Juma'a 15 ga Sha'aban 1435 | Bugu na 1133 | ISSN 1595-4474 |
---|
Babban Labari
Al'amarin Imam Khumaini na Allah ne
In ji Shaikh Ibraheem Zakzaky
Daga Aliyu Saleh
Shaikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky ya tabbatar duk wani mai hankali, idan har ya kalli lamarin Imam Khumani, zai fahimci cewa na Allah ne, kuma shi ya taimake shi, ya ba shi nasara a duk tsawon da’awarsa da kuma kafin da bayan cin nasarar juyin-juya-halin Musulunci a kasar Iran...
Shaikh Zakzaky, wanda ke jawabi a wajen rufe taron Makon Imam Khumaini da ’yan uwa na Academic Forum suka shirya ranar Lahadin nan da ta gabata a Husainiyya Bakiyyatullah, Zariya, ya bayyana yadda kiran na Imam ya yi tasiri ga kowane bangare na duniya.
Ya ce, in mutum ya ga al’amarin Imam Khumaini ya duba, sai ya ce wayo ne, ko dabara ce, ko ilimi ne, ko iyawa ne, sai mu ce ya binciki hankalinsa. Wannan al’amari na Allah ne, ba wani bayani banda wannan. Duk da yake mun san yana da ilimi da hazikanci, amma wane wayo ya yi wa mutuwa har ya shekara 90 bai mutu ba, har sai da ya kammala aikinsa?
Tun farko Malam ya fara ne da nuna alhini dangane da rashin da duniya ta yi na Imam Khumaini, inda ya ce a lokacin da ya rasu duniya ta girgiza, duk da cewa kafafen yada labarai na duniya irin su BBC da suka saba rage yawan jama’ar da suka halarci duk wani taro da ba sa so, amma a kan na Imam sun tabbatar da cewa fiye da mutane miliyan shida ne suka halarci jana'izarsa. Duk da kuwa bayanai sun tabbatar da cewa fiye da mutane miyan 10 ne suka halarta.
Ya ce, mu kaddara ma miliyan shida din ne suka halarta, akwai wani da ya mutu wanda ya samu rakiyar mutane miliyan shida? Ya ci gaba da bayyana yadda jama’a suka kadu da rashinsa, duk da kuwa ya shekara fiye da 90 a duniya.
Shaikh Zakzaky ya kawo yadda Allah ya tsawaita rayuwar Imam Khumaini har shekara 10 da ya yi bayan nasarar juyin-juya-halin da aka yi, yana ganin yadda abubuwa suke tafiya, kamar yadda Manzon Allah (S) shi ma sai da ya shekara 10 bayan nasarar da Musulunci ya yi kafin ya koma ga rahamar Ubanginsa.
Ya kawo wani bayanin da Imam Khumaini din ya yi, inda ya bayyana cewa shi dai ya yi aikinsa. Ya bayyana haka a cikin wata wasiyyarsa da ake ce wa ‘khalidah’, wacce take a rufe, ba a bude ta ba, sai bayan rasuwarsa.
Ya ce, Imam Khumaini ya bayyana ne a wani lokaci da aka cire fata, amma sai Allah ya bayyanar da shi, ya zo ya kawo gyara a cikin al'umma. Ya yi dogon bayanin dangane da yadda mutane suka yanke kauna da samun fata kafin bayyanar Imam Khumaini a wannan zamanin.
Ya kawo yadda wasu da ke ganin za a samu gyara a duniyar Shi’a da kuma yadda ake ganin sa a duniyar Sunna. Ya yi tsokaci mai tsawo a kan yadda wasu ke ganin babu yadda za a yi mutanen kirki su shiga cikin harkokin siyasar tafiyar da rayuwar mutane. Suna ganin mutanen kirki ba za su shige ta ba. Har ya kawo yadda aka kirkiro wani addini a kasar Iran da ake kira BAHA’IYYA, amma sai kiran Imam Khumaini ya fita daban.
Shaikh Zakzaky ya tunatar da mahalarta taron abin da ya faru a lokacin da Imam Khumaini yake makaranta, sai ya fara bayanin irin zaluncin da ake yi a duniyar nan. Wannan wani abu ne da ba a saba jin sa ba a makarantu. Har wasu suna ganin ya kamata ya kame bakinsa. Wasu suna ganin abin da yake yi ya saba wa addini. Suna ganin siyasa daban, addini daban. Suna cewa ina ruwan Malami da harkokin siyasa? Ya ce mutane sun dauka siyasa mutum yana hawa dirom ne ya rika kunduma zagi. Mutane sun dauka siyasa ba abar kirki ba ce.
Sannan sai Malam ya yi bayanin irin siyasar da take da amfani, irin siyasar Imam Ali (AS). Ya kawo labarin yadda wani babban jami’in gwamnatin Iran ya je ya sami Imam Khumaini (KS) da dukkan girmamawa yana fada masa cewa irin wannan siyasar ba ta dace da shi ba. Siyasa ce ta lalatattu. Ya ce ka ga yanzu ni ina shan giya, kuma ina zina, mu ya kamata mu rika yin irin wannan siyasar.
Amma sai Imam Khumaini ya bayyana masa cewa shi irin siyasar Imam Ali (AS) yake yi. Ya kuma ce in dai siyasa tana nufin a ba ka amana ta jinanan mutane, dukiyarsu da mutuncinsu ne, to masu addini ne ya kamata su yi.
Malam ya yi tambayar cewa; wa ya dace ya rike amana? Mutumin kiriki ko lalatacce? Idan ka bai wa mutumin kirki amana, me zai yi? Idan dai wannan ne ake bai wa mutanen kirki, to Malamai ya kamata su yi. Amma yanzu ka ga yadda aka dauki al’amarin tafiyar da mulki, al’amari ne na lalatattu.
Shaikh Ibraheem Zakzaky ya kawo yadda Imamu Khumaini yake kiran mutane, yana fahimtar da su yadda Sarki Shah ya sallama wa kasashen waje siyasarsu da mutuncinsu.
Ya ce, sai ya zama mutane suna ganin wannan abin da yake yi kamar fandara ce, kamar ya kauce wa tafarki. Har wata rana dansa ya shiga wani waje ya sha ruwa, sai wani ya dauki kofin zai sha ruwan, sai aka hana shi, aka ce dan wannan fandararren ya sha ruwa da shi, sai an yi masa ta’afiri kafin a yi amfani da kofin.
Shaikh Zakzaky ya ci gaba da cewa; amma da yake magana tana da tasiri, sai ya zama maganar da Imam Khumaini yake yi tana tasiri a zukatan jama’a, musamman dalibai, har suka fara gane inda maganarsa ta fuskanta. Ya kawo yadda ake cin zarafin mutane Iran, yadda Ba’amerike yake yawo da mota yana banke mutane, amma ba abin da za a yi masa.
Ya ce sun shirya sosai don ganin sun lalalata jama’ar kasar Iran, har ya zama giyar da ake yi a Amurka ta fi araha a Iran saboda a lalata jama’ar kasar. Ya kawo yadda wani mawaki ya kawo ziyara kasar Iran, amma kuma sai ’yan mata sun kwanta tsira a filin jirgin sama ya bi ta kansu ya wuce.
Ya ce a birnin Tehran kadai akwai karuwai dubu 50, suna hulda da shugabannin kasashen duniya, ana kwasar su ana kai masu. Shan kawaya da sauran fasadi kala-kala sun zama ruwan dare a kasar duk da nufin a lalata rayuwa da tarbiyyarsu. Ga kuma talauci da jama’ar kasar suke fuskanta, ba ruwan famfo, ba wutar lantarki sai a birane.
Shaikh Ibraheem Zakzaky ya kawo yadda ya ga wani hoto da idonsa a lokacin zuwansa na farko Iran a shekarar farko ta nasarar juyin Musulunci, inda aka nuna masa yadda mutane suke shan ruwan kwatami. Ba kawai ana tatsar arzikinsu da kuma mutuncinsu ba ne, banda wannan kuma ga shi ana ta karatu, amma ba ruwansu da magana a kan irin zaluncin da ake yi, sai dai su ce Allah ya gaggauta bayyanar Imam Mahdi ya yi maganin wannan zaluncin. A cikin wannan yanayin ne Imam ya bayyana.
Ya kawo yadda Sarki Shah ya nemi ya bai wa Imam Khumaini cin hanci don ya daina abin da yake yi. Ya kuma kawo yadda a karshe dai ya kore shi zuwa Iraki, daga nan kuma zuwa Turkiyya, har kuma ya koma zuwa Faransa. Ya kawo irin ka’idoji da dokokin da aka yi ta sanya masa a wadannan kasashen. Ya kawo kuma yadda ake yada jawabansa, da irin matakan da jami’an tsaro suka dauka don dakile yaduwar jawaban Imam a kasar Iran. Ya ce idan an gan ka ga kaset din jawabi Imam a cikin Iran, ka mutu. Don haka dalibansa suka dauki duk matakai don ganin hakarsu ta cimma ruwa. Kuma hakan suka yi, har zuwa lokacin da jama’a suka fahimci kiran.
Ya ce, duk da irin ta’addancin da jami’in tsaron ciki na Iran da ake kira SAVAK suka yi domin hana juyin-juya-halin da Imam Khumaini yake jagoranta, amma dai hakan bai hana cin nasara ba. Bai kuma hana gwamnatin Sarki Shah faduwa ba, duk da kokarin kare ta da gwamnatin Amurka ta yi don ganin hakan ba ta samu ba. Amma daga bisani sun lura lallai ba zai yi yiwu su hana Imam kafa gwamnati ba. Sai dai suka yanke shawarar cewa su yi juyin-mulki kawai idan har Shah ya fice daga kasar.
A wani bangare na jawabinsa nasa, ya kawo yadda sojoji suka rika bude wa masu zanga-zanga wuta ba sassauci, su kuma jama’a suna ci gaba da fitowa. Shi kuma Imam yana cewa ba sassauci. Yayin da wasu daga cikin dalibansa suka same shi suna shaida masa cewa kisan ya yi tsanani, Sarki Shah yana neman ya karar da mutane Iran don haka a sassauta, amma kawai sai ya ce masu a kawo masa ‘list’ din mutanen da za su tafiyar da gwamnati. Sai ya ce masu wannan abu na Allah ne, kuma zai tabbatar da shi.
Ya kawo yadda mutane suke fitowa suna Muzahara ba su dauke makamai, a maimakon haka ma sai suke bai wa sojojin filawa. Su kuma jama’ar Iran suna girmama filawa sosai. Sai ka ga soja yana harbin mutane, amma yana kuka. Daga bisani sai sojojin suka fara komawa bangaren daliban Imam.
A cikin jawabinsa, Shaikh Zakzaky ya kawo yadda Sarki Shah ya gudu ya nada Faraministan rikon kwarya, Baktiyar, shi kuma ya rubuta wa Imam Khumaini wasika da dukkan girmamawa. Har yake ce masa, a shirye yake ya yi duk abin da Imam yake so. Sai Imam ya ce masa ya yi murabus kafin ya zo.
Ana cikin wannan yanayin Imam Khumaini ya taho kasar. Duk hankalin masu tafiyar da mulki ya tashi. Sai suka ce a hana shi sauka a Airport. Sai jama’a suka ce yanzu kam ba sauran rarrashi, jama’a za su fito su dauki mataki.
Shaikh Zakzaky ya kawo yadda jama’a suka bijire wa duk wata doka da Sarki Shah ya kafa. Sai ya zama an sanya dukar hana fita (curfew), amma sai mutane suke kwana a kan titi. Masu shara, maimakon su share titi, sai su debo shara su zuba a kan titi. Amma aka ji Imam zai zo, sai aka gyara ko’ina, aka rika wanke titin da sabulu. Miliyoyin jama’a suka fito, suna son ko da su hango rawani, ko rigarsa.
Shaikh Ibraheem Zakzaky ya yi tsokaci mai tsawo dangane da yadda Iran ta yi fice a duniyar dauri da kuma ta yanzu ta fuskar bunkasar ilimi. Ya kawo cewa hatta Amurka ta yi i’itarafi da cewa a fannoni daban-daban na ilimi Iran ta fi su. Ya ce mafi yawan Malaman da ke koyar da ilimi kimiyya da fasaha yanzu a Amurka Iraniyawa ne. Ya ce hatta a lokacin baya, mutane irin su Bukhri da ya tattara Hadisan Ahlus Sunna Ba’iraniye ne, duk kuma wannan ya samu ne albarkacin juyin-juya halin da aka yi a kasar.
Ya bayanin irin yadda da’awar Imam Khumaini ta yi tasiri a kan kowa hatta ga wadanda ba Musulmi ba. Ya bayyana yadda aka yi suka fara jin labarin kiran da yake yi tun farkon wannan da’awar. Ya ce, duk da yake Imam Khumaini ya yi watafi shekaru 25, amma tamkar yana nan da rai, domin fikirarsa tana nan da rai, don haka makiya ke ta kokarin su takaita juyin a Iran kar ya bazu zuwa wasu kasashe. Ya ce nan kasar da’awar Imamu Khumaini ce.
A jawabin na tsawon awa daya da minti 40, Shaikh ya tabo dukkan janibobi na rayuwa, gwagwarmaya, iliminsa da kuma irin matakan da Imam Khumaini ya bi ya cimma nasara a da’awarsa, har da kuma da irin fadi-tashin da makiya suka yi don ganin haka ba ta cimma ruwa ba, amma da yake al’amarin nasa na Allah ne, sai ga shi Allah ya ba shi nasara, kuma ya ga kafuwar gwamnatin na shekara 10 kafin Allah ya amshi rayuwarsa yana da shekaru 94 a duniya.
Kafin Malam Shaikh Zakzaky ya jawabinsa, sai da Malama Zeenatuddeen Ibraheem ta fara gabatar da jawabi, inda ta janyo hankalin mahalarta a kan irin muhimmiyar rawar da dalibai suka taka a lokacin gwagwarmayar Imam Khumaini da kumai irin rawar da dalibai suka taka a farkon tsirowar Harkar nan, don haka sai ta bukaci a ci gaba daga inda aka tsaya.
Shi dai a wannan taron da aka fara gabatar da shi tun daga ranar Juma’ar makon shekarajiya, daliban sun gabatar da abubuwa daban-daban da nufin kara wayar da kan al’umma game da wane ne Imam Khumaini (KS).
Kamar yadda Shugaban da ke kula da bangaren, Malam Shu’aibu Ahmad ya bayyana tun farko, daga cikin abubuwan da suka gabatar akwai ziyarori, jawabai daga Malamai da Masana, tattaunawa, da dai sauran su.
Sanarwa
Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)
Labarai cikin hotuna
Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana