Juma'a 15 ga Sha'aban 1435 | Bugu na 1133 | ISSN 1595-4474 |
---|
Rahoto
‘Ba ni da wani shiri, sai zabin da Allah Ya yi’
In ji Gwamnan Katsina Shema
Daga Danjuma Katsina
Gwamnan na bayani ne a wajen taron da ya yi da manema labarai na bikin dimokradiyya shekaru goma sha hudu da kafuwa a kasar nan.
Gwamnan ya ce, badi kamar yanzu ba shi ba ne ke jagorancin jihar nan, wani ne. Ya ce, ba shi ba ne ke cikin gidan nan, wani ne. Wanda ba don Shema aka gina wannan sabon gidan gwamnati ba. Ba kuma don duk wani Gwamna da zai zo ba. Ba kuma wanda zai nade shi ya tafi da shi. A’a na al’ummar Katsina ne.
Da yake haska nasarar da ya samu, ya yi bayanin cewa sun kammala duk wani aikin da gwamnatin da suka gada ta bar masu, irin su ginin Jami’a, filin jirgin sama, filin wasa irin na zamani, wanda yanzu Shugaban kasa da ya kawo ziyara ya tabbatar babu irin sa a yanzu a kasar nan, da sauransu. Sun kuma assasa nasu wanda suka dora sabo, shi ma kusan duk sun kammala mafi yawansu, wasu kuna na gab da kammaluwa.
Gwamnan ya yi bayanin cewa, shi bai shirya wa zai gaje shi ba, amma al’ummar Katsina su yi Addu’ar Allah Ya kawo masu wanda zai ci gaba da yi masu ayyukan alherin da aka saba. Ya ce, shi kuma zai duba cikin wadanda jama’a ke so, ya ga wa zai tallafawa?
Ya ce, shi bai wa kansa wani tsari ba, sai dai ya mika lamarinsa ga Allah ga duk abin da Ya tsara masa. Gwaman ya yi bayanin cewa, shirye-shirye sun yi nisa na zaben Kananan Hukumomi, wanda nan da lokaci kankane za a ji me ake ciki.
Ya kuma yi bayanin cewa, manoma za su dara a shekarar bana, domin yana da isasshen takin da za a ba su, wanda aka tanade shi tun tuni.
Sanarwa
Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)
Labarai cikin hotuna
Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana