Juma'a 15 ga Sha'aban 1435 | Bugu na 1133 | ISSN 1595-4474 |
---|
Rahoto
Bala’o’in da ke sauka a kasar nan; Masu aikata miyagun laifuka suka jawo
Cewar Shaikh Dahiru Bauchi a Katsina
Shehin ya bayyana cewa, sakamakon zagin waliyyai da kafirta juna ne da wasu suke yi, tare da wasu ayyuka na sabo suka fusata Allah, ya sauko mana wannan bala'i.
Ya soki wasu masu fakewa da Darika suna cewa sun yi ‘wusuli,’ suna iya aikata abin da suka ga dama ko da haramun ne, da cewa, ba ma sun bar Darika ba ne, a’a sun ma yi ridda. Domin babu wanda ya isa ya halasta abin da Allah ya haramta.
Ya ce, akwai bukatar su tuba, su dawo cikin Musulmi. Ya yi kira ga jama'a da cewa idan sun ga wanda za ya iya saurara, to a yi masa nasiha, in kuma bai ji nasihar ba, to a kaurace masa, domin ba Musulmi ba ne.
Shehin ya yaba, tare da godiya ga Injiniya Muttaka a kan wannan yunkuri, ya kuma yi fatan Musulmi masu hali su yi koyi da wannan bawan Allah.
A zantawarsa da manema labarai, Injiya Muttaka, ya bayyana godiyarsa ga Allah a kan wannan lamari. Dangane da iyaye kuma, kira ya yi a gare su da su tura yaransu makaranta, domin samun ilimi, tunda shi ne gishirin zaman duniya, kamar yadda Bahaushe yake cewa. “Ilimin addini shi ne babban gishirin zaman duniya ni a gare ni, saboda shi ne ginshikin kowane ilimi da za ka iya samu."
Ya kara da cewa, idan Allah ya taimake ka, kana da ilimin Alkur'ani da Hadisi da sanin yadda za ka bauta wa Ubangijinka, to ko kiyama ta zo maka, ba sai ka yi wata wahala ba. Saboda haka ilimin addini, ilimi ne mai muhimmanci ba ma kamar mu Musulmi.
Ita dai wannan makaranta da take kusa da makarantar tsohuwar ATC da ke gab da kofar Kwaya, Injijiya Muttaka Rabe ne ya gina ta, ya kuma mika ta ga Shaikh Dahiru Bauci, domin ci gaba da karatun haddar Alkur'ani mai girma.
Sanarwa
Masu Jawabi: Akwai Malamai da masana daban-daban da za su gabatar da lakca, ciki har da Jagoranmu, Sayyid Ibrahim Zakzaky (H)
Labarai cikin hotuna
Hotunan YAUMUL MAB'AS na bana