Almizan: Jarida don karuwar Musulmi

AlmizanAlmizan logo
Juma'a 15 ga Sha'aban 1435 Bugu na 1133 ISSN 1595-4474


Labaran Harka Islamiyyah

’Yan uwa Muhajirun da ke Suleja sun yi maulidin Imam Ali (AS) a Suleja

Daga Magaji Alh. Idi Zariya


Imam Aliy

A ranar Alhamis 30/7/1435 ne, 'yan uwa Muhajirun din garin Sakkwato da ke zaune a garin Suleja suka gudanar da Mauludin Imam Ali (KW), tare da Murnar Yaumul Mub'ath a makarantar Fudiyyar garin Suleja. Malam Hasan Adamu wakilin 'yan uwa na garin Suleja ne ya gabatar da jawabi a wajen...

Cikin jawabinsa yake cewa, babu yadda za a yi addinin Musulunci ba tare da Imam Ali (KW) ba. Lokacin da aka haife shi Imam Ali ( KW) bai bude ido ba sai da Manzon Allah (S) ya zo. Manzon Allah ne farkon wanda Imam Ali (KW) ya fara gani a rayuwarsa. Manzo (S) ya sanya wa Imam Ali (KW) harshensa a bakinsa. Ya tsotsi hikima, tsoron Allah, jarunta, karfin haki, shaja'a, da ilmi.

Malamin ya kara da cewa lokacin da Manzon Allah ya je Is'ra'i da Mi'iraji, Allah (T) ya aiko Manzon Allah (S) zuwa ga Imam Ali (KW) cewa, "ka ce wa Ali ina gaishe shi. Ka ce masa shi ne Shugaba a bayanka. Kuma ka aura masa ’yarka Fatima".

Da ya koma kan jarumtar Imam Ali (KW) cewa ya yi, a dukkan Sahabbai babu jarumi kamar Imam Ali (KW). Bai taba fuskantar kafiri, ba tare da ya halaka shi ba. Hasali ma a wadanda ake cewa manya, babu wanda ya fi shi Ilmi. Babu Wanda aka haife shi a Ka'aba sai shi.

Ya ci gaba da cewa, sau tari akan zo a tambayi Halifa, ya kasa ba da amsa, sai an nemo Imam Ali (KW).

Da ya koma kan magana a kan Sayyada Fatima (SA) cewa, ya yi babu wata mace da ta kai Sayyada Fatima daraja. Mijinta shi ne Wasiyyin Manzon Allah (S). Babanta shi ne Manzon Allah (S). Ita kuma ita ce Shugabar matan duniya da lahira. 'Ya'yanta su ne shuwagabannin samarin Aljanna.

Malamin ya ci gaba da cewa, ita Sayyada Fatima ( SA) an halicce ta ne da ruwan Ajanna. Domin an sami ruwan halittar ta ne daga cin tuffaha ta gidan Aljanna. Don Haka ita tsarkakakkiya ce. Kuma sam ba ta haila.

Haka kuma Allah (T) ya bai wa Sayyada Fatima (SA) abin da ya bai wa Imam Ali (KW). Ya ba ta ilimi irin nasa. Ya ba ta karfi irin nasa.

A karshe Malamin ya kirayi al'ummar Musulmi zuwa ga amsa kiran Sayyid Zakzaky (H). "Domin ba ka da wata hujja ta kin amsa wannan kira. Domin ga komai nan a fili, sai dai ka runtse idanunka".


Sanarwa

Sanarwa
Nan filin duk wani sanarwa ne daga duk bangarorin Harka Islamiyyah

  GAYYATA ZUWA MAKON IMAM KHOMEINI
  Imam KhomeiniDandamalin Dalibai da Malamai na Harka Islamiyyah (Academic Forum) na sanar da dukkan ’yan uwa cewa za a yi Makon Imam Khomeini na bana, wanda za a fara daga ranar:
  Juma'a 30 ga Mayu 2014 zuwa Laraba 3 ga Yuni 2014

  Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)

  Wannan gayyatar na kowa da kowa ne. Allah ya ba da ikon halarta
  Za mu buga jaddawalin nan gaba kadan in sha Allah.


  Labarai cikin hotuna

  Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana

  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asMalam Zakzaky yana jawabi
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron
  • Yaumul Mab'asSashen 'yan uwa a taron