Almizan :Sirrin nasarar Asusun Da’iratul Am a Suleja ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 6 Zulhijjah, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Wakilanmu

Sirrin nasarar Asusun Da’iratul Am a Suleja


Daga Magaji Idris Suleja

A ranar Juma'a ne 22/11/1426 (23/12/2005) ’yan uwa na garin Suleja suka yi walimar godiya ga Allah na tara gudummawa mafi tsoka saboda nasarar da suka samu na asusun Da'iratul Am. Walimar, wadda aka yi a masallacin Juma'a na garin na Suleja ya sami halartar 'yan uwa maza da mata masu yawa.

Cikin jawabinsa, Malam Baba Adamu ya jawo hankalin ’yan uwa ga tsoron Allah da kuma yin abu don Allah, wanda yin haka ne ya kai mu ga samun nasara,'' in ji shi. Malam Baba Adamu, wanda ya wakilci Wakilin ’yan uwa na garin Suleja saboda shi Wakilin ’yan uwan ya yi tafiya don sada zumunci, ya ci gaba da cewa, “kada ’yan Suleja kadai su yi tutiya da cin wannan kofi, a'a, duk da'irar da ke karkashin Suleja kamar su Lambatta, Kaduna Road, Zuba, Abuja da Gwagwalada, su ma za su yi tutiya da godiya ga Allah da samun wannan nasara. Domin su ma akwai tasu gudummawar a wannan samun nasara.”

Haka kuma Malam Baba Adamu ya ci gaba da cewa ko a bangaren tara kudi ba mune muka fi tara kudi ba, a’a, ’yan uwa na Kaduna sune suka fi tara kudi a wannan yanki. Kawai dai ’yan uwa na Suleja sun fi su sadaukarwa ne, in an kwatanta yawan da'irar Kaduna da ta Suleja.

A tattaunawar da ALMIZAN ta yi da Malam Baba Adamu, ta fara ne da tambayarsa ko me yake ganin ya jawo wa wannan da'ira irin wannan gagarumar nasara da ta samu?

Sai ya ce, “abin da ya kawo wa wannan da'ira wannan gagarumin nasara, ba wani abu bane illa sadaukarwa da kuma biyayya. Duk lokacin da aka ce ga wani abu da za mu yi, to muna la’akari da muhimmancin abin. Kuma mu ginu a kai. Wannan ne ya sa muka samu wannan nasara da kuma wannan matsayi da muka kai.”

ALMIZAN ta tambaye shi ko nawa wannan da'ira ta sami tarawa har ya kai ta ga wannan nasara? Sai Malam Baba ya ce, ''Duk da dai za mu iya cewa wannan gagarumin kyauta da muka samu ba wai iyawarmu bane, ba kuma wani kokari na a zo a gani ba, abin da za mu iya cewa shi ne kyauta ce daga Allah. Domin babbar da'irar da muke karkashinta ta kawo gudummawa fiye da namu, mu mun kai N650,000:00, su kuma N660,000:00. To amma irin wannan kokari da muka yi har muka kusa zuwa kan-kan-kan da babbar da'ira, shi ya sa muka sami wannan babban matsayi.

An tambaye shi ko wane irin sirri suka yi amfani da shi a wajen tara irin wannan gudummawa? Sai ya ce, Ba wani sirri illa sadaukarwa, addu'o'i, da kuma daukar matakai na yadda za mu hada wannan kudade. Ba wai wata dabararmu bace, a'a, al'amari ne na Allah da kuma sadaukarwa na 'yan uwan wannan da'ira, inda da zarar an ce ga wani abu daga Malam, to akan yi himma akan abin.”

Shin wane kira Malam Baba Adamu yake da shi ga sauran da'irori dangane da wannan asusu? Sai Malamin ya ce, “kiran da zan yi shi ne ga mu kanmu, domin sauran da'irori sun fi mu ci gaba. Sai dai abin da zan gaya mana lallai mu sake lale, domin wannan ba wai mun yi wani abu bane da za mu kwanta mu yi barci. A'a, za mu tashi ne mu ci gaba da sadaukarwa, domin mu ga mun cimma samun babban kofi da Malam zai ba mu da hannunsa mai albarka, mu kuma samu yardar Allah. Domin ba wai an ba mu kofi bane kamar yadda ake ba 'yan kwallo ba, a'a an ba mu ne domin ya kara mana himma da sadaukarwa har mu kai ga samun yardar Allah gobe kiyama.”

ALMIZAN ta cancanci yabo

Jinkirta karin farashi sai yanzu

Daga Danjuma Katsina

Kila da za a yi tambayar ina ne a duniya farashin abu ya fi saurin tashi gagab, nan da nan? Ina jin babu kamar Nijeriya.

Abin kamar almara, a kasar nan ne Shugabanta ya fito ya ce bai san cewa farashin kananzir, abin bukata sosai ga mai karamin karfi, ya fi na fetur da dizel na masu hannu da shuni ba sai da aka shaida masa.

Daga hawan Obasanjo ya yi kare-karen kudin mai, karin da ya haifar da tashin farashin komai, har da goro wanda ake kasawa a tire ana yawo da shi a titi.

Har yanzu Hukumar NEPA, ko in kira ta da sabon sunanta, PHCN, babu wani kokarin da ta yi na inganta harkokinta. Kullum lamarin sai kara lalacewa yake yi, kamar wanda ke saman babbar bishiya ne ya sulmayo rijiya. Wannan ya sa daruruwan kamfanoni sun kulle; wadanada ke rayuwa kuma suna rayuwa ne a wata irin masifar tsadar yanayi.

A Kano kawai, kungiyar masu kamfanonin sun bayyana wa duniya cewa sama da kamfanonin ’ya’yansu 500 aka garkame don ba wutar lantarki, babu kuma man da za a iya gudanar da su.

Sun ce ko an samu man yana zuwa ne da tsadar gaske, wanda aikin, in an yi shi sai dai a yi faduwa. Kungiyar ta ce da yawa masu kamfanoni sun shiga wani hali saboda wannan yanayin da suka shiga.

Babban Shugaban Hukumar NITEL, wani Bature ya bayyana a wata hira da aka yi da shi cewa idan akwai wutar lantarki, NITEL na kashe kasa da Naira miliyan 500 ne a wurin gudanar da tashoshinta a kasar nan a duk shekara. Amma a rashin wuta, da hikima da dabaru suna kasha sama da Naira biliyan biyu a kowace shekara. Wannan ya janyo NITEL na cikin wani mawuyacin hali, shi ya sa ma suka kara kudin ayyukan da suke wa jama’a.

Tsadar gudanar da kamfanoni ya sa hatta masu cin ribar biliyoyi kuka suke. Manyan masu bayar da hanyoyin sadarwa irin su MTN, V-mobile, Glo da sauransu, da an yi rubutu a kan cewa Nijeriya ta fi ko’ina tsadar waya a duniya, sai ka ji sun ce Nijeriya ta fi ko’ina tsadar gudanar da ita a duniya.

Ba NEPA ba, mai da za a zuba a injuna a cikin sauki, dole sai an bi barauniyar hanya ake samowa da tsadar gaske.

Duk wani mai harka dole ya rika neman wace hanya zai bi ya fid da duk kudinsa da ya kashe a abin da yake yi? Kowa ya sani, duk inda a yanzu ake biyan dari a motar haya, yanzu ya nunnuka.

Ga kuma irin halin ’yan kasa, sau da yawa kamar jira suke a ce wata dama ta samu, sai ka ga an yi amfani da ita, wani sai ya zo da wannan damar zai hau ya yagi nasa kason. Misalin da zan iya kawowa shi ne, idan aka ce azumin watan Ramadan ya matso da kuma ya shigo, duk wani kayan bukata sai kawai ya yi fiffike ya filfila. Ka rasa dalili. Hatta kayan lambu, wanda in mai azumi ya kai su yake fara nema ya buda baki ya yi hamdala, sai kawai su mike tsaye, banda sauran kayan bukatu. Kuma don rashin ta ido da an ce azumin ya tafi, sai su sami inuwa su zauna.

Cikin shekara daya komai ya tashi a kasar nan, wani sau daya, wani sau biyu, wani ma sau uku. Wannan annoba ba ta bar hatta kayan dab’i ba, ko kuma gidan jaridu. Dab’in, tunda da wutar lantarki ake yi, mai ya tashi, rashin wuta ya karu, don haka mai kamfanin tunda ba sadaka yake yi ba, shi ma dole ya kara kudi domin ya tabbatar ya yi daidai da wahalarsa. Takarda ta wuntsula, ta kuma birkice, sannan ta kara kudade.

Yo!!! Mi!!! Ai wannan dole ne domin ai ita ma ’yar Nijeriya ce. In kuma za ka yi mata adalci sai ma ka ce mata a samu wurin zama lafiya, domin abin yin takardar saye ake, inji ke yin ta mai amfani da wutar lantarki. Ko mai karatun baya zai fassara wa mai bi na amsar wannan.

Wannan ya sa kusan duk shekara jaridu ke kara kudaden kansu. Duk mai sayen jaridu ya san wannan. Ba zan kawo sunayensu ba domin kar su ce na ba da misali da su ba izni. Amma akwai mujallar da ta yi karin kudi Naira Hamsin-Hamsin sau biyu a cikin wata shida kawai. Hamsin din farko duk ta yi dogon sharhi da ban hakuri. Hamsin ta biyu sai ta murje idanu ta ce a yi hakuri da su, mai iya mallaka, ya mallaka.

Wata jarida kuwa cikin sati tara ta yi kari sau biyu. Tana saba’in ta zama tamanin. Sai kawai ta dake ta koma dari. Sai ka zo saye ka mika darinka kana jiran canji, sai mai saidawa ya ce ai ba ka da komai.

Wata jaridar karin dari ta yi baki daya a lokaci daya. A sharhinsu suka ce hali da yanayin Najeriya ya kawo haka. Wasu jaridun tuni suka tarkata yanasu-yanasu suka ce sun bar fagen. Wasu kuma sun yi wata ya hakima suka ce fitowarsu yanzu ba koyaushe bace, amma akai-akai ne.

Masu harka da jaridu sun dade suna mamakin yadda ALMIZAN ta dau lokaci ba ta kara kudi ba, duk da kuwa cewar ga yadda kasar take, kamar yadda na kawo a baya.

Sannan ga jaridar ba wani talla take samu ba, wanda kan mai da mata kudinta daga wanda yake karuwa kullum a wurin fitowarta. Jaridar ta tausaya tare da tafiya da makarantanta a halin da ake ciki, su su yi hakuri da daurewa da ci gaba da saye. Ita kuma ta dage da fitowa a kudinta. Wannan yanayi da hali ya sha taka rawar da ta sa jaridar ta rika dan samun tsaiko, ka ga wani satin an ce jaridar ta yi husufi.

Duk da dagewa da cijewar da wannan jaridar ta yi da kuma tausayawar da ta nuna na tsawon lokaci ba ta yi kari ba, lamarin ya kai magaryar tukewa, dole ta sa, ba domin ana so ba, sai an kara wannan kudi.

Kamar yadda ita a bangaren jaridar ta dade tana sadaukarwa don ta dade a farashinta kuna saye, makaranta su dauka su ma za su iya wannan sadaukarwa a karin da aka yi domin jaridar ta bunkasa ta kuma ci gaba da tabbata. Zan ba ku wani labari da ya taba shafar jaridar Tempo, wadda kamfanin The News ke bugawa. A zamanin Abaca sai aka dirar masu aka kulle ta. A satin, sai Tempo suka yi shelar cewar ba su iya fitowa saboda an dira a kansu, suka kuma yi bayanin cewa sun yi muguwar asara a wannan dirar mikiya da aka yi musu.

Wannan satin da ba su fito ba sai jama’a suka rinka dandazo wuraren sai da jarida suna ba da kudadensu na Tempo ta wannan satin a Legas suna cewa a kai ma kamfanin, asarar da suka yi sune suka yi asara ba Tempo ba. Kuma ba da wannan kudin alama ce ta suna tare da Tempo a duk halin da suke ciki. Wannan sadaukarwa da nuna tare ta sa kamfanin na The News har yanzu yana fitowa.

Wani misalin da zan kawo shi ne na kamfanin Gidan Rediyo da talabijin na AIT, lokacin da suka sami matsala da Bankin da ya ranta masu kudin da aka kafa su, First Bank, kotu ta rufe gidan watsa shirye-shiryen, aka fara shirye-shiryen gwanjonsa. AIT sun sayi filaye a jaridu suna bayyana halin da suke ciki, masoyansu sai kawai suka kakkafa wasu kamar kungiyoyi na hada gudummuwa a ba AIT, don su hada wannan kudi da kotu ta ce in ta kawo su za a fasa yin gwanjon kamfanin.

Masoyansu sun yi kira ga ’ya’yan su ba da Naira goma kacal. Jaridu sun ruwaito yadda aka rika harhada wadannan kudade ana ba AIT.

Har yanzu kamfanin AIT sai ma abin da ya yi gaba, wanda a yanzu shi kadai ne kamfanin yammacin Afrika da yake watsa shirye-shirye duk duniya a satalayit. A takaice karfin kafar watsa labarai ita ce masu karatu.

Masu karatu su yi hakuri an kara kudi, amma kuna da tabbacin za a samu ingancin filaye masu ilmantarwa.

Ni a nawa bangaren, filin Hantsi ya gama yankewa. Zan rika ba da na satuttuka ga Edita. Zan hutar da shi tambaya ta “Ba ka aiko da Hantsi ba. Zan kuma farfado da filin Rubutu da marubuta domin masu adabi. Zan rika tsakulo rubutun gwanayen marubuta da kuma yadda za a koyar da salo da hikimomin rubutu sosai.

Na san cewa M.M. Awwal zai ci gaba da yadda yake kawo filin Kai Tsaye ba tsoro, wanda na lura filin tsumagiyar kan hanya ce.

Haka nan filin Malam Abubakar Daga Gidan Annabta, ko shi ya ishi mutum guzuri da garkuwa.

Kila Aliyu Sale sai ya hada da shan shayin buzaye domin karin kuzarin yin zirga-zirga domin kara zakulo tabbatattun labarai, ya tabbatar maku da su.

Akwai abin da ya fi ALMIZAN din zama ALMIZAN, wanda kashi casa’in da tara suna sayen ALMIZAN ne domin wannan. Wannan kuwa shi ne jawabin Sharafuddin na duk sati da kuma filin Malam mai amsishin tambayoyinku. Wadannan filaye biyu jari ne na duniya da lahira.

Edita na san ba zai kyale kowa ya huta ba, har sai ya ga cewa ingancin jaridar ya fi karfin duk kudin da ke sayen ta.

Wani abin farin ciki, Ubangiji ya daukaki jaridar nan fiye da duk yadda ake tsammani. Duk wani dan siyasa ya san cewa idan yana son ya ga bayin Allah na hakika sai a Almizan. A shekarar da ta gabata kawai Gwamnonin jihohin Arewa uku suka yi taron manyan manema labarai. Dukkaninsu Editan Almizan na cikin wadanda aka yarda tare da amincewar ya isa, kuma dole a tafi da shi. Lamarin ya kai har cewa ake kamfen din ALMIZAN shi ya ka da Kwankwaso. In Allah ya so jaridar nan za ta kara armashi, gardi, dadi da biya maku bukatarku. Tana bukatar addu’arku da sadaukarwarku.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International