Almizan : Obasanjo ta-zarce: Ba wanda ya isa ya saye mu ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 6 Zulhijjah, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Tattaunawa

Obasanjo ta-zarce: Ba wanda ya isa ya saye mu


In ji Honorabul Alhaji Abubakar Bawa Bwari

Daga Shu’abu Lili


Alhaji Abubakar Bawa Bwari dan Majalisar Wakilai ne mai wakiltar mazabar Suleja, Tafa, da Gurara, kuma shi ne mai tsawatarwa a Majalisar wakilai. Tun kimanin watanni shida da suka wuce ALMIZAN take ta dana tarkonta don ta kama shi, amma tarkonta bai yi kamu ba sai a ranar Asabar 31/12/2005 ta rutsa da shi a wajen radin sunan dan da aka haifa wa Shugaban Karamar Hukumar Tafa na jihar Neja.

Bayan maganganu cikin raha da barkwanci tsakaninsa da Wakilin ALMIZAN Magaji Alhaji Idi Zariya, inda ya kwatanta cewa yadda yake tsoron ’yan sanda haka yake tsoron ’yan jarida, sai ya koka da cewa al’amura suna yi masu yawa. “Albashina Naira dubu 150 ne, amma ina biyan ma’aikatan ofishina Naira dubu 170,” in ji shi. Ga dai hirar kamar yadda take.

ALMIZAN: Muna so mu san tarihin Honorabul.

HON. BAWA BWARI:- Ni dai an haife ni ne a Bwari, kuma na yi firamare dina a Bwari wajen 1970. Lokacin ashe ba a sa sunana ba, in aka je kiran suna a aji irin na safen nan, ko dai a kira ni a farko, ko kuma a kira ni a karshe. Wata rana kuma sai a yi kuskure ma ba a kira sunana ba. A karshe sai a ce waye bai ji sunansa ba? Sai in ce nine. A ce meye sunanka? Sai in ce Abu Bawa Bwari. To ashe ba na cikin ‘list.’ To sai aka ce in fito in koma gefe, sai aka zo gwada ni, aka ce in sa hannuna na dama ta saman kaina in tabo kunnena na hagu. Irin dai yadda ake gwada yaro a da kafin a dauke shi a firamare. To a karshe dai a Sakkwato na ci gaba da firamare dina. Daga Sakkwato na je Gusau, a can ne na kare firamare dina. Kuma muka dawo Sakkwato. Da aka raba jiha a 1976, sai muka koma Minna. Nan na kare makarantar. Saint Peters ake kiran makarantar a lokacin. Yanzu ana kiran makarantar Madaki Primary School. A Sakkwato kuma na yi Saint Paul, a yanzu ana kiran makarantar Muhammad Bankano. A Gusau kuma na yi Lady Of Fatima, amma yanzu ban san yadda ake kiran sunan makarantar ba.

Daga nan sai a 1977 na je Gov. Sec. School Suleja. Da na gama a 1982, sai na je School Of Basic Studies Zariya, na gama a 1983. Sai na je na yi karatun digiri dina a ABU Zariya. A 1986, sai na je bautar kasa a Sakkwato. Na yi karantarwa a FCC Sakkwato. Ina gama bautar kasa sai na koma ‘masters’ dina a kan ‘Regional Planning’ a ABU Zariya. Sai aka ba ni aiki a ‘Town Planning Division’ na jihar Neja a 1988. Ina ‘masters’ ina aiki. A 1994 na dawo na fara aiki nawa na kaina tunda dai ni ‘Town Planner’ ne. Sai muka shiga ‘consulting’ a kan ‘Town Planning’ din.

To muna cikin wannan ne a 1998 sai aka gayyace ni UNPP don na shiga siyasa. Da kyar na yarda na shiga. Muka ci wancan zaben, daga baya aka soke. Da Abaca ya rasu, Abdussalam ya hau, sai aka shirya mana wani zaben a jam’iyyar PDP da aka kafa. Lokacin ban so in koma ba. Kodayake na ci zaben da aka yi, amma na ci tsananin wuya. To amma tunda na koyi wasu abubuwa sai na ga, to ai ba komai, na dawo muka yi PDP. Na je National Assembly. A nan National Assembly na zama Chif Whip. Aka sake zabe a 2003 na sake ci. Na yi aure a 31/12/1993, ina da yara uku, kuma suna nan Abuja.

ALMIZAN:- Jam’iyyarku ta shiga rikicin cikin gida ko me za ka ce a kan haka?

HON. BAWA BWARI:- TO ai dama haka yake, ya zama dole a samu irin wadannan abubuwa yau da kullum. Amma mafi muhimmanci shi ne in aka shiga irin wannan rikici a gama ba tare da tafiya ta ji wani ciwo ba, ko ta kawo wa jiharka matsala, ko kuma ta kawo wa kasa matsala. Wannan ita ce addu’armu. Ita dama siyasa dole ne a samu irin wadannan a ko’ina a duniya. Ko da a Amurka wadanda suka dade suna yi ana yin haka. Addu’ar da muke yi kullum in aka je warware matsalolin, ya kasance an warware su ba tare da an samu wani abin da zai bata jam’iyyar ko kuma kasar ba.

ALMIZAN:- Yaya kake ganin rikicin Atiku da Obasanjo?

HON. BAWA BWARI:- To dama ai kamar yadda na gaya maka ne, ba yadda za a zauna ba a samu wata matsala ba, kodayake ban san abin da ya hada su ba, tunda rikicin manya ne. In aka bukaci mu shiga mu shirya su, to za mu yi. Kuma ma rikicin ba kamar yadda ake gani bane. Ku ’yan jarida ne kuka yayata shi.

ALMIZAN:- Mutane da yawa suna rade-radin za ka fito takarar Gwamnan jihar Neja, ko meye gaskiyar wannan?

HON. BAWA BWARI:- E, to a gaskiya haka abin yake, mutane da yawa sun zo mun yi magana a kan wannan batun. Abin da zan ce maka a takaice shi ne, muna nan muna rokon Allah, in shi ne mafi alheri ya tabbatar da shi.

ALMIZAN: To a cikin ’yan takara shidan da ake da su a yanzu, wanne ne ganin ka?

HON. BAWA BWARI:- Amma ai baka kira shidan ba. Domin ni bansan ko sun kai shidan ba. Sai ka gaya mani ko waye da waye. Ko ba gaskiya ba? (dariya). Don kada in je in kira wani wanda ba shi a ciki.

AL-MIZAN:- Akwai IBB...

BAWA BWARI:-To shi kenan kar ka je ko'ina. Ai babu kuma. In dai da IBB a wuri, ai shi kenan. (dariya).

AL-MIZAN:- Su Buhari fa da su Buba Marwa?

BAWA BWARI:- Af, to Buhari dai ya yi takara da, ban ce ko zai sake yi nan gaba ba. AL-MIZAN;- To yanzu kana nufin babu wani dan takara kenan sai IBB?

BAWA BWARI:- A wajena fa. Don duk cikin wadanda ka kira banda fosta babu abin da suka yi.

AL-MIZAN:-Ko da wadanne ayyuka za ka dogara in ka zo kamfe a lokacin zabe? BAWA BWARI;- Ai ba na gori. ni ba na gori. Mutanena sun san abin da na yi. Da so samu ne zan so in yi abin da ya fi haka. Don in ka yi ya fi haka, in ka zo kamf ba sai ka yi wata wahala ba. Ba sai ka sa fosta ba. Sai ka yi ta nuna musu abin da ka yi. Don sun tura ka ka je ka yi musu abin da ya dace ne. Sune za su duba su ga in ka cancanta ka ci gaba, ko ka cancanta a ba ka goyon baya, ko kuma asa wani da ake ganin zai yi fiye da abin da ka yi.

AL-MIZAN: Wasu mutane suna zargin wai IBB ne ya turo ka, ko me za ka ce a kan haka?

BAWA BWARI: To in ALLAH ya sa IBB ne ya turo ni, to menene? Komai sai a ce shi ne. Ko da IBB ne ya turo ni, tunda kowa IBB yake so, na ji. To, ai shi kenan. amma ni yana da kyau a ce IBB ya turo ni. Amma ka je ka tambayi jama'ata ka ji IBB ya turo su ko kuwa ra'ayinsu kenan?

AL-MIZAN: Mutane da yawa suna zargin cewa wai Obasanjo ya saye ku domin ya zarce a 2007, ko meye amsarka a kan haka?

BAWA BWARI:- Nawa ya saye mu? Sai kace riga? Ai yadda kuke ganin mu a wurin nan akwai wadansu suna da mutunci, kuma suna son kare wannan mutunci nasu. In ba su kare mutuncinsu ba za su kare mutuncin mutanensu. An tura mu can mu yi wa mutane aiki, amana muka dauka. Kuma ba mun je cin amana bane. Duk wanda zai bari a yi abin da ba zai taimaki mutanensa ba, to ya ci amana. Kuma maci amana ka san makomarsa. Mu nan ba wanda ya isa ya saye mu. Ba Shugaban kasa ba, ko Shugaban menene, ni dai ina tabbatar maka da cewa zancen a saya bai ma taso ba. Abin da muke yi aiki ne wanda kowannenmu dan majalisa, in akwai wani tunani ko wata manufa, to bai rigaya ya zo inda muke ba. Amma mu mun san abin da mutane ke tsoro. Ina tabbatar muku da cewa kar mutane su ji tsoro, su ba mu goyon baya. Su yi ta mana addu'a, insha ALLAHU ba za mu ba su kunya ba.

AL-MIZAN: Meye fatanka ga jihar Neja a nan gaba?

BAWA BWARI: Fatana ga jihar Neja shi ne mu samu jihar Neja da ake zama lafiya. Da ci gaban da kowa zai ji dadin abin da gwamnati ke yi.

AL-MIZAN: Wane sako kake da shi ga al'ummar jihar Neja?

BAWA BWARI: Sakona gare su shi ne su yi hakuri. Muna son wadanda suka yi gwagwarmaya a kirkirar mana jihar Neja, da abin da suka sa a gaba, da kuma abubuwan da har yanzu ba a hango su duka ba. Amma an yi wasu. Cewa da ikon ALLAH duk sauran wadanda suka yi kokari a kirkiro mana jihar Neja, za su ga sakamako da ikon ALLAH.

AL-MIZAN: Honorabul, mun gode.

BAWA BWARI:- Ni ma na gode.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International