Almizan :Ina neman karin bayani kan kabbara uku bayan sallama ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 6 Zulhijjah, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Tambaya da amsa:Tare da Shaikh Ibrahim Zakzaky

Maimaitawa

Ina neman karin bayani kan kabbara uku bayan sallama

SHAIKH ZAKZAKY
Malam Ibraheem Yaqoub Zakzaky H.
Ya na amsa tambayoyinku

Mai karatu wannan amsoshin tambayoyinku ne da Shaikh Ibraheem Zakzaky ya bayar a ranar Talatar da ta gabata a Fudiyya Islamic Centre da ke Zariya. Muna godiya ga Malam saboda ba mu lokacinsa mai albarka da ya yi duk da tarin ayyukan da ke gabansa. Allah ya sa mu amfana. M. M. Awwal ne ya nakalto maku daga kaset.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam ina neman karin bayani game da daga hannu sau uku ana kabbara da nake ganin wasu Musulmi suna yi idan sun sallame salla? Shin yin hakan yana da asali a Musulunci ne?

Daga Mustafa M.J. 0802 552 9597

SHAIKH ZAKZAKY: Eh, yana daga cikin mustahabbobin ta’akibi. Bayan sallama mutum ya yi kabbara sau uku, ya kuma karanta addu’ar wahada, wanda a ciki a akan ce “Wahadahu wahadahu wahada…” din nan, daga nan aka sa masa suna wahada. Manzon Allah ya yi haka nan bayan da ya sallame salla da ya yi na godiya ga Allah bayan bude Makkah. Kuma wannan shi ya maishe shi sunna.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam ni dan kasuwa ne, wata rana ina zaune sai wani ya shigo shagona da giya, na yi, na yi, ya fita, amma ya ki, sai na tunkuda shi, sai giyar tasa ta zube, amma sai ya kai ni kara wajen ’yan sanda sai suka ce sai na biya shi giyarsa. Yana halatta a gare ni in biya shi ko kuwa?

Daga Mujahid Mai Bulawus Unguwar Azara Gwagwada Abuja 0806 571 9146

SHAIKH ZAKZAKY: Ga yadda na fahimta yana nufin kenan hukunci ne aka yi masa. Sai dai idan yana ganin an zalunce shi, ya daukaka kara. Amma yanzu batun yana halatta, wani abu ne yake tambaya ta daban. Da ya ce mani hukuncin da aka yanke masa, ya yi daidai ko bai yi daidai ba? Abin da muka sani shi ne a shari’a in mutum ya zubar da giyar zimmi, zai biya shi. Ko ya kashe masa alade ko abin da ya yi kama da haka nana. Amma yanzu wannan kamar yadda ya fadi, ba ya nuna shi ya zubar da giya bane, shi wannan ya shigo masa shago ne, kuma ba shi da ’yancin ya shigo masa. Saboda haka ya samu ya tunkude shi din kamar yadda ya yi.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam mutum zai iya sayar da kaset-kaset na wakokin kadade na zamanin na Amurka da kuma fima-fiman Hausa, da na Indiya?

Daga Ibrahim Sabo El-Tafaseer Potikum. 0803 207 6472

SHAIKH ZAKZAKY: To idan wadannan ya zama an tattace su aka ga duk abin da ke ciki sun yi daidai da shari’a, ba su saba wa shari’a ba, to zai zama ba damuwa. Amma idan akwai wasu miyagun abubuwan da ake nunawa, to yana sayar da wadannan miyagun abubuwan ne, saboda haka ba zai halatta masa ba.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam ina so in san abin da Allah (T) yake nufi da ayar nan da ke cewa ‘Asshu’ara’u yattabi’uhumul gawun?’

SHAIKH ZAKZAKY: Abin da yake nufi, shi ne, wawaye ne ke bin mawaka. Kuma ya bayyana su wane ne mawaka wadanda suke fadin abin da ba su aikatawa. Sai kuma ya yi istisna’i da cewa sai wadanda suka yi imani suka kyautata ayyukansu. Don ayar ba kawai abin da aka fada kenan ba, tana damfare da abin da ya biyo baya. Ya nuna cewa mawaka wawaye ke bin su. “ Za ka gan su a kowane wadi suna dimuwa kuma suna fadin abin da ba sa aikatawa.” Sai aka ce, “sai wadanda suka yi imani kuma suka kyautata ayyuka,” suka yi ayyuka nagargaru. Ka ga wato a nan ashe galiban mawaka in ba masu imani masu kyautata aiki ba, wauta suke koyarwa, shi ya sa wawaye ke bin su. Amma ka ga nan masu imani wadanda suke amfani da wakokin su don koyar da tarbiyya da addini, ka ga banda su kenan, an yi istisna’i da su. Saboda haka ayar ba a nan ta tsaya ba. Wanda ya dauki wannan ya tsaya a nan kamar ya yanke magana ne, sai ya karasa har karshen ayoyin da suke gaba wadanda suka yi istisna’i da mawakan da suke da imani. Wadanda suke yin wakokinsu ba na bata ba.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam wani mutum ne ya rasu sai kuma ake ta rigima a kan wanda ya wajaba ya rama wa Mahaifinsu Azumi. Babban da ne, ko kuwa babbar ’ya?

Daga Alhaji Muhammad Gada Abuja

SHAIKH ZAKZAKY: Abin sani shi ne Babban da ne ramuwa ta hau kansa. Ba a ce babbar diya mace ba. Saboda haka tunda shi bai da wanda lazim ya hau kansa, ba za mu taba dora wa ubansa ba, illa iyaka yanzu batun waye ya wajaba a kan sa ya riga ya tashi kenan. Saboda an ce ita diya in ta yi, babu laifi amma ba a wajabta mata ba. Amma wanda aka wajabta mawa wanda muka sani shi ne da. Ba mu san an ce ana wajabta ma uba ba. Saboda haka a wannan hali ba wani wanda za a wajabta masa a matsayin wajibi ba. Saboda haka ko wane ya biya ya kyautata.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam a cikin aya ta 11 cikin suratul Nisa’i Allah yana cewa; “Fa’illam yakun lahu waladun wawarisahu abawahu, fali’ummihis sulus. Fa’in kana lahu ikhwatun fa li’ummhi sudus….” Malam wurin da aka ce uwa a ba ta 1/3, uba zai dauki 2/3 kenan saboda “azzakaru mislu hazzil Unsayaini.” A wurin da aka ce idan yana da ’yan uwa 1/6,… Tambaya a nan ita ce za a ba uba kashi 5/6 ne? Ko kuwa ’yan uwan suna da wani kaso ne?

Daga Baffa Cikaji Zariya 0803 694 4299 SHAIKH ZAKZAKY: In na fahimci tambayar tasa, lallai batun “Lizzakri misli hazzul unsayaini,” bai taso ba a nan, saboda shi ana batun gadon ’ya’ya ne. Shi ne namiji yake da kason biyu mata, ba gadon iyaye ne ba, gadon ’ya’ya ne, idan maza da mata ne. Shi ne namiji daya ke da kason mata biyu. Amma gadon iyaye, in wanda ya rasu yana da da, ko wanne daga cikin uwa da uba yana da daya bisa shida ne. Idan su biyu ne kawai suka gaje shi, wato ya zama ba shi da da, iyayensa biyu ne kawai suka gaje shi, to uwar tana da daya bisa uku, ma’ana uban yana da sauran kenan, biyu bisa uku. In kuwa yana da ’yan uwa, to sai uwa ta koma tana da sudusi, mana’a sauran duk na uba ne. Su ’yan uwa ba su da gado ta kowane hali. Matukar mutum yana da iyaye ko yana da ’ya’ya, ’yan uwa ba su gado. Gadon ’yan uwa yana zuwa ne idan mutum ba shi da iyaye ba shi da ’ya’ya.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam mutun ne ya yi noma sai ya kyautar da abin da ya noma ga wani tun a gona. To Malam wanda aka bai wa kyautar zai fitar da zakka ne, ko kuwa zai fitar da Khumusi ne?

Daga Musa A Muhammad Keffi jihar Nassarawa (musaba333@yahoo.com)

SHAIKH ZAKZAKY: To ya danganta da lokacin da aka ba shi ne. Idan aka ba shi kafin ta’allukin zakka, wato kenan kafin lokacin abin da za a girba din ya nuna, to zakka ta riga ya yi ta’alluki a kan manomi din. Saboda haka ko an ba shi ya san ba a fitar da zakka ba dole ya fitar. Kuma in ya fitar, a nan ya fitar wa wanda ya noma ne, ba ya fitar wa kansa bane. Amma idan an ba shi yabanya, to shi ne zakkar ta hau kansa. Idan an ba shi yabanya ya dago bai kai mikidarin ya fid da kai ba har ya ci gaba da nomawa, to tamkar shi ne ya noma, shi ne kuma zakka ta hau kansa. Saboda haka ta kowane hali in ya kai nisabin zakka, zakka za a yi, sai dai illa iyaka zakkar na iya hawa kan mai bayarwa ko ya hau kan wanda aka ba. Amma ba batun Khumisi bane a nan. Amma in ya ba shi bayan ya fid da zakka, to shi ne zai koma batun Khumusi. Daga lokacin da ya zamana an sami amfanin kayan gona din, ana ce mashi lokacin ta’allukin zakka, kafin ma a girbe. Saboda haka in dai ma wannan lokacin ne, to ya hau kan wanda ya noma, ko da ya kyautar sai an ba da zakka, amma shi ne za a fid da mawa.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam mace ce ta yi aure da cikin wani sai bayan wani lokaci ta bayyana, to yaya matsayin aurensu da wannan mijin?

Daga Musa A Muhammad Keffi jihar Nassarawa (musaba333@yahoo.com)

SHAIKH ZAKZAKY: Wannan akwai surori da daman gaske. Akwai batun cewa in tana sane ko shi yana sane. Akwai batun cewa ita ba ta sani ba, shi bai sani ba. Wato in dayansu bai sani ba hukuncin ya bambanta da in dayansu ya sani. Idan ta san tana da ciki din, to ita sunanta mazinaciya. Har ta makkanar da kanta ga wani ya take ta, haka zalika in shi ma ya sani. In su duka biyu sun sani sun zama mazinata kenan. Ka ga ba aure sannan kuma ga hukuncin zina. In ita ta sani, ita hukuncin ya hau kanta, kuma zai zama babu aure a tsakanin su. Amma tana iya yiwuwa ya zama ba wanda ya san da cikin. Ita ma kanta ba ta san tana da cikin ba. To wannan in ta haihu sai a ga in za a iya riskan da cikin ya zuwa wane. In ta haihu kasa da wata shida bayan dukhuli, to in zai yiwu a riskar da dan ga mijin farko, sai a ba shi. Wato in lokacin da ta bar shi zuwa lokacin da haihu bai wuce shekara guda ba kenan, to sai ya zama dan wancan ne. Kuma a nan ba a ce akwai wani abu dangane da aurensu ba.

TAMABAYA: Assalamu alaikum. Malam ya hukuncin layya yake a Imamiyya da yadda ake yin ta?

Daga Shehu Al-Jafariyy Kaduna (shezeez20@yahoo.com)

SHAIKH ZAKZAKY: In dai hukunci ne, sai mu ce wajibi ne ga wanda yake da hali. Amma yadda ake yin sa da bayanin wannan, lallai abin da ya fi alheri shi ne ya karanta babin layya a wata risala amaliyya na Mujtahidi don ya ji cikakken bayani.

TAMABAYA: Assalamu alaikum. Malam ko ya halatta ga mutum ya yi wa budurwa asiri don ta so shi, don ya zama ba wanda za ta aura sai shi?

Daga Ibahim Mai Riga Badawa Kano da Daga Musa Gambo Alkzim Zariya jihar Kaduna 0802 436 6429

A biyo mu mako na gaba don jin amsar wannan tambaya da ma wasu da dama.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International