Almizan :Yiwuwar bude tashar satalayit na rediyo da talabijin ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 6 Zulhijjah, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Tunatarwa:Tare da Shaikh Ibrahim Zakzaky

Yiwuwar bude tashar satalayit na rediyo da talabijin

In ji Malam Zakzaky

SHAIKH ZAKZAKY
Malam Ibraheem Yaqoub Zakzaky H.

Mai karatu wannan ci gaba ne na jawabin da Malam Ibraheem Zakzaky ya gabatar a lokacin da yake rufe wani taron tunatar da juna na kwana biyu wanda ’yan uwa na ‘Resource Forum’ suka gabatar a kwanakin baya a Fudiyya Islamic Centre, Zariya. Kuma in dai ana biye da mu, mun tsaya ne a inda Malam yake bayanin muhimmacin bude tasha a Satalayit. A biyo mu a ji sauran abin da Malam yake cewa game da wannan batu, kamar yadda Musa Muhammad Awwal ya rubuto mana da ga kaset. A sha karatu lafiya.

Wato yana da sauki ka yi ‘Channel’ din satalayit. Abin da kake bukata kawai ya zama kana da na’urorin (Gadgets) da zai watsa (transmitting) zuwa satalayit din su samu (receiving), shi kenan. Ko da kai tsaye (live) ne. Za ka ga kamar misali, ALFURAT ga dukkan alamu na su Abdul’aziz Hakeem ne. Ko shekaran jiya suna sallar idi ana nunawa kai tsaye, khudubarsa ta idi. Banda wannan akwai wani ANWAR ma wanda wani dan uwa sun hada da wani wanda ya ce shi ne Daraktan ANWAR din. Sai ya ce masa daga ina kuke yi? Sai ya ce su sun ga cewa Egypt da suke da ‘Nilesat’ in a Egypt kake watsawa (Transmitting) din abin, to ya fi arha. Saboda haka sai suke kai dakin shirye-shirye (studio) din Egypt a Alkahira. Amma suna Syria ne. To ta yiwu akwai hanyar da suke bi.

Kodayake su duk ‘programmes’ din su da ma galibansu kasusuwa ne, ba ‘Live’ bane. Sukan ta sa ma kasusuwan wasu malamai da suka yi magana tun da, sai a sa. Ba sa sa komai, daga irin su Du’a’u Kumail da irin addu’o’in nan da karatul Alkur’ani da sauransu. Sai kuma a sa wani jawabi da wani Malami ya yi, wani Malamin ma ya dade da rasuwa, amma ana sa jawabansa.

Kuma ko da wane lokaci in ka duba za ka gan su, in ba su watsa (transmitting) wani abu za su sa karatu Alkur’ani ko addu’a. Sai ya zama wato a nan Misra kenan suka dan bude dan dakin shirye-shirye (studio) yana harbawa, sai a kai masa kasusuwa. Saboda ba sa yin wani abu na kai tsaye (live), sam ba ka ganin sun awani abu na kai tsaye (Live) kullum kasusuwa ne.

To sai nake ganin ko da wannan ya kamata kar mu tsaya muna ganin kila ba zai yiwu bane, a fara nazarin yiwuwarsa (feasibility study) a gani. Ko da idan misali ba za mu iya sayen mashin din da zai rinka watsawa (transmitting) kai tsaye ba, yanzu mu sami wasu ’yan uwa da suke wata kasa, kamar wadanda suke zaune a London, masalan. Su bude dan situdiyo (bai wuce shago ba), wanda kuma a can zai fi arha, a rinka aikawa da kasusuwa din. Kuma a tambaya a ji nawa ne kudin mashin din da zai iya harba ma satalayit,’ din da zai yi watsa masu (Transimitting), tunda yake mota tana iya tafiya da shi. Yanzu yadda muke maganar nan inda za a sa kyamara irin wannan a hada da waya ya je cikin mota din, shi kenan yanzun nan sai mutane su rinka kamawa kai tsaye a ko’ina.

Ya kamata a sami wasu, a sa su aikin su nemo mana ‘feasibility studies’ su ga yadda zai yiwu. Don ta yiwu abin ma za mu iya yi, amma mun dauka kila dai da tsada ne ba za mu iya yi ba, muna kallon na wasu, tunda muna kallon na wasu, ga su nan wasu za ka ga ’yan wajila-wajila ma dai, duk suna da irin wadannan abubuwa din. Wanda yake mune ‘aula’ ya zama cewa lallai akwai abubuwan da ya kamata a sami irin wannan hanya din. Tunda ga satalayitoci nan birjik. A lokaci guda za ka iya sa daya a satalayit daban-daban. Alal misali in ka sa a ‘Nilesat’ za ma ka iya sa wa a ‘Arabsat,’ za ma ka iya sawa a wasu. Ga ma wasu nan wadanda ake watsa (broadcasting) su zuwa Afrika ta yamma yanzu, kamar wannan NSS, wanda ke duban Afrika ta yamma ne yanzu, yana da karfi. Ko dan karamin Dish ma zai iya kama shi, wanda DITV suke a kai, misali. To da ire-iren wadannan.

Har walayau a lokaci guda nake cewa in an yi daura (Hosting) tasha (Channel) na talabijin, shi kuma yana da sauki a lokaci guda ka yi duk da na rediyo, satalayit rediyo din kenan, wanda shi kuma a lokaci guda da sauti da kuma murya.

Dalili shi ne irin kwamacalar da muke ga ana ta ta yi, musamman a wadannan ’yan shekarun game da yadda ake ta tallar addini, barkataitayi a gidajen talabijin na kasar nan na sayarwa da na Hukuma. Da gidajen rediyo masu zaman kansu da na hukuma. Sai nake ganin ba ni da sha’awar a ce mu ma mun shiga irin wannan layi din.

Kamar misali a ce yanzu za ku saurari Malam wane, sai ya dauki addini ya yi Kudu da shi. Sai a ce, to yanzu Malam wane ya gama, to yanzu sai kuma Malam wane. Shi kuma sai ya dauki addinin ya yi Yamma. Sai a ce yanzu sai Malam wane. Shi kuma sai ka ga ya yi Arewa. Wani kuma sai a ba shi, shi kuma sai a ce yanzu ga Malam wane, shi kuma sai ya shiga tsallen kwadi da addini. Wani kuma sai ya shiga jujjuyawa, birgima. Ga su nan dai, da mai birgimar hankaka da addini, duk dai ka ji batsaltsale kala-kala.

To sai nake ganin anya ya kamata a cikin wadannan kwamacalar za mu sa namu? Ya kamata ya zama tunda yake akwai yiwuwar a ce ga namu ne, ka ga in kana so ka ji kwamacala, akwai wuraren kwamacaloli na nan, in kuma kana so ka ji namu ka sami namu.

Na san akwai wani lokacin da wani ya nemi cewa ya kamata a ce mu ma mu rinka ba da gudummawa (Contributing) a wannan ‘list’ din nan na ’yan Nijeriya Muslim ….. Sai na ce haba wannan kwamacalar bai dace da mu ba. Su dai su yi ta kayansu. Mu im ma wannan in muna da bukata sai mu yi irin namu ‘list’. Sai ya zama mune muke zuba namu. Amma dai su wadannan a cikin wannan wurin bai dace da mu ba. Ya kamataa ce in kana bukatar ka fahimcemu, to mu ma akwai namu hanyoyin da za ka je ka ji; in ba ka bukata shi kenan ka huta. Amma ba zai yiwu ka watso kwamacalarka a ciki ba. In kuma ka watso, in mu muka ga daman ya kamata mu sa, muna iya sawa, amma dai ya zama namu ne, amma mu ba bukatar mu shiga nasu.

Kamar yadda nake ganin duk da dai ga yadda nizamin tattalin arziki yake jaridar ALMIZAN ta riga ta zauna daram, saboda su mutane suna saye, masu karanta Hausa suna saye. Kuma ta riga ta sami karbuwa tsakanin mutane, ma’abota harka da ma mutanen al’umma din. Har ma da wadansu mutanen da mukan sha mamaki. Don akwai wani da ya je ya halarci ko ‘Embassy’ din Birtaniya ne, sai ya an sayo guda 25 ana ajiyewa a tebur, har da ma wanda aka dauka aiki mai fassara. Akwai ‘Embassies’ da suke da mai fassarar ALMIZAN, wanda zai fassara masu sannan a duba.

To ka ga dai ta sami karbuwa, akalla suna son su fahimce mu, duk da ma ba wai harshen da suke iya fahimta muke magana ba, amma su suna neman wanda zai sanar da su abin da muka ce din.

Karbuwar ALMIZAN inda muka yi sa’an haka nan kawai, ana saye ne, sai ya zama da kudin sayar da jaridar (cover price) ma za a iya yi, za a iya ci gaba da jaridar. An yi ta kokarin (attempting) na Ingilishi ya ki yiwuwa, saboda in an yi na Ingilishi din ba a saye. Sai ya zama su ’yan uwa galiba sai ya zama cewa na Ingilishi din ya zo masu a makare. Duk wani bayani da za su so su ji da dumiduminsa, Almizan ta riga ta gaya masu. Tunda dai an yi kokari an yi wata-wata ko? Sai su ga cewa ai duk sun san abin da aka rubuta. Saboda haka wadanda kawai za su bukaci su sayi wannan sune wadanda ba su karanta ta Hausa. To su kuma sun karanta da za su saya da yawan da za a iya ci gaba da yi. Da a ce muna da hali ko da ba za a iya sayarwa ba, sai mu ci gaba da yi har ta samu ta zauna, amma dai mun kasa yin wannan. To shi ma wannan wani kule (Challenge) ne da ke gaban Resource Forum. Da ma an tattauna wannan jarida tuntuni? Ko an dan yi hobbasa? Ka san wani lokaci in aka yi magana kawai aka tashi aka bar shi, shi kenan.

Kamar yanzu nake cewa kamata ya yi kar a tashi a bar wannan, kamar yanzu a sa ma wasu alhakin kawo bayanan ya za a dora (hosting) tasha (channel), su binciko nawa zai ci (How much it cost),’ duk kowane sashe. In ma kamar Ofishin da na fadi, wanda yake shi ba ma sai ka yi situdiyo a nan, ka yi wannan, ka yi wannan ba, kawai kasusuwa za a kai. A sami wani ya yi situdiyo din a waje, a fara da wannan.

Kuma idan muna bukatar wanda za a yi kamar wanda za mu yi kai tsaye (live), mashin din nawa ne? Wani zai iya zuwa ya sayo shi ko za a yiwo odansa? Ba ina batun mu yi rajista a matsayin gidan talabijin ba, wannan nan gaba a yi, akalla (atleast) yanzu ma dai akwai batun cewa suna da ka’idodin cewa sun hana yin rediyo da talabiji na addini, ko? To amma shi wannan watsa shirye-shirye (transmitting) na satalayit bai shafi wannan ba. Wani abu ne wanda yake ba shi a cikin karkashin abin da suke da iko (control) da shi. Kodayake shi ma wannan din nan gaba za a iya yi. Na san ALMANNAR daga nan ne ya fara. Don na taba zuwa Lebanon na ga suna yi. Na ga kuma suna da gidajen rediyo da yawan gaske. Har na yi hira da wani redio ANNUR. Sai na ga suna da ’yan na’urori (gadgets) din magana din ’yan kanana ne. Har ya ce yanzu ana ji ne kai tsaye ai. Kuma dan karamin mashin ne kuma magana ana ji kai tsaye. Wanda sai na ga suna da gidajen rediyon ne da yawan gaske haka nan, wanda yake kai tsaye ana kakkamawa.

Sai nake ganin wadansu abubuwan ba wai suna da tsada ne ba, kila ba ka kula da ka je ka bincika ya yake ne ba. Saboda haka yanzu idan aka ba wasu aikin (assignment), shi kenan nan gaba sai mu ji. Na san akwai wani lokacin da wani aka yi hira da shi a wani gidan rediyo yana fadin cewa ko da suka je Hajji sai suka yi magana, su sun yi kokarin su yi wa harka din mummunan fenti. In sun fadi wani abu suka ce haka da kaza. Sai su ga mutanen can duk sun sani. Duk wanda suka yi magana da shi sai su ga ya sani. Ya ce ai duk mun karanta a ALMIZAN. Kuma su suna gani ne a Intanet.

To shi ne sai yake tunanin cewa ya kamata su ma a sami su shiga intanet. Shi ya dauka shiga intanet din kila sai ma gwamnati ta sa masu hannu. Saboda bai san yadda ake shigan bane. Shi ya dauka kila sai da Hukuma mai zai shiga.

Shi ne nake ganin kada ya zama muna kallon tashoshi a matsayin su ma haka nan ne. Na san Satalayit bai wadata sosai-sosai a nan ba, har yanzu mutane suna kallon sa ne haka. Amma dai yanzu ya fara zama gidan kowa da shi ko? Ana ta ta yi. Kuma ko da ma bai damu mutum ba, kamar yadda intanet din nan, shi ma da yawan mutane ba su san intanet ba a nan. Amma a waje suna dogaro da shi saboda yana da sauki a waje.

Ta intanet din, in ka ga irin yadda, musamman wannan shafin (site) din, islamicmovement.Org din nan, ba karamin yada abubuwa suka yi ba, don da yawan mutane ta nan suka san harka din.

Na hadu da wasu suna cewa, wasu hotuhan Ashura na bara din nan da suka gani, su abin ya ba su mamaki. To irin wannan. Sai ya zama su intanet sassaukan abu ne, kowa da kowa yana da shi. Saboda haka sai ya zama wannan ya fi yada harkar a wajen duniya fiye da nan.

To ka ga in ma ana ganin kila ma kamar na satalayit muhimmancinsa kila zai zama kadan a nan, to a waje ya fi. Saboda su a waje yana da karfi, nan da nan za a iya gani.

Za mu ci gaba insha Allah.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International