Juma'a 15 ga Sha'aban 1435 | Bugu na 1133 | ISSN 1595-4474 |
---|
Labaran Harka Islamiyyah
Shurafa sun gudanar da Maulidi a Kaduna
Ranar Asabar da ta gabata ne Sharifai almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky suka gabatar wani gagarumin bikin Maulidi don tunawa da ranar da aka haifi Manzon Allah (AS), Imam Ali da Fatima (AS), wanda kuma ya gudana a dakin taro na Gamji da ke Kaduna, inda jama’a daga sassa daban-daban na kasar nan suka sami halarta...
Sharifai da dama ne suka gabatar da jawabai a wannan wuri. Cikin jawabin da ya gabatar, Sharif Ma’aruf, wanda kuma ya yiwo takakka daga Kano, ya bayyana cewa duk wani abu da mutum zai yi a duniyar nan, musamman a cikin addini, in ba ya yi tare da soyayyar Iyalan gidan Annabi (S) ba, to ya yi aikin banza, domin Allah ba zai kalle shi ba.
Da yake magana game da Sayyida Fatima (AS) kuwa, Sharif Ma’aruf cewa ya yi, “addinin Musulunci nata ne, Allah nata ne, Manzon Allah nata ne, Hasan nata ne, Husaini nata ne, ita kanta Aljanna tata ce, duniya tata ce, lahira tata ce, alkiyama da barzahu, duk nata ne.”
Saboda haka sai Sharifin ya bayyana cewa babu yadda za a yi mutum ya samu tsira duniya da lahirarsa, ba tare ya nuna soyayya gare ta da mahaifinta, mijinta da ’ya’yanta ba. Yana mai cewa haka kuma babu tantama, duk makiyinta, ba shi ba rahamar Allah ranar lahira, duk wanda ya cutar da ita dan wuta ne.
Ita kuwa Sharifiya Marya cewa ta yi Iyalan gidan Annabi ne tsirar duk wani mai neman tsira, kamar yadda yake kuma babu tsira ga duk wanda bai kama su ba. Ta ce “wallahi da ba don Fatima ba da ’ya’yayenta, da sai dai a tattara a zuba a wuta.
Shi ma Sharif Al’alawi, wanda ya yiwo takakka daga Kano, ya yi nasa jawabin ne shi ma cikin darajoji da falalolin da Allah ya yi wa Ahlul Baiti (AS).
Sanarwa
Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)
Labarai cikin hotuna
Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana