Juma'a 15 ga Sha'aban 1435 | Bugu na 1133 | ISSN 1595-4474 |
---|
Labaran Harka Islamiyyah
Dandalin Matasan Maiduguri sun yi Mauludin Imam Ali (as)
Daga Hasan Ibrahim Barnawy
A ranar Asabar din makon jiya ne 'yan uwa na Dandalin Matasa da ke Da'irar Maiduguri suka shirya tare da gudanar da gagarumin bukin tunawa da ranar haihuwar Imam Ali (AS). Bukin, wanda ya gudana a Markaz din 'yan uwa da ke unguwar Bulumkutu, ya samu halartar dimbin mahalarta daga ciki da wajen Harka Islamiyya...
A yayin bukin, an gudanar da gagarumin Majalisin mawaka karkashin jagorancin Malam Basiru Sha'iri, inda suka fara kwararo baitocin tunda yammacin wannan ranar har zuwa lokacin da aka gabatar da babban bako mai jawabi. Su ma sauran 'yan uwa ba a bar su a baya ba wajen ba da gudummawar halarta cikin tsari, tsafta, da kuma shigar kaya irin na kure adaka.
Haka su ma iyayen bukin, wato 'yan uwa matasan sun ba da mamaki wajen irin salon da suka yi amfani da shi na shirya filin taron da kuma irin shigar da suka yi mazansu da matansu, da kuma wani hotun su Sayyid Zakzaky (H) da suka kawata shi suka rataya a wuyansu, wanda ke alamta su ne masu gudanar da wannan bukin.
Kazalika bukin ya samu halartar Malamai daga ciki da wajen Harka, yayin da matasan suka zabi Wakilin 'yan uwa na Maiduguri Malam Bala (Yahaya) Sa'idu da ya gabatar da jawabi a wajen. Inda ya gabatar da gamsasshen jawabi a kan tarihin rayuwar Imam Ali (AS), ilminsa, jarumtarsa, hakurinsa, da ma kuma irin darajojin da Allah ya yi masa a birbishin dukkan halittu.
An dai tashi daga wannan buki da misalin karfe tara na dare, inda kowa ya tafi yana jinjina ga irin wannan namijin kokari da matasan suka yi.
Sanarwa
Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)
Labarai cikin hotuna
Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana