Juma'a 15 ga Sha'aban 1435 | Bugu na 1133 | ISSN 1595-4474 |
---|
Rahoto
Hukumar ‘NAFDAC’ na muhimmantar da rayuwar al’umma
In ji Shugaban Hukumar a jihar Neja
Daga Bala Musa Minna
Mista Dadi Nantim, ya fara da bayyana tarihin kafuwar Hukumar, inda ya ce: “Wannan Hukumar ta ‘NAFDAC’, wani reshe ne da ke karkashin Ma’aikatar kula da kiwon lafiya ta kasa, wacce aka kafa ta karkashin doka (decree) ta ‘NAFDAC’ na 19 a shekarar 1999, wanda a yanzu ake kira ‘Act.Cap. N 1’, a cikin dokokin Nijeriya.”
Ya kara da cewa, “an kafa wannan Hukumar ce don ayyuka na musamman, da suka hada da kula da tsarin sarrafawa, ajiya, tantancewa, da shiga-da-fita, tallace-tallace da sayarwa da rarrabawa da rika yin amfani da kayayyakin da duk abin da ya shafi kowane irin abinci, abin sha (drinks) kayan shafe-shafe (cosmetics), sinadarai (chemicals) da kayayyakin harhada magunguna da kuma abin da ya shafi ruwa da ake tacewa (package water), wanda duk wadannan suna karkashin abubuwan da muke kula da komai nasu a hukumance.”
Har ila yau, Mista Dadi ya ce, “ayyukan Hukumar na da yawa ga al’umma, don kare rayuwar jama’a daga hadurra wanda kan samu daga amfani da wadannan kayayyakin da al’umma ke yi yau da kullum.”
Ya ce, “wadannan ayyukan sun hada da duk wani abin da zai hana wata illa ko cuta samun al’umma ta dalilin amfani da kayayyakin da muka fada a baya. Haka kuma mukan gudanar da gwaje- gwaje na kowane kaya, don sanin ko ya cancanta wajen amfani da shi, kafin ya shiga kasuwa don sayarwa, sannan a rika amfani da shi.”
Bugu da kari, ya ce: “Mukan gudanar da bincike na kamfanoni ko masana’antu don sanin yaya tsaftar muhalli da kayayyaki (raw-materials) da Hukumar ke kula da su, wanda mukan tantance yadda ingancin kayayyakin da akan sarrafa suke, da yadda za su shafi abin da za a fitar daga gare su a karshe.”
“Haka kuma mukan kula da yadda sarrafa kayayyakin ke gudana a kamfanonin, yadda ba zai yi illa ga ma’aikatan da masu saye ba. Misali, idan kamfani ko wani dan kasuwa zai sayar da kayan da ya shafi sinadaran da akan yi amfai da su a gonaki, mukan bayyana wa mai sana’ar cewa kada ya sayar da su a wuraren da zafi mai yawa yake ko inda hasken rana zai shafe su, ya yi masu illa. Don abubuwan da aka yi wadannan sinadaran da su ba su bukatar hasken rana ko zafi matsananci.”
“Haka in za a ajiye kayayyakin sha (drinks) mukan tabbatar ana ajiye su a wuraren da aka gina, sannan a sanya su a kan farantai (plates). Ya kasance akwai wadataccen wutar lantarki da wadataccen iska da yake ratsa ko’ina, don kada yanayi ko wani abu ya janyo illa ga kayayyakin. Wannan tsarin zai sanya ko a wajen sayar da kayayyakin su yi daraja don ba su gurbata ba, kuma ba su lalace ba.”
Mista Dadi ya kara da cewa: “’NAFDAC’ kan tabbatar an yi wa duk kayayyakin da akan yi amfani da su a cikin al’umma rajista, don tabbatar da ganin sun cimma matakin cancanta a yi amfani da su wacce gwamnatin Nijeriya ta amince. Yadda ko shigowa da kayayyakin za a yi ko fitarwa ko a nan kasar ake sarrafa su, Hukumar kan kula da su. Hakan kuma kan taimaka wajen sayar da su da amince masu.”
Sannan ya ce, “Hukumar ‘NAFDAC’ takan yi kokarin wayar da kan al’umma kan abin da ya shafi ayyukanta ta hanyoyi da yawa. “Misali, mukan tallata ayyukanmu a kafafen watsa labarai da jaridu. Haka ma, mukan ziyarci sarakunan gargajiya da Hakimai da Dagatai da makarantu, hada hannuwa hukumomin da hakan ya shafa a kasashe na duniya, da sauransu.”
A karshe, ya bayyana yadda Hukumarsa ta yi kokarin shawo kan kamfanoni da masana’antun da ke jihar wurin yin rajistar kayayyakinsu, da kula da wuraren sana’arsu, ta yadda a yanzu suna gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Sannan suna samar da kayayyaki masu inganci, kuma wasu ma a yanzu na kokarin yin rajistar. Wanda kafin zuwansa jihar Neja a shekarar 2009, lamarin ba haka yake ba, kamar yadda ya bayyana.
Ya ce: “Ita wannan rajistar ta kayayyaki da ‘NAFDAC’ ke yi mai sauki ce, inda za ka zo ofishin ‘NAFDAC’ ne, ka nemi ofishina na Shugaban Hukumar, in kana jihar Neja, ko kuma wani Shugaban Hukumar a ko’ina, za ka samu bayanai kan yadda ake rajistar a saukake.”
Sai dai Mista Dadi Nantim ya bayyana matsalolin da Hukumar ke fuskanta, wadanda suka hada da rashin wadatattun ofisoshi a manyan Kananan Hukumomin jihar, kamar Suleja, Mokwa, Kwantagora da Bida, wanda hakan zai saukaka ayyukansu. Da kuma rashin wadatattun motoci don zirga-zirga, da rashin wadatattun kudade ga ma’aikatansu, don gudanar da ayyukansu.
Sanarwa
Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)
Labarai cikin hotuna
Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana