Almizan :Da gangan aka haifar da matsalar aikin hajji ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 6 Zulhijjah, 1426                 Bugu na 699                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Rahotanni

Da gangan aka haifar da matsalar aikin hajji

In ji Malam Zakzaky

H

’Yan uwa na yankunan Azare da Potiskum, sun kai wa Malam Ibraheem Yaqoub Zakzaky ziyara a Zariya ranar Talatar nan da ta gabata.

Da yake yi wa ’yan uwan da suka kawo masa ziyarar jawabi a Fudiyya Islamic Center, Malam Ibraheem Yaqoub Zakzaky ya bayyana jin dadinsa da wannan ziyarar da suka kawo masa. Kodayake ya ce da sun zauna a gida da ya fi, amma ya ce,“insha Allahu na gode da zuwa gaishe ni da kuka yi.”

Malam Zakzaky, ya bayyana takaicinsa a kan yadda aikin jigilar Alhazai yake tafiyar hawainiya a Nijeriya. Ya ce da gangan aka haifar da wannan matsalar. Ya ce, ya ji ana hira da daya daga cikin jagororin Alhazan, amma sai yake cewa, wai wanda aka bar shi ba a dauke shi ba, da ma can Allah bai rubuta zai je aikin Hajji ba, “ai duk wanda ya biya kudinsa, Allah ya kira shi, sai dai wani hana shi zuwa,” in ji Malam Zakzaky.

Ya ce sai ka ga an ba mutum kwangilar jigilar Alhazan, amma ba shi da ko fiffike, sai dai ya je ya yi ta neman jirgin da zai kwashi mutane ya kai su aikin Hajji. Ya ce, a irin haka sai ka ga mutum ya je ya yiwo hayar jirgin da ake kwasar rake a ciki a wata kasa ya zo nan da shi a yi jigilar Alhazai.

Ya tabbatar da cewa da da gaske ake yi ana son yin maganin wannan matsalar, da yanzu an yi. Ya ce da za a ba manyan kamfanoni na duniya kamar Saudi Air, aikin kwangilar jigilar Alhazan Nijeriya, da lokaci guda zai kwashe su bayan an tara masa su waje guda.

Malam Zakzaky, ya kuma nuna takaicinsa a kan yadda kafafen yada labarai, musamman na Yammacin duniya suke nuna Musulmi a matsayin dan ta’adda, addinin Musulunci kuma a matsayin ta’addanci. Ya ce sai dai ta Allah ba tasu ba, domin duk da haka mutane a Turai sai shiga cikin addinin Musulunci suke yi.

Ya nuna damawarsa matuka a kan yadda taron kasashen Musulmi da aka yi kwanakin baya a Saudiyya ya tashi ba tare da ya yi Allah Allah wadai da bayyana danniya da mamaya a matsayin babban kulen da Musulmin duniya suke fuskanta ba. Ya ce, “abin takaicin sai ka ji su ma (Shugabanin kasashen Musulmi) suna amfani da kalaman da Bush yake amifani da su.”

A cikin takaitaccen jawabin nasa, Malam Zakzaky ya nuna goyon bayansa dari bisa dari ga jawabin da Shugaban Iran, Dakta Ahmadinajadi ya yi a ’yan kwanakin nan na share haramtacciyar kasar Isra’ila daga doron kasa, da kuma canza mata mazauni daga Gabas ta Tsakiya zuwa can kasashen Turai. “Tunda a can aka yi kisan Yahudawa, (Holocaust), ai kamata ya yi a ba su waje a wuraren kamar su Alaska su koma can, amma bai kamata wanda ya yi kisa daban, wanda kuma yake biyan ladan kisan daban ba.”

Da ya juya kan yadda Nijeriya take ci gaban mai hakar rijiya, Malam Zakzaky ya ba da misali da kafuwar kamfanonin jiragen sama, idan a baya Nijeriya ta zarce Saudiyya yawan jirage, amma yanzu ga shi bayan ’yan shekaru Nijeriya ba ta da ko fifike, amma Saudiyya tana da jirage sama da 1000.

’Yan uwan da suka kai wa Malam Zakzaky ziyara, da suke karkashin Malam Mustafa Potiskum, sun fito ne daga garuruwan Azare, Potiskum, Maiduguri, Gashuwa, Misau, Jama’are, Zaka, Disina, Zadawa, Gwaza, Dambam, Biu da Baga.

Wani mawakin gwagwarmaya ya rasu!

Daga Musa Jega (musalabbojega@yahoo.com)

Allah ya yi wa dan uwa Malam Nasiru S. Hakimi Jega rasuwa ranar Alhamis 21/Zulkida 1426 (22/12/2005), sakamakon wani mummunan hatsarin mota da suka yi a kan hanyar Biu ta jihar Borno zuwa Kano.

Bayanan da muka samu daga wajen da aka yi hatsarin sun nuna cewa; Malam Nasiru sun sami hatsarin ne bayan da falfelar motar bas din da suke ciki ta zare ta kuma caki kasa inda nan take motar ta fadi ta ci gaba da jujjuyawa. Gaba daya dai mutane bakwai ne suka rasu a cikin motar, daga cikinsu har da wasu ’yan gida daya da su ma suka rasu a hatsarin.

Shi dai Malam Nasiru Hakimi Jega ta jihar kebbi, mawakin gwagwarmaya ne, ya yi wa Manzon Allah waka da Sayyida Fatima Zakiyyah da kuma Malam Zakzaky.

Dan asalin garin Jega ne, ya je jihar Adamawa, wani gari da ake kira Mubi da ke da kan iyaka da kasar Kamaru, inda ya yi makarantar addini a can.

Bayan ya kare ne ya fara sana’a yana zuwa jihar Kano yana sayen kayan shadda ya je can da su ya sayar ya dawo Kano ya sake sayen wasu; a kan hanyarsa ta dawowa a wannan rana ta Alhamis ne suka sami hatsarin.

Ba a samu labarin rasuwar Malam Nasiru ba sai da ’yan uwa Malam Rabi’u Mubi da Yarima Mubi suka je garin Biu suka bincika, musamman da yake an ta buga wayarsa ba ta shiga ba, kuma ya zarce kwanakin da ya saba dawowa, inda suka tarar da gawar Marigayi Malam Nasiru Jega a garin na Biu. A can garin na Biu dai aka yi masa salla, aka binne shi a makabartar da ke kusa da asibitin garin.

Malam Nasiru S. Hakimi dai, sananne ne ga ’yan uwa na yankin Kebbi, ya yi makaranta a Zuru da Jega, kuma ya yi makarantar Haliru Abdu Jega, inda daga nan ya je can Mubi a jihar Adamawa ya karasa karatun nasa a kan tsare-tsaren gidaje.

Kafin rasuwarsa dai, Malam Nasiru Hakimi, Malami ne a wata makarantar Islamiyya ta can Mubi, ya kuma sami kyakkyawar shaida daga jama’ar garin.

Malam Muhammad Dan Shagari cewa ya yi, “wallahi ban taba ganin fadansa ba. Muna zaune da shi tun lokacin da ya zo nan Mubi.”

Shi kuwa Malam Haruna Shinkafi cewa ya yi, “Malam Nasiru mutum ne mai hankali da hakuri. Bai taba yi min abin da ya bata min rai ba duk da cewa muna tare da shi koyaushe.”

Wannan rasuwa ta Malam Nasiru ta girgiza jama’a sosai, musamman da yake yana tashi sosai wujen waken gwagwarmya a wannan yankin. Ya rasu ya bar ’yarsa daya mai suna Zakiyyah, yana da shekaru 29 a duniya. Da fatan duk wanda ya karanta wannan bayanin, zai karanta salati 10 ga Annabi da nufin Allah ya kai ladan gare shi.

Marigayi Malam Nasiru Hakimi Jega

Allah ya yi wa Sulaiman Sabon Gari Rasuwa

Ranar wata Lahadin da ta gabata ne Allah ya yi wa dan uwa Sulaiman Isyaku wanda ke zaune a Matazu Close, Sabon Garin T/Wada, Kaduna rasuwa bayan ya yi fama da wata gajeruwar rashin lafiya.

Marigayi Malam Sulaiman Isyaku, mutum ne wanda ’yan uwa na Sabon Garin da sauran ’yan uwa suka shaida da himma da hazaka a duk wani abu da aka ce na gwagwarmaya ne.

Daya daga cikin abokan Marigayin, wanda kuma suna tare kusan ko da wane lokaci, musamman a harkar gwagwarmaya, Malam Ibrahim Mujaheed, ya shaida mana cewa Suleiman dan uwa ne wanda har kullum shi dai burinsa ya sami shahada, “don haka ne muke addu’ar tunda ya mutu da wannan buri a tare da shi, Allah ya karbe shi a matsayin Shahidi,” in ji Mujaheed.

Malam Ibrahim ya ci gaba da shaida mana cewa Marigayi Suleiman ya kasance mutum ne wanda duk inda ake harka ta addini, to yana gaba-gaba, “hatta waki’ar Sakkwato ma ya je kuma har ya samo rabo, domin ya dawo da rotsi a ka” in ji abokin nasa.

Ta fannin infaki kuwa, Marigayi Sulaiman mutum ne mai himma a duk lokacin da ake neman infaki don wannan harka. “Saboda haka mun addu’a ga Allah ya gafarta wa Sulaiman. Allah ya amfanar da abin da ya bari,” inji Mujaheed.

Marigayi Sulaiman Isyaku ya rasu ya bar Iyayensa uwa da uba, matan aure biyu da ’ya’ya shida.

Imam Jawad (AS) ya karbi imamanci tun yana yaro karami

Na'ibin Limamin Juma'a a birnin Tehran, kuma Shugaban Hukumar kare tsarin Musulunci a Iran, Ayatullah Ahmad Jannati ne ya jagoranci dimbin al'ummar musulmi sallar Juma'ar da aka gabatar a babban masallacin Juma'a da ke Jami'ar Tehran a kwanakin baya.

A lokacin da yake gabatar da hudubobin sallar Juma'arsa, Ayatullah Jannati ya fara ne da kiran al'ummar musulmi da tsoron Allah, kamar yadda aka saba a kowace huduba.

Haka nan kuma Ayatullah Jannati ya yi gajeren bayani kan rayuwar Manzon Allah (SAWA) da kuma kasancewar rayuwarsa Alkur'ani ce kamar yadda ya zo a ruwaya. Sannan ya nuna cewa dukkanin mumini na kwarai yana so rayuwarsa ta zama koyi ne da rayuwar Fiyayyen halitta, Manzon tsira (SAWA).

A lokacin da yake magana kan munasabobin da suka zo a makon da ya yi hudubar da kuma makon da zai biyo, Ayatullah Jannati ya ambaci shahadar Imam Jawad (AS) wanda ya zo a karshen watan Zulkida.

Ayatullah Jannati ya tabbatar da cewa shi Imam Jawad (AS) ya kebanta da cewa shi ne kawai cikin Limaman shiriya, wanda ya karbi ragamar tafiyar da al'umma a lokacin yana shekarun da ba su kai na mukallafi ba, watau yana yaro karami dan shekara takwas ko tara. Imam Jawad (AS) dai ya yi shahada ne a ranar 29 ga watan Zulka'ada shekara ta 220 bayan hijirar Manzon Allah (SAWA).

Mutane 27 sun rasu a hatsarin mota a Zamfara

Wani mummunan hatsarin motar daukar kaya da aka yi da misalin karfe 4:30 na asuba a kan hanyar Gusau zuwa Sakkwato a karshen watan jiya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 27. Ciki har da wasu mata su takwas.

Rahoton jaridar DAILY TRUST da ake bugawa da harshen Turanci ya nuna cewa wannan mota tana dauke ne da buhunhuna 200 na hatsi, sannan kuma kimanin mutane 87 suna ciki, yayin da ta fada cikin wani babban rami a bayan garin Bakura.

Rahoton ya kara da nuna cewa hatsarin ya faru ne da sanyin safiya yayin da mutane ba su riga sun fito neman abinci ba. Saboda haka an sami karancin wadanda za su gudanar da ayyukan ceto. Shi ya sa ma da yawa wadanda suka rasa rai sun mutu ne saboda matsalar makara da buhunan hatsin suka yi masu, abin da ya jawo rashin isasshen numfashi.

An kai gawawwakin wadanda suka rasa rayukansu babban asibitin garin Bakura ne, sannan kuma wadanda suka tsira da rayukansu suna kwance a asibitin suna karbar magani.

Hanyoyi a baki dayan Nijeriya dai suna fama da matsalolin da suka hada da rashin tsaro saboda yawan samun ’yan fashi da makami da ake yi a kan hanyoyin, sannan kuma da yawa daga cikin hanyoyin ba su da kyau.

Kawo ya zuwa yanzun dai jami’an kula da kaiwa da komowa a kan hanyoyi, ‘Road Safety‘ sun fara gudanar da bincike kan wannan hatsarin.

Wani binciken da wasu masana suka yi, sun gano cewa hatsarin mota na daya daga hanyar da ta fi lakume rayukan jama’a a Nijeriya.

Ya kashe uwarsa mahaifiya

Daga Ahmad M. Misau

Ranar Laraba 7/12/2005, al’ummar da ke zaune a layin Mai unguwa Guga, Hayin Taro-taro, Rigasa, Kaduna suka hantse da wani al’amari mai ban tausayi da firgici, inda wani matashi dan shekara 22 mai suna Bello Sulaiman ya kashe mahaifiyarsa mai suna Malama Safiya Sulaiman har lahira.

Mai unguwa Malam Abubakar, wanda aka fi sani da suna mai unguwa Guga ya ce biri ya yi kama da mutum, domin kuwa shi wannan matashin a bara ya same shi inda yake neman a raba musu gadon uwar tasu, amma shi mai unguwa ya ce ai ba a raba gadon wanda ke da rai. Amma bayan wata shida ’yan uwansa sun kawo karan sa inda suka ce yana fada musu da su yi hankali don sai an raba musu gidan. Sai mai unguwa ya kira shi ya ja masa kunne tare da yi masa nasiha.

Da yake wannan kudurin nasa na tare da shi, a ranar Talata, 6/12/2005, kwana daya kafin ya yi wannan aika-aika ya yi fada da wadanda ke haya a gidan har ya babbale kyauren dakunansu, har ma ya yi yunkurin ya doki matar wansa.

Ganin haka sai uwar ta yi masa fada, amma bai daina ba. Ita kuwa sai ta sanar wa ’yan sanda har ma suka kama shi suka tsare, suka kuma ja masa kunne kafin su sako shi da yamman ranar Talata.

A ranar Laraba da misalin karfe 11:00, lokacin mutanen gidan sun fita, kuma daya daga cikin yayyansa yana waje yana kwabin kasa don ya yi gyaran kyauren kofa, ita kuma uwar tasu tana alwala a kofan daki, sai ya nemo shirgegen faskare inda ya yi ta shema mata sai da ya ji ba ta numfashi.

Da Wan nasa ya ji alamun ana duka, sai ya yi maza ya shigo gidan inda ya iske mahaifiyarsu kwance jina-jina. Sai ya yi ihu, shi kuma Bello ya ruga da gudu. Amma cikin ikon Allah aka damke shi.

Da aka kama shi har matasa sun yi niyyar shi ma su kashe shi, amma mai unguwa Abubakar ya yi nasarar hanawa, ya gama shi ga rundunar ’yan sanda na Rigasa.

ALMIZAN ta bincika don ta gano ko Bello ya taba samun tabin hankali, wasu sun ce ba shi da tabin hankali, amma yana shaye-shaye. Wasu kuma sun ce akwai dai alamun rashin hankalin.

ANSARUL MAHDI sun kai ziyara ofishin ALMIZAN da ke Kano

A ranar Asabar din da ta gabata ne jami’an gudanarwa da kuma daliban makarantar ANSARUL MAHDI suka kai ziyarar aiki ofishin shiyya na ALMIZAN da ke Kano.

Manufar ziyarar dai kamar yadda Daraktan Cibiyar Mala Muhammad Jakara ya bayyana shi ne, don kara dankon zumunci, fahimtar juna da kuma bude ido kan yadda ake gudanar da aikin ALMIZAN.

Yayin wannan ziyara wadda ta hada har da ’yan uwa mata da dalibai ’yan Cibiyar, an tattauna kan wasu matsaloli da masu ziyarar suka bijiro da su, inda a karshe aka fahimci juna.

Da yake musu jawabi, Manajan Shiyya na kamfanin I. M. Publications, Alhaji Hasan Isyaku, ya bayyana cewa wannan ofis shi ne ke kula da garuruwan da ke makwabtaka da garin na Kano wajen raba jaridar ta ALMIZAN da kuma sauran kayayyaki da kamfanin ke bugawa.

Ya ce shekaru biyu da suka gabata, jami’an kamfanin sun yi wata ziyara zuwa sassa daban-daban na kasar nan da nufin inganta harkokin kamfanin, yana mai bayyana wannan ziyara da ’yan ANSARUL MAHDI suka kawo da cewa mai matukar muhimmanci ce da karfafa gwiwar daukacin ma’aikatan.

Alhaji Hasan ya kara da cewa ta hanyar irin wannan tuntuba a kan warware matsaloli da daman gaske, musamman ma alakar makaranta jaridar da kuma jami’an da ke gudanar da ita.

Daga nan sai ya jawo hankalinsu da cewa shi aikin jarida aiki ne da yake bukatar gudummawar jama’a da daman gaske ta fuskacin sadaukar da kai, aiki da abin hannnu da kuma lokaci.

Lokacin da yake amsa tambayoyin masu ziyarar dangane da matsalolin da akan samu na rashin fitar labari a kan lokaci, Manajan Shiyyar ya ce a wannan zamani namu da aka samu fasahar zamani, zai yi kyau a ce masu aika rahotanni ko mukaloli su rinka yin amfani da fasahar zamani ta sakar sama wajen buga abubuwansu suna turawa da su ta adireshin jaridar na sakar sama wanda ke jikin jaridar. Wannan, a cewarsa, shi ne zai sa nan da nan mukalolinsu su rinka fita.

Haka kuma wata ’yar uwa ta yi tambaya kan yadda mata ba su da wani takamaimen fili a cikin jaridar, inda Alhaji Hasan ya ba ta amsar cewa wannan kule ne ga su matan wadanda suke yin kasa a gwiwa wajen yin rubuce-rubuce.

Ya ce a baya an fuskanci makamanciyar wannan matsala a wajen fitar da Mujallar MUJAHIDA, wacce duk da cewa ta mata ce, amma kuma mafi yawan rubuce-rubucen da ke ciki mazajensu ne ke yi. Don haka ya ce, ya kamata mata su yi ta-maza su dauki alkalami su rinka rubutu ta yadda za a kawo karshen irin wadannan korafe-korafen.

Alhaji Hasan ya yi wa jami’an Cibiyar rokon su samu lokaci don kai makamanciyar wannan ziyara a can babban ofishin ALMIZAN don su gane wa idanunsu hakikanin yadda ake gudanar da aikin jaridar.

Daga karshe ya bayyana jin dadinsa a madadin sauran jami’an gudanarwa da daukacin ma’aikatan kamfanin dangane da wannan ziyara da ANSARUL MAHDI suka kawo wa ALMIZAN, yana mai bayyana fatan cewa hakan zai kara musu dankon zumunci.

Tun da farko da yake jawabi a wajen, Daraktan Cibiyar, Malam Muhammad Jakara ya bayyana cewa ziyarar dai ta bude ido ce da kuma fahimtar juna, sannan ya koka kan yadda ake samun jinkiri wajen buga labarai, ko kuma rashin zuwan Wakilan ALMIZAN a wuraren taruka na Harka Islamiyya a Kano.

Daga nan ya yi addu’a da fatan alheri ga ma’aikatan na ALMIZAN saboda kwazonsu da jajircewarsu a kan aiki.

Yayin wannan ziyara dai, Daraktan makarantar na tare ne da Malam Sunusi Dandishe, da kuma wani jami’i, yayin da shi kuma Manajan Shiyyar suka karbi masu ziyarar tare da Malam Hasan Muhammad na sashin labarun kasashen waje na ALMIZAN.

Malam Yakubu Yahya ya ziyarci Liman Katagum

Daga Alhaji Lawal K/Madaki

A ranar Talata 6/11/1426 (6/12/2005) Madrasatul Fudiyya Liman Katagum ta yi bukin saukar karatu na dalibai 54. Da yake gabatar da jawabi ga dimbin al’ummar da suka taru a garin na Liman Katagum, Malam Yakubu Yahya Katsina ya gargadi al’ummar Musulmi dangane da muhimmancin aiki da Alkur’ani, tare da tsayin daka na ganin shi ke hukunci a doron kasa.

Malam Yakubu ya ci gaba da cewa tunda yake wannan taro yana da nasaba ne da Alkur’ani kuma har ga shi ma muna bukin karrama wasu dalibai da suka sauke, to in kuwa haka ne ya zama tilas mu ga cewa muna riko da wannan Alkur’ani, tare da aiki da shi kamar yadda yake bukata.

Har ila yau Malam Yakubu Yahya Katsina, ya tabo janibobi daban-daban wadanda suke nuni da gazawar wannan al’umma dangane da rikonta da Alkur’ani. “Kodayake a duniya mutanen Nijeriya sune kan gaba wurin karatun Alkur’ani, sune kan gaba wurin yada Alkur’ani. Kai hatta a yawan salla da yarda da kaddara babu ya al’ummar Nijeriya. Amma a fannin aiki da shi kam, mun ci baya.”

Malamin, a duk jawabansa a wannan muhalli, ya yi su ne dangane da Alkur’ani, tare da kiran al’umma su tashi tsaye domin ganin wannan addinin ya tabbata.

Malam Yakubu Yahya ya gargadi irin jama’ar nan da ke sukar Shi’a, tare da neman fitar da duk wani dan Shi’a daga da’irar Musulunci, ya ce, to su sani sun kama babban aiki ne, “domin kuwa duk wanda ke son zagin Shi’a, to dole ne ya fara daga kan Imam Ali (AS) da Fatima ’yar Manzon Allah (S) domin kuwa sune tushen Shi’a, in kuma har mutum ya ki yarda har ya zage su, to ya sani dole a ba su nasu rabon na zagin kafin ya iso kanmu.”

Daga karshe sai ya kare wannan jawabi nasa da jawo wasu ayoyi daga Alkur’ani mai girma tare da hadisan Manzo (S) kan muhimmancin abin da yake magana a kai.

Ita dai wannan saukar karatu an hada ta ne tare da neman tallafi domin ci gaba da aikin makarantar ta Fudiyya Liman Katagum, kuma an tara kudi sama da dubu 160 har da alkawura.

Hedimastan makarantar, Malam Dahiru Aliyu L/K ya tabbatar mana da cewa wannan buki shi ne karo na biyar da makarantar ta gudanar. Amma wannan shekarar ita ta fi kowace shekara yawan masu sauka. Kuma ya ce daga cikin dalibai 54 da suka yi sauka, 26 maza ne, ’yan mata 20, sai kuma matan aure 8.

Garin Liman Katagum ya cika makil da al’umma daga ko’ina cikin fadin jihar Bauci, domin sauraron wa’azin Malam Yakubu Katsina.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International