Sani Roni Rigasa Kaduna

YA BATUN KAI MALAMANMU ASIBITI ZUWA WAJE?

Assalamu alaikum. Don Allah gwamnatin jihar Bauci me ake ciki ne game da batun kai Malamanmu da suka yi hadarin mota zuwa kasar waje domin jinya?

Daga Murtala Ahmad (Mabson) Bauci 0802 679 4157

ALLAH YA FARA AMSAR ADDU’ARMU

Mun gani a fili Allah ya fara amsar addu’amu a Sakkwato. ’Yan tallar sharri karshenku ya zo a Sakkwato. Kun rasa makama, ku dawo ku bi Ahlul Baiti.

Daga 0802 427 9229

HABA MASARAUTUN GARGAJIYA KANO, SAKKWATO DA ZAZZAU

Nasiha ga masarautun gargajiyar Kano, Zariya da Sakkwato. A gaskiya abin kunya ne yadda kuka manta da kaburburan kakanninku a Lokoja suka zama jujin zubar da shara.

Daga 0802 509 2151

KUN MANTA DA “ASSARIKU WASSARIKATU NE?”

Shari’ar gwamnatin jihar Kano ta takaita ne ga “wala takrabuzzina…” watakila sun manta da “assariku wassarikatu.”

Daga Ashiru Umar Bakori da Mu’awiyya Umar Usman R/Lemo 0805 266 8202

MUSULMI MU RINKA KUSANTAR JUNA

Assalamu alaikum. Musulmi mu hada kanmu ta hanyar kusantar juna da bai wa juna uzuri domin tunkarar makiyanmu wadanda kullu yaumin jinin Musulmi tamkar wata zuma ce a wurinsu.

Daga Ibrahim Zone E 0802 602 8213

IDAN BA ZA KU IYA BA

Mahukuntan kasar nan idan ba za ku iya kare lafiyarmu da dukiyoyinmu ba, to ku bar kowa ya mallaki bindiga don ya kare kansa.

Daga 0802 469 3273

SHIN BA KU DA WAKILI A RIJAU NE?

Assalamu alaikum. Wai don Allah ALMIZAN ba ku da Wakili a Rijau, Kontagora, Zuru da kewaye ne? Don ba mu cika ganin labaran wadannan garuruwan a cikin jaridar taku ba.

Daga Alkasim Rijau 0805 512 2898

WANDA YA MUTU BAI YI JIHADI BA

Duk wanda ya mutu bai yi jihadi ba, to ya mutu a kan wani yanki na kafirci.

Daga 0804 229 6604

KAI! GASKIYA ALLAH YA SAKA WA MALAM ZAKZAKY (H)

Assalamu alaikum. Gaskiya mun ga labarin zuwan Malam Zakzaky garin Lokoja. Wallahi ni da sauran abokaina ba mu taba sanin cewa wadannan bayin Allah na kwance a Lokoja ba sai da muka ji Malam Zakzaky ya ziyace su. Don haka muna farin ciki da wannan abu. Kuma Allah ya saka wa Malam Zakzaky (H) da alheri. Muna son don Allah ku rubuta mana tarihin wadannan bayin Allah da yadda aka yi aka kai su can.

Daga Tanko Muhammad Abuja 0805 776 6277

HATTARA DAI ’YAN NIJERIYA!

Assalamu alaikum. ’Yan Nijeriya mu kula kada tsaffin kurayen Kudu da na Arewa su sa mu yaki da juna don biyan bukatar kansu.

Daga Aliyu Salisu Kaduna 0803 600 9231

DUK NA ANNABI YA CE AMIN!

Allahumma salli ala Muhammad wa ali Muhammad. Ina rokon Allah (T) Ubangijin sama da kasa, Ubangijin Jibrilu da Mika’ilu da Isra’filu, Ubangijin Isa da Musa da Manzon Rahama. Ubangiji mai saukar da ruwa daga sama, ya fitar da tsirai daga kasa. Allah ka gaggauta sakayya ga duk wanda ke da hannu ko da na farin ciki ne ga abin da aka yi wa ’yan uwa a Sakkwato. Allah yadda suka yi abin da ba a taba yi wa Musulmi ba a Sakkwato, Allah ka yi masu sakayyar da ba ka taba yin irin ta ba a Sakkwato. Allah mun san irin talalar nan ce da kake yi wa azzalumai har su dauka babu kai, amma kuma akwai ka, sai su dauka sun fi ka karfi. Ya Allah ka gwada masu kai ne karfi, kuma kai ne Mahalccin karfi. Allah ka yi masu abin da ka yi wa iyayensu bayan abin da suka yi wa Imam Husaini a Karbala. Ya Allah ka gwada mana muna tare da masoya gidan Manzonka Muhammad (SAW).

Daga Muhammad Sakkwato 0805 972 6449

GA HANYAR KAMUWA DA KANJAMAU

Albishirinku matasa ga dama ta samu ta hanyar kamuwa da cutar kanjamau a saukake, ita ce yin jima’i ba tare da aure ba. Don haka sai a ba da himma.

Daga Dan Asabe Dan Tureda Giwa 0806 088 4467

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International