Almizan: Jarida don karuwar Musulmi

AlmizanAlmizan logo
Juma'a 15 ga Sha'aban 1435 Bugu na 1133 ISSN 1595-4474


Babban Labari

An sace mata Fulani 40 a Borno

Me ake nufi ne?


Fulani
Rahotanni daga jihar Borno sun ce, wasu ’yan bindiga sun sace wasu mata Fulani masu yawa a wata Rugar Fulani. An ce Rugar ba ta da nisa daga garin Chibok, inda kusan watanni biyu da suka wuce aka sace wasu ’yan matan Sakandare su fiye da 250, kuma har ya zuwa lokacin hada rahoton nan ba a gano su ba...

Wani Jami’in gwamnatin Bornon ya shaida wa manema labarai cewa, sun sami labarin aukuwar lamarin, amma ba za su iya tabbatar da shi ba.

Rahotanni sun ce lamarin ya auku ne a wata Rugar Fulani da ke kusa da Chibok, inda wasu ’yan bindiga suka yi awon gaba da su, kamar yadda daya daga cikin shugabannin Fulani da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana wa manema labarai ta wayar tarho.

Ya ce, “Al’amura suna faruwa da matanmu na Fulani; kafin ma maganar sace wadannan matan Fulani, akwai mata wadanda ake daukewa, a samu mazajensu a ce sai sun ba da shanu kamar 30 ko 40 kafin a sako wadannan matan. Yau bai wuce kwana biyar ba da aka sako wata mata da aka dauka bayan an kai shanun da suka ce dole sai an ba da.”

Sannan ya ce, “a yanzu haka ma akwai mata guda 40 da aka tafi da su da aka bi gida-da-gida aka debe su. Amma abin kowa na jin tsoro, ba kowa zai iya fitowa ya ce an sace mana mutane ba. Wadanda aka tabbatar mana dai mata arba’in ne.”

Haka kawai ake bi gida-gida ana daukar su? “Suna zuwa da makamai ne su ce a fito, a fito. Bayan an tara mutane, sai su tantance. Ba a daukar tsofaffi, sai dai a duba wacce ta haihu daya, biyu, uku, sai a hada a tafi da su. A ce ku ku yi nan, sai a tafi da su.”

An tambaye shi, su wane ne ke sace matan? “To, wallahi mutane ne dai suke zuwa da makamai da yawa, kuma za ka gan su da yunifom na soja.”

Amma wani Jami’in gwamnatin Borno ya ce, a labarin da suka samu mata 20 aka sace, amma suna ci gaba da yin bincike.

Ita kuwa gwamnatin Tarayyar Nijeriya, a ta bakin Shugaban Cibiyar ba da bayanai kan tsaro, Mike Omiri, ta ce, ba ta san da labarin ba. “A gaskiya mu ba mu samu labarin ba. Labarin da muka samu shi ne na sojojin Nijeriya da suka yi yaki da wadannan ’yan boko Haram a Vital kusa da Chibok din.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron