Juma'a 15 ga Sha'aban 1435 | Bugu na 1133 | ISSN 1595-4474 |
---|
Tambihi
Munasabobin watan Sha’aban
Watan Sha’aban shi ne wata na takwas a jerin lissafi na watannin Musulunci 12. Haka nan kuma yana da munasabobi daban-daban. Watan Sha’aban yana da khususiyya na cewa dukkan munasabobin da ke ciki na wiladar (Haihuwar) Ma’asumin ne, ba na wafatinsu ba. Wato babu wani daga cikin Imaman Ahlul-baiti, wanda ruwaya ta zo da rasuwarsa cikin watan. Ruwayoyin da suka zo sune na wiladar Imam Husain (AS), Imam Sajjad (AS) da Imam Mahdi (AF). Wato dai wannan wata na Sha’aban akasin watan Muharram ne, wanda shi ma yake da khususiyyar cewa babu wani daga cikin Ma’asumin da wiladarsa ta zo a cikin watan. Ruwayoyin da suka zo sune na shahadar Imam Husain (AS) da kuma Imam Sajjad (AS)...
Watan Sha’aban wata ne na Manzon Allah (S), kamar yadda ya zo a ruwayoyi na hadisai, saboda haka wata ne da ke da falaloli masu yawa. Ga wasu daga cikin falalolin wannan wata. An samo daga Imam Ali (AS) cewa, Manzon Allah (S) ya ce:Sha’aban watana ne, duk wanda ya azumci watana, zan kasance mai ceton sa ranar kiyama.” Haka nan a wani hadisi Manzon Allah (S) ya ce, “Sha’aban watana ne, duk wanda ya azumci rana guda daga cikin watana, to Aljanna ta tabbata gare shi.”
An samo daga Imam Sadik (AS) ya ce, Manzon Allah (S) ya kasance idan watan Sha’aban ya kama, yakan sa a yi sanarwa cikin Madina da cewa: “Sha’aban watana ne, Allah ya yi rahama ga wanda ya taimake ni cikinsa.” Taimakon sa a nan shi ne ta hanyar yin ibadodi daban-daban a cikin watan. Ya zo a hadisi cewa tun da Imam Ali (AS) ya ji wannan sanarwa, bai taba fashin azumin watan Sha’aban ba. Ya ce, kuma in har yana duniya, to duk watan Sha’aban idan ya zagayo, sai ya azumce shi dukkan sa. Kuma an tambayi Manzon Allah (S) wane azumi ne ya fi falala? Sai Manzon Allah ya ce, azumin Sha’aban.
Haka nan a wani hadisi Manzon Allah (S) ya ce, “Watan Sha’aban wata ne mai daraja, kuma watana ne, Mala’iku na girmama shi, kuma sun san hakkinsa. Kuma wata ne da ake kara arzikin bayi a cikinsa, saboda watan Ramadan; ake kuma kawata Aljanna.” Da dai hadisai masu yawa dangane da falalolin wannan watan. Kuma idan mutum ya duba cikin wasu daga cikin littafan hadisai na Ahlus-sunna zai ga cewa sun tabbatar da cewa Manzon Allah ya kasance yana azumtar watan Sha’aban baki dayansa.
Sai kuma abin da ya shafi munasabobi na wannan watan. A ranar Alhamis 3 ga watan Sha’aban, shekara ta hudu bayan hijira aka haifi Imam Husain (AS). Bayan da aka haifi Imam Husain (AS) aka je aka shaida ma Manzon Allah (S), ya zo wannan gida mai albarka, yana murna da farin ciki. Ya ce ma Asma’u ’yar Umais ta miko masa shi. Manzan Allah ya karbe shi ya rungume shi ya yi masa kiran sallah a kunnensa na dama, sa’annan ya yi masa ikama a kunnensa na hagu, sai ya aza shi a cinyarsa mai albarka, ya yi kuka. Sai ita Asma’u ’yar Umais ta ce: “Babana da Mamana su kasance fansa gare ka ya Manzon Allah! Wannan kukan fa?” Sai Manzon Allah ya ce mata: Ina kuka ne saboda abin da zai same shi a bayana. Wadansu jama’a azzalumai za su kashe shi a bayana. Ba za su samu cetona ba.”
Bayan haka sai Manzon Allah (S) ya ce ma Imam Ali (AS) ka sa masa suna. Sai ya ce, ban kasance zan riga ka ba wajen sa masa suna. Sai Manzon Allah (S) ya ce ka sa masa suna Husain.
Haka nan a rana ta bakwai da haihuwa, Manzon Allah (S) da ya je wannan gida mai albarka, ya dauki Imam Husain, sai aka ga ya yi kuka shigen yadda ya yi a rana ta farko. Da aka tambaye shi kan kukan, sai ya ba da amsa kamar yadda ya bayar a rana ta farko.
Daga cikin abin da Imam Husain ya kebanta da shi, shi ne bai taba shan mama (nono) na wata mace ba ko kuma na Sayyida Fatima (AS), kamar yadda Kulaini ya ruwaito a cikin littafin Kafi, juz’i na 1 shafi na 386, wato babin da yake magana kan wiladar Imam Husain (AS). An samo daga Imam Sadik (AS) ya ce: “Imam Husain bai sha mama na wata mata ko kuma na Fatima ba. Ya kasance akan kawo shi wajen Manzon Allah (S) ya sa babban yatsansa a cikin bakinsa, sai ya tsotsa daga gare shi. Hakan yakan ishe shi kwana biyu, kwana uku.”
Nan kuma wasu sassa ne na rayuwar Imam Husain (AS). 1- Haihuwarsa: An haife shi a Madina 3 ga watan Sha’aban. 2- Shekarunsa: Imam Husain (AS) ya rayu a duniya shekaru 57 ne. 3- Muddan Imamancinsa: Shekaru goma ne. 3- ’Ya’yansa: Imam Husain (AS) ya kasance yana da ’ya’ya bakwai – maza 4 da mata 3. Mazan sune: Imam Zainul-Abidin, Aliyyul Akbar, Ja’afar da kuma Abdullah. Aliyyul Akbar da Abdullah sun yi shahada a Karbala. Ya Aba Abdullah da ake yi masa kinaya da shi, ana nufin wannan Abdullah. Matan sune: Sukaina, Fatima da kuma Rukayya. 4- Shahadarsa: Ya yi shahada a ranar Juma’a, a wata ruwaya ranar Asabar 10 ga watan Muharram shekara ta 61 bayan hijira. Kuma ya zo a ruwayoyi na hadisai cewa a ranar da ya yi shahada ne Imam Mahdi (AF) zai bayyana, wato a ranar Asabar ko Juma’a 10 ga muharram a shekarar da Allah Ta’ala shi ne masani a kai. 5- Kabarinsa: Yana a Karbala ne tare da wadanda suka yi shahada tare da shi.
Nan kuma wasu sassa ne na rayuwar Sayyid Abul-Fadhal Abbas. 1-Haihuwarsa: An haifi Abul-Fadhal Abbas a Madina, ranar 4 ga watan Sha’aban, shekara ta 26 bayan hijira. A cikin ’ya’yan Imam Ali (AS) maza, to baya ga Imam Hasan da Imam Husain, to ba wanda ya kai shi daraja. Kuma Abul Fadhal Abbas tanadi ne na musamman da Imam Ali (AS) ya yi ma Imam Husain (AS) domin waki’ar Karbala. 2- Nasabarsa: Sunan mahaifiyarsa Fadima ’Yar Hizam.
Idan mutum ya bibiyi tarihinta, zai ga cewa baiwar Allah ce mai gayar biyayya da kuma girmamawa ga Ahlul baiti. Alal misali lokacin da ta zo gidan Imam Ali, wato bayan aurensu ta ce tana son idan Imam Ali zai kira ta, kada ya kirata da sunanta, wato Fatima, saboda girmamawa ga Sayyida Fadima, kuma kada haka ya dinga sosa ran su Imam Hasan, Imam Husain, da Zainab, wato saboda tunawa da Mahaifiyarsu. To, a lokacin shi ne Imam Ali yake ce mata Ummu banin, domin daga baya ta haifi ’ya’ya maza guda hudu. Wannan kuma in muka duba za mu ga cewa wata karama ce daga cikin karamomin Imam Ali (AS). Haka nan kuma wadannan ’ya’ya nata ta yi masu kashedi da cewa, kada wani daga cikin su ta ji ya kira sunan Imam Hasan da Husain, sai dai su ce “Shugabana.” Kuma dukkan su wadannan ’ya’ya nata sun yi shahada ne a waki’ar Karbala.
Ga sunayen ’ya’yan nata da kuma shekarun da kowannensu ya yi a duniya: Sayyid Abbas 34, Abdullah 25, Usman 21, sai kuma Ja’afar 19. Kuma dukkan wadannan ’ya’ya nata sun yi shahada ne a Karbala. Lokacin da labari ya zo Madina dangane da abubuwan da suka faru a Karbala, abin da ya damu Ummul Banin shi ne Imam Husain, domin wanda ya zo da maganar tana tambayar sa dangane da me ya samu Husain? Sai yake ce mata an kashe maki danki wane da wane. Ta ce Husaini fa? Sai ya ce shi ma an kashe shi. Jin haka, sai ta fashe da kuka.
3- Lakubbansa: Sayyid Abul Abbas yana da lakubba masu yawa. Ana ce masa Kamaru Bani Hashim, wato saboda gayar kyan halitta da Allah ya yi masa. Ana kuma ce masa Babul-Hawa’ij, wato saboda duk wanda ya yi tawassuli da shi, tare da iklasi ga kowace bukata tasa, to Allah Ta’ala zai biya masa bukatar sa. Ana kuma ce masa Hamilu-liwa’i, domin a ranar Ashura shi ne Imam Husain ya ba tuta. 4-Nash’a dinsa: Sayyid Abul-Fadhal Abbas ya tashi a Madina, ya kuma rayu tare da mahaifinsa shekaru 14, tare kuma da Imam Hasan (AS) shekara 24, tare kuma da Imam Husain (AS) shekaru 34. Abul Fadhal Abbas ya kasance ko da wane lokaci yana tare da Imam Husain (AS) 5-Shekarunsa: Ya rayu a duniya shekaru 34 ne. 6- ’Ya’yansa: Yana da yara biyu maza, sune Fadhal da kuma Kasim, wato shi ya sa ake yi masa kinaya da Abul Fadhal. Dan sa Kasim ya yi shahada ne a Karbala.7- Wafatinsa: Ya yi shahada ne ranar 10 ga watan Muharram shekara ta 61 bayan hijira. 8- Kabarinsa: Yana a Karbala ne, wato kusa da na Imam Husain (AS).
Nan kuma wasu sassa ne na rayuwar Imam Zainul Abidin. 1-Haihuwarsa: An haifi Imam Zainul Abidin a Madina ranar Juma’a 5 ga watan Sha’aban shekara ta 38 bayan hijira. 2- Nasabarsa: Sunan mahaifiyarsa Maryam, a wata ruwaya Fadima. Asalinta Bafarisa ce, wato mutuniyar Iran. Kuma ita diya ce ga Sarkin Iran na lokacin mai suna Yazdajir. Kafin zuwansu Madina ta yi mafarki da Manzon Allah (S) da kuma Sayyida Zahra (AS). 3- Nash’a dinsa: Imam Zainul Abidin ya tashi a Madina. Bayan haihuwarsa, Allah Ta’ala ya yi ma Mahaifiyarsa rasuwa, kuma shi kadai ne a wajen Mahaifiyarsa. Ya rayu tare da Kakansa Imam Ali shekara biyu, tare kuma da Amminsa Imam Hasan shekaru 12, tare kuma da Mahaifinsa Imam Husain shekaru 23. Ya kuma rayu bayan shahadar Mahaifinsa shekaru 34 ne. 4- Shekarunsa: Imam Zainul Abidin (AS) ya rayu a duniya shekaru 57 ne. 5- Lakubbansa: Imam Zainul Abidin yana da lakubba masu yawa, amma lakubbansa da suka fi fice sune Sajjad, wato saboda yawan sujudarsa. Zainul Abidin, wato saboda yawan ibadarsa. Kuma ana yi masa kinaya da Abu Muhammad. 6-Muddan Imamancinsa: Shekaru 34 ne. 7- ’Ya’yansa: Imam Zainul Abidin ya kasance yana da ’ya’ya 15 - maza 11, mata hudu. 8- Wafatinsa: Ya rasu ranar 25 ga watan Muharram shekara ta 95 bayan hijira. 9- Kabarinsa: Yana a madina ne, wato a makabartar Baki’a.
Nan kuma wasu sassa ne na rayuwar Imam Mahdi (AF). 1-Haihuwarsa: An haifi Imam Mahdi (AF) a garin Samarra, wato a Irak ranar Juma’a 15 ga watan Sha’aban shekara ta 255 bayan hijira. 2-Nasabarsa: Sunan mahaifiyarsa Narjis, nasabarta na tukewa ne ga Wasiyyin Annabi Isa wato Sham’un. Sunan Mahaifinsa Imam Hasan Al-askari (AS). 3- Nash’a dinsa: Imam Mahdi ya rayu tare da Mahaifinsa shekaru biyar. Bayan rasuwar Mahaifinsa, ya shiga gaiba karama, ana ce mata gaiba ta farko. Tsawon shekarun wannan gaiba ta farko shi ne shekaru 69. Bayan haka kuma ya shiga gaiba babba ana ce mata gaiba ta biyu.
Tambaya a nan mene ne bambanci tsakanin gaibar farko da ta biyu? Bambancin shi ne, a ta farko akwai wasu bayin Allah ko Jakadu guda hudu da yake da alaka da su, wadanda ta hanyarsu yake ba da umarni ko hani zuwa ga Shi’arsa, ko kuma su idan suna da tambayoyi ko wasu matsaloli sukan gabatar ta hanyar wadannan Jakadu. Sai dai nan a lura wadannan Jakadu ba sun kasance a lokaci guda ba ne, a’a sun kasance ne daya bayan daya. To, a gaiba ta biyu, babu wadannan Jakadu, sai abin da ake ce ma Nuwwab, amma wadancan kuma Nuwwab khassa.
4- Lakubbansa: Yana da lakubba masu yawa. Daga cikin su akwai Al- Mahdi, Al-Ka’im, Al-Muntazar, da Sahibuz Zaman. Haka nan ana yi masa kinaya da Abul-Kasim. 5- Shekarunsa: A yanzu Imam Mahdi (AS) yana da shekara dubu daya da dari daya da tamanin, wato 1180 a duniya. Saboda haka a wannan al’umma ta Manzon Allah ba wanda ya kai shi yawan shekaru. Ta yiwu wani ya tambaya cewa mutum zai iya tsawon rai haka? Amsa na’am. Idan mutum ya duba tarihin wasu Annabawa da ma wadanda ba Annabawa ba, zai ga haka. Misali Annabi Nuhu (AS) ya yi shekaru 2,500 a duniya, ya shekara 850 gabanin aiko masa da sako, ya shekara 950 wajen isar da sako, ya kuma shekara 700 bayan halakar da mutanensa. Annabi Adam shi kuma ya shekara 930 a duniya, Annabi Idris 965, Annabi Hudu 962. Saboda haka wannan tsawon rai na Imam Mahdi ba wani bakon abu ba ne a tarihin dan Adam. Kai ko da ma ba a samu a cikin tarihi wani ya yi tsawon rai irin haka ba, hujjar cewa Allah Ta’ala Mai iko ne a kan komai ya wadatar.
Nan kuma wasu sassa ne na rayuwar Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H). Kasantuwar wannan wata na Sha’aban ne aka haifi Malaminmu kuma Jagoranmu a wannan gwagwarmaya ta tabbatar da addini, ga wasu sassa na rayuwarsa mai albarka. 1-Haihuwarsa: An haifi Sayyid Zakzaky (H) ne a birnin Zariya ranar Talata 15 ga watan Sha’aban, shekara ta 1372 bayan hijira, wanda ya yi daidai da 5 ga watan Mayu 1953 Miladiyya. 2- Nasabarsa: Sunan Mahaifinsa Yaqoub, shi kuma dan Aliyu dan Tajuddin dan Limam Husain. Shi Liman Husain, wani Malami ne kuma bawan Allah da ya fito daga Mali ya zo garin Sokoto a lokacin Shehu Usman dan Fodiyo. Sunan Mahaifiyarsa Hajiya Salihatu. 3- Nash’a dinsa: Sayyid Zakzaky (H) ya tashi a garin Zariya, kuma ya taso mai riko da son addini, kuma ya kasance mai hazaka da basira tun tasowarsa. Ya yi karatu a wajen Malamai daban-daban a Zariya da Kano. 3-Lakubbansa: Akwai Al-Zakzaky, wanda yake nufin mutumin Zazzau. Akwai kuma lakubba da Shehu Usman ya ambace shi da shi. Misali Sharafud-din da kuma Ibrahimul Magribiy. 4-Shekarunsa: Yanzu yana da shekaru 63 a duniya. 5- ’Ya’yansa: Yana da ’ya’ya 9 - maza 7, mata biyu. 6- Muddan da’awarsa: A yanzu haka Sayyid Zakzaky ya kwashe kusan shekaru 40 yana wannan kira domin tabbatar da addini a wannan kasa.
Sai kuma abin da ya shafi ayyuka na ibadodi da ake son aikatawa cikin wannan wata na Sha’aban. Ayyukan sun kasu kashi biyu. Akwai ayyuka na ‘Ama’(na bai-daya) wato sune ayyuka na ibadodi da ake son aikatawa a kowace rana cikin watan Sha’aban. Akwai kuma ayyuka na ‘hassa’ (musamman), wato sune ayyukan da ake son aikatawa a wasu raneku ko darare na cikin watan Sha’aban. Wannan ke nan a dunkule, amma a warware mutum na iya duba littafin Mafatihul Jinan ko Dhiya’us Salihin da sauransu.
Wani tambihi a nan shi ne, wannan wata da muka ciki na Sha’aban, wata ne na shiri da kuma yin shimfida ga babban bako da yake tafe, wato watan Ramadan. Wato dai kamar yadda yake bisa al’ada, in za ka yi babban bako, to za ka yi shirye-shirye na zuwansa, to haka ya kamata mutum ya yi kafin zuwan watan Ramadan. Ya kasance ya shirya kansa ta hanyar tazkiyyar naf’s dinsa, wato tsarkake kansa, zahiri da badini, da kuma horas da kansa ga ayyuka na ibadodi daban-dabam, ta yadda jikinsa zai saba kafin shigar watan Ramadan. Domin ya kasance mutum ya samu saukin raya dararensa da kuma ranekunsa da ibadodi. Haka nan kuma domin ya samu zauki da halawar watan Ramadan.
Sanarwa
Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)
Labarai cikin hotuna
Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana