Almizan: Jarida don karuwar Musulmi

AlmizanAlmizan logo
Juma'a 15 ga Sha'aban 1435 Bugu na 1133 ISSN 1595-4474


Labaran Harka Islamiyyah

Fudiyya Zariya ta yi bikin yaye dalibai 77

Daga Aliyu Saleh


Fudiya Zariya

A ranar Asabar din nan da ta gabata ne, Madrasatul Fudiyya Zariya ta yi bikin yaye dalibai a bangaren manya da kananan makarantun sakandire, yayin da Shaikh Ibraheem Zakzaky ya zama babban bako a wajen taron...

A cikin jawabinsa, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya jawo hankalin bangarori daban-daban, kama daga iyayen yara, Malamai da dalibai a kan su tashi tsaye wajen ganin an samar da ingantacen ilimi a tsakanin ’yan uwa.

Ya bayyana cewa shi karatu ba kawai yana ka iya rubutu da karatu a takarda ba ne, ko kuma a koya maka iya magana ba, ko fahimtar harshe ba, “Tarbiyya ne ake yi wa mutum. Tarbiyya shi ne girmamar da abu da kuma rayar da shi kamar yadda ya kamata. Kamar yadda aka yi tarbiyyar tsiro ta hanyar ba shi da ruwa da duk abin da yake bukata kafin ya girmama ya zama ya kai mustawar da ya ba da kakkyawar natija”.

Ya ci gaba cewa; “Shi kuma mutum ana tarbiyyarsa ne domin ya ba da kyakkyawar natija. Shi mutum yana da bambanci da sauran halitta, ta cewa su sauran halitta idan suka gama bukatansu na yanzu, al’amarin ya riga ya kare. Amma shi mutum ba haka yake ba, shi al’amarinsa ana tarbiyyarsa ne saboda shi yana da wata rayuwa wadda take ta wuce wannan. Kuma a nan ake son a samu kyakkyawar natija din, wanda wannan natijar ba za a same ta ba, sai an samu kyakkyawar natija a nan. Saboda haka ana tarbiyyar sa ne ya zuwa makoma. Don haka ne ma a tafarkin komawa ga makomar ya zama ya gamu da aljalinsa, shi ba asara ya yi ba. Ana tarbiyyar mutum ne domin a samar da bawan Allah na gari”.

Shaikh Zakzaky ya yi watsi da irin ra’ayin nan da ke nuna cewa ana son mutum ya yi karatu ne domin ya samu aiki. Ya ce, abin takaici har ma ana tambayar yara idan sun kammala karatu me suke so su zama? Wani ya ce soja, wani ya ce dan sanda, wani ya ce direba, wani ya ce Gwamna. Ya ce wannan tambayar ba ta da ma’ana. “Ba ta tarbiyyar mutum don zama wannan. Bai ma kamata a tambayi yaro me kake so ka zama ba, don ba ita ce matsalar da ke gabansa ba yanzu. Abin da ya kamata a nuna masa shi ne yana da makoma ta nesa da ta kusa. Ta nesa ita ce lahira, ta kusa ita ce kafin ya je lahira. Kuma ya rika hankoron wannan manfar, ya zama bawan Allah na gari”.

Tun farko sai da dalibai na bangarori daban-daban ne suka gabatar da karatuttuka a kan wasu darrusa, da kuma wasu muhimman abubuwa da suka shafi karatun nasu, wanda ya yi matukar burge mahalarta taron.

Ita dai wannan makarantar wacce aka kafa ta a shekarar 1990, ta yaye dalibai a bangarori daban-daban, dalibanta na Jami’o’i da sauran manyan Cibiyoyin ilimi, kuma tuni har sun samar wani tsari, idan suke dawowa wajen ba da gudummawarsu a fannoni karantar da sauran daliban da suke karatu a makarantar yanzu.

A jawabinsa Shugaban makaranta, Malam Kabir Abbas, ya bayyana irin namijin kokarin da suke yi wajen ganin sun inganta harkar koyar a makarantar, wanda hakan ya sa yanzu Hukumar tantance makarantu masu zaman kansu ta amince masu, kuma aka ba su damar su zama Cibiyar shirya jarabawar SSCE, kamar yadda kuma suke samun manyan makarantu da Cibiyoyin ilimi suke aiko da mutane suna zuwa koyarwar gwaji.

A jawabinsa, Malam Abdulhamdi Bello kokawa ya yi da irin rikon sakainar kashin da wasu daga cikin ’yan uwa, musamman na Zariya suke nuna dangane da kula da karatun ’ya’yansu da kuma tallafa wa wannan makarantar. Ya ce akwai bukatar ’yan uwa su canza wannan yanayin. Akwai bukatar a samu canji cikin gaggawa.

Sai dai kuma duk da haka ya yi jinjina ta musamman ga wasu daga cikin tsayayyun da suke sadaukar da dan abin da suke da shi wajen ganin an inganta makarantar. Ya yi fatan ’yan uwa za su kara zage damtse wajen ganin an cimma hadafin kafa wannan makarantar.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

    GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
    Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
    Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

    Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

    Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
    Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


    Labarai cikin hotuna

    Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
    • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron