Juma'a 15 ga Sha'aban 1435 | Bugu na 1133 | ISSN 1595-4474 |
---|
Rahoto
Kai gwamnatin Siriya kotun duniya:
Faransa ta sha kunya
Daga Sirajo Shehu Abuja
Wannan mataki da kasashen Rasha da Chaina suka dauka bai yi wa Amurka dadi ba, inda ta bakin Jakadiyarta a Majalisar Samantha Power, ta nuna takaicinta. Inda ta ce dole ne kasashen duniya su goyi da bayan a kai kasar Siriya gaban kotun duniya, saboda sakamakon yadda gwamnatin Siriya ta gallaza wa masu adawa da ita. Sai dai a yayin gabatar da bahasin ta Jakadiyar Amurkar ba ta tabo bangaren 'yan ta’addan Siriya ba, duk da cewa kuwa zaman yana da manufar ya kamata a gurfanar da dukkanin bangarori biyun a gaban kotun duniya.
A nata bangare kasar Rasha ta bakin Jakadanta a Majalisar dinkin duniya,Vitaly Churkin, ya zargi kasashen Faransa, Saudiyya da Amuruka da laifin ingiza wutar yakin, ta hanyar samar da makamai ga kungiyar Alka'ida, tare da kutse cikin kasar da ba tasu ba, ta hanyar tura mayaka daga wajen Siriya, wadanda suke da alhakin kisan gillar 'yan kasar Siriya. Ya ce wannan aikin, ba abin yarda da shi ba ne a duniya.
A nata martanin, kasar Siriya ta bakin Jakadanta a Majalisar dinkin duniyar, Dk. Bashar Alja'afari, ya fara ne da jaje ga kasar Najeriya a kan aikin 'yan ta'adda da suke kashe daruruwan mutane a kasar. Sannan ya zargi gwamnatin Faransa, Amurka, Saudiyya, da Isra' ila da laifin dukkanin aikin ta' addancin da ke faruwa a Siriya, da ma Nijeriya na Boko-haram, da Falastinu, Iraki, Afghanistan, da kuma Libiya. Inda ya ce Amurka da Faransa su ke da hannu dumu-dumu a ciki.
Jakadan kasar Faransa da ya kawo batun gaban Majalisar, Mista Gerrad Araud, ya nuna bakin cikinsa da matakin da kasashen Rasha da Chaina suka dauka. Lokacin da yake zantawa da Wakilin talbijin na Aljazeera, jim kadan da kammala taron, ya ce, yanzun dai bisa dokar Majalisar dinkin duniyan ba zai yiwu a kai ga gurfanar da gwamnatin Siriya ba da ma 'yan ta'addan kasar ba a gaban kotun duniya.
Sanarwa
Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)
Labarai cikin hotuna
Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana