Juma'a 15 ga Sha'aban 1435 | Bugu na 1133 | ISSN 1595-4474 |
---|
Babban Labari
Almajiran Shaikh Zakzaky sun je ta'aziyyar rasuwar Sarkin Kano
Daga Muhammad Sakafa da Hasan Baffa (muhammadsakafa@yahoo.com)
Tawagar ta ’yan uwa da ke karkashin jagorancin Wakilin Shaikh Zakzaky a Kano, Shaikh Mahammad Turi, sun samu gagarumar tarba da girmamawa daga daya daga cikin ’ya’yan Sarkin na Kano.
Shaikh Muhammad Turi ya isar da sakon ta’aziyyarsa a madadin Shaikh Ibraheem Zakzaky, tare da jajanta masu kan rashin Mahaifi da suka yi.
Daga karshe Shaikh Muhammad Turi ya yi addu’a neman rahamar Allah ga mamacin
Iyalan Sarkin sun nuna farin cikinsu da zuwan wannan babbar tawaga ta ’yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky. Daga nan suka rako tawagar suna godiya ga ’yan uwa bisa wannan ta’aziyya da suka suka yi masu.
Sanarwa
Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)
Labarai cikin hotuna
Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana