Almizan: Jarida don karuwar Musulmi

AlmizanAlmizan logo
Juma'a 15 ga Sha'aban 1435 Bugu na 1133 ISSN 1595-4474


Labaran Harka Islamiyyah

Maulidin Sayyida Zahra (as) a garin Masaka ya kayatar

Daga Sirajo Shehu Abuja


Sayyada Fatima

Ranar Laraba 29 ga Rajab 1435 (28/5/2014), 'yan uwa mata na Halkar Amirul muminin a garin Masaka Da'irar Abuja suka shirya wani gagarumin Maulidin Sayyida Fatima (as)...

Maulidin, wanda aka gudanar a babban masallacin Juma'a da ke kan hanyar Abuja-Keffi, an fara shi ne tun da misalin karfe takwas, duk da ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya sauko daidai fara Maulidin.

Mal. Musa Kuchikau ne ya bude taron da addu'a, sai karatun Alkur'ani mai tsarki daga dalibar Fudiyya Karima Kabiru, sai kuma wake daga shu'ara. Bayan nan ne sai aka saurari wani waken yara 'yan Fudiyya.

Wani abin da ya dauki hankalin mahalarta taron shi ne, irin yadda yaran suka rinka rera waka mai dauke da tsararren karatu, wanda yake dauke da tarihin rayuwar Sayyida Zahra (as). Abin da za a iya kira da sunan jawabi daga yaran. Waken nasu ya tabo kowane fanni ko bangare na rayuwar Sayyida Fatima Azzahra (as), kamar matsayinta a gurin Allah (T), fifikonta kan dukkan matan talikai, matsayinta a wajen Mahaifinta, Mijinta, da kuma wasu kebabbun martabobi nata, dss.

A wani bangaren na waken, yaran sun yi bayani a kan irin musgunawa, cutarwa da zaluncin da aka yi wa Sayyida (as) bayan wafatin Mahaifinta Manzon Allah (S). Kamar kai mata hari, dukan ta, sabbaba barin cikinta da shahadarta. Bayan nan sai aka ci gaba da gabatar da Maulidin kamar yadda yake a tsare, inda aka saurari karatuttuka daga bakin 'yan uwa mata a matakai daban-daban, kamar Ziyarori, Tarihi, Fikh, Hadisi, da sauransu.

Haka kuma ’yan uwa matan sun gabatar da jawabi a kan Sayyida cikin harsunan Larabci, Turanci da kuma Hausa. Daga bisani 'yan uwa matan sun gabatar da wata 'yar kwarya-kwayar tamsiliyya a kan matsayin Hijabi ga 'yan mace a addinin Musulunci.

Bayan haka ne sai Wakilin 'yan uwa na Abuja, Malam Abubakar A. Bugawa ya yi dan takaitaccen jawabi, saboda kuncin lokaci, sakamakon ruwan da aka samu a baya. Malamin ya kawo takaitattun bayanai dangane da Sayyida Fatima (as), da matsayinta, dss.

A daya bangaren na jawabinsa Malamin ya mai da hankali sosai gami da kule ga 'yan uwa, dubi ga irin bajintar da sistoci da kuma yara suka nuna. Ya kuma yaba wa wadanda sun ka shirya wannan Maulidi, wato 'yan uwa mata, inda ya yi addu’ar ganin an samu ci gaba a shekaru masu zuwa. Haka nan ya ja hankalin 'yan uwa baki daya da su tashi tsaye su yi hobbasa wajen ganin an samar da matsugunin Fudiyya na dindindin a garin na Masaka.

Haka nan Malamin ya nuna farin cikinsa ga irin kwazon da yara 'yan Fudiyya suka nuna, da ma 'yan uwa matan wajen gabatar da karatuttuka. Inda ya kara jan hankalin 'yan uwa da su tashi tsaye don ganin sun habaka wannan bangare na ilimi. "Duk wannan karatuttuka da muka ji ana yin su ne, a dan wani guri, ko dakin kwana, saboda haka akwai bukatar 'yan uwa su tashi don ganin an samar da azuzuwa."

Malam Abubakar ya ci gaba yana cewa; "Akwai bukatar kula da su kansu Malaman bisa wasu bukatu, kamar kayan karatu, dss. Wannan duk yana daga cikin raya al'amarin Ahlil baity (as).”

Ya kawo wani Hadisi na Imam Sadik (as) yana cewa: "Allah ya yi rahama ga wanda ya raya al'amarinmu! Allah ya yi rahama ga wanda ya raya al'amarinmu! Sai aka tambaye shi (as), ya ake raya al'amarinku? Sai ya ce: ‘wanda ya karantar da iliminmu, to ya raya al'amarinmu, domin mutane in suka san iliminmu, lallai za su so mu, kuma su bi mu. Bin mu kuma bin Muhammad Rasulullahi (s) ne.’ Saboda haka akwai bukatar 'yan uwa su mai da hankali a kan haka.”

Daga bisani an yi walima, sai aka rufe taro da addu'a. Jama'a da dama sun nuna mamaki, musamman ga irin yadda yara 'yan Fudiyya suka nuna kwazo da hazaka, irin yadda suka gabatar da jawabi a cikin wake. An kammala taro lafiya, kowa yana sambarka, da fatan ganin na badin-badada.


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

    GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
    Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
    Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

    Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

    Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
    Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


    Labarai cikin hotuna

    Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
    • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
    • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron