Almizan: Jarida don karuwar Musulmi

AlmizanAlmizan logo
Juma'a 15 ga Sha'aban 1435 Bugu na 1133 ISSN 1595-4474


Labaran Harka Islamiyyah

Lajnar Fudiyya ta gabatar da Mu’utamar a Zariya

Daga Idris Muhammad


Muassasr Ilimi title=

Kamar yadda ta saba, Lajnar Fudiyya Am, wacce take da hakkin kula da yadda makarantun Fudiyya na Harka Islamiyya a Nijeriya a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky ke gudana, ta gabatar da taron kara wa juna sani ga Malaman da ke karantar da harshen Larabci da Turanci da kuma Lissafi a makaratun Fudiyya na Harka baki daya...

Taron na bana mai taken inganta fikirar koyar da harsunan Larabci da Turanci hade da Lissafi, an fara gudanar da shi ne ranar Alhamis 8 ga Sha’aban 1435 a Fudiyya Islamic Center da ke Dan Magaji Zariya, inda Malam Abdulrahaman Sa’id Ango na Kwalejin horar da Malamai na Tarayya FCE Zariya ya fara gabatar da makala a kan dabarun koyar da harshen Turanci da kuma yanayin gudanar da aji ga Malamai.

Malamin ya gabatar da cewa abin da ake kiran sa da dabarun koyarwa suna da yawan gaske, amma ya yi talkisun wadannan hanyoyin guda shida da ya yi cikakken bayani a kansu daya bayan daya.

Wadanda ya zaba kuwa sune kamar haka; Classroom method. 2. Group method. Questioning method. 4. Discussion method. 5. Excursion method. 6. Dictation method.

Sannan sai Malamin ya dauki bayani a kan yadda ake koyar da Turanci. Ya ce, Turanci bai da wahala idan aka bi wadannan matakan, kamar haka. Amfani da ka’idojin shi. Yarda da wadansu abubuwa da ake kira ‘basic skill’, wadanda suke dole ne a san su, sune kamar haka; i) Listening skill. ii. Reading skill. iii. Speaking skill. iv. Writing skill.

Ya kuma ci gaba da cewa dole ne a san ‘parts of speech’ da yadda ake amfani da su da sanin adabin Turanci. Malamin ya ambaci cire tsoro wajen amfani da ‘basic skills’ da kuma kokari wajen amfani da wadannan ‘basic skills’ din da ya ambata a matsayin matakan cin nasara a koyar da harshen Turanci.

Sai Malami na biyu, wanda shi ma ya gabatar da nasa jawabi a kan dabarun koyar da Lissafi ga makarantun Fudiyya da yanayin gudanar da aji.

Malam Muhammad Kabir Abbas Principal ne makarantar Fudiyya Secondary School, Zariya. Shi ya gabatar da wannan makalar. Malamin ya jawo hankalin mahalarta taron da cewa darasin lissafi bai da wahala, sauki ne da shi ga wadanda ya mayar da hankali a kansa. Wannan kuma shi ne matakin farko da za a yi kokarin nuna wa dalibai idan har ya zama bai tsaron darasin insha Allah zai sanya himma wajen koyonsa, kuma ba tare da shan wata wahala ba.

Ya ce darasin Lissafi darasi ne da ke bukatuwa ga samun yanayi na tunanin domin a gano abin da ake so a gano, sannan akan fara da mafi sauki ne, kafin mai sauki, sannan zuwa mai tsauri.

Malami na uku wanda ya cike gurbin Malamin da ya kamata ya gabatar da makala a kan matsalolin koyar da harshen Larabci da yadda za a warware su shi ne Malam Salisu M. Bala, wanda yake daga Jami’ar Maiduguri. Ya gabatar da tarihin harshen Larabci, wanda Imam Ali bi Abi Talib ya ba da gagarumar gudummawa gaya wajen habaka wannan harshen, musamman wajen samar masa da nahwu, wanda ke magana a kan ka’idojin magana da Larabci.

Malamin ya ambaci cewa daga cikin matsalolin da ake fuskata wajen koyar da harshen Larabci akwai rashin kwarewar Malaman Larbci, ya ce mafi yawansu ’yan ci-karfi ne, sannan littafan da ake koyar da mutane ko yara ba su dace da su ba, ba an rubuta su ne domin mutanen muhallin da ake rubuta su domin su.

Ya ce, mafita ga wadannan matsalolin sune dole ne mu koma mu tsara littafin da za su dace da su, ko ma daidai da kwakwalwarsu a matsayinsu na Ajamawa.

Sannan dole ne mu koma manufa irin ta su Sayyid Zakzaky na samar da ingantaccen ilimi da tarbiyya na Musulunci. Malamin ya bukaci a yawaita yin Larabcin da su daliban, kuma a yawaita nazarin harshen a kowane mataki. Wannan zai taimaka.

Malam Muhammad Salaiman Malumfashi ya yi tsokaci ne a kan wannan maudi’in, a inda ya jawo hankalin mahalarta taron da cewa kar a tsaurara wa dalibai wajen koyar da su Larabci, ya kamata ne a kwadaitar da su a yi kokarin sanya masu ‘ragaba’ a kan koyon harshen Larabcin.

Malam Abdulkarim Isa (Abul Kasim) shi kuma ya gabatar da tasa makalar ce a kan matsalolin da ake fuskanta wajen koyar da harshen Turanci da kuma hanyoyin magance su.

Malamin ya ambaci matsaloln harshen Turancin kamar haka; Rashin sanin harshen, wato babu kwarewa a kan shi da kuma rashin kayan aiki. ‘English culture’ (al’adun Turawa), wanda yake ya saba wa addinin Musulunci. “Lallai dole ne mu yarda da cewa al’ada tana da tasiri wajen koyo da koyar da harshe. Saboda haka dole ne a yi watsi da al’adun Turai da suka saba wa Musulunci”, in ji shi.

Har ila yau ya ce, idan ana bukatar a san harshen Turanci, to dole a samar da manhajar da ta dace da yanayin da muke ciki, sannan dole a samu kwararrun Malamai a kan harkar koyarwa.

Daga cikin hanyoyin koyar da kowane harshe akwai sanin haruffan kamar A.B.C.D. a harshen Turanci a san su a karance da kuma rubuce har ma ya haddace su.

Sai kuma a koya wa yaro yadda ake rubuta su, musamman a yi amfani da littafin nan da ake cewa ‘writing exercises’, sannan a koya wa dalibi gina kalmomi da kuma koya masa hada jimla, akan fara daga saukakkun jimloli, daga nan sai a koya masa ‘part of speech’, bayan nan sai a samu ‘introduction of speech’, sai kuma ‘figures of speech’. Daga nan sai a koya masa ‘punctuations’. Ya ce dole ne a samar da wa dalibi ka’idojin rubutu, kamar su ‘comprehension’, ‘summary’ da ‘conclusion’. Akwai bangarorin ‘lexis and structures’ da ‘register composition’ rubutun zube, wani jigo ne cikin koyon harshen Turanci.

Malamin ya yi bayanin cewa kawai bangarori masu yawa a harshen Turanci wadanda idan har ana da wadatattun Malaman Turanci a makaranta ya kamata kowanne ya zama Malaminsa daban ne, kamar a ce ‘lexis and structure’ Malaminsa daban da na ‘English grammar’.

Malam Sabo ATC daga Katsina shi ne Malami na biyar da ya gabatar da makala a kan dabarun koyar da harshen Larabci a makarantar Fudiyya da kuma yadda Malamin koyar da harshen Larabci zai tafiyar da aji.

Malamin cikin shamfidarsa ya kawo tarihi da matakan da harshen Larabci ya kasance, ciki har zuwa wannan lokacin da muke ciki.

Cikin hanyoyin da Malamin ya kawo cewa Malamin da zai koyar da dalibi dole ya zama ya san hanyar da zai bi ya koyar da dalibai. Dole ne cikin sa ya dinga la’akari da halin da dalibinsa ke ciki, suna cikin nishadi ne, ko kuma suna cikin rashin walwala ne a cikin aji. Malamin ya kawo hanyoyin da Malami ya kamata ya kasance ya bi har guda bakwai.

Sannan ya yi bayani a kan cewa kowane Malami da zai karantar da harshen Larabci, dole ne ya zama masanin dabarun koyarwa ne, wanda ya ce kuma suna nan da yawa, a inda ya tsakuro wasu ya yi bayani a kansu.

Malamin na shida cikin jerin Malaman da suka gabatar da makala shi ne Dakta Abubakar Gado na Jami’ar Umar Musa ’Yar’aduwa da ke Katsina.

Malamin cikin shimfidarsa ya ce lokacin da ake rubuta masa maudi’in da zai gabatar, sai da ya sanya shi tunanin me ya sa za a ce ya gabatar da magana a kan matsalolin koyar da Lissafi a makarantu. Amma da ya zo sai ya ga akwai kwatankwancinsa a Turanci da Larabci a tsarin jadawali da aka gabatar.

Shi ne dai ya yi iya bakin kokarinsa wajen ya jawo hankalin Malamai su gane cewa Lissafi ba matsala ba ne, illa iyaka ana bukatar natsuwa da ragaba a cikin sa ne.

Malam Abdulhamid Bello a jawabinsa na rufewa, ya jawo hankalin Malamai da su kara kokari da sadaukarwa da suke yi, kuma mu yi kokarin koyon hanyoyin koyarwa da dabarunsu.

Malamin ya nuna jin dadinsa da yadda taron ya gudana ne a karkashin jagorancin yankuna na Lajnar Fudiyya Am.

Malamin ya bukaci Malamai da Hedimastoci su kara himma dangane da koyar da wadannan darussan guda uku, Larabci, Turanci, da kuma Lissafi. Ya kuma bukaci Malamai gaba daya da su kara dagewa domin mu cika wa Jagoranmu burinsa kan ’ya’yanmu dangane da ilimi da tarbiyya.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

    GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
    Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
    Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

    Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

    Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
    Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


    Labarai cikin hotuna

    Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
    • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron