Almizan :Taron ’yan siyasar Kudu ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 22 Zulkidah, 1426                 Bugu na 697                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Babban Labarinmu

Taron ’yan siyasar Kudu

Ba za mu yarda mulki ya koma Arewa ba

Daga Musa Muhammad Awwal

Wani gagarumin taro da manyan kusoshin ’yan siyasa na yankin Kudancin kasar nan suka gabatar a garin Enugu a karshen mako ya tabbatar da cewa ba za su amince shugabancin kasar nan ya sake dawowa Arewacin kasar nan ba.


.

Wannan yana kunshe ne a wata takardar sakamakon bayan taro wacce Gwamnan jihar Akwa Ibom, Ogbon Victor Attah ya karanta wa manema labarai a karshen bayan taron nasu.

Taron, ya ce, “ganin cewa yankin Arewacin kasar nan ya yi shugabanci har na tsawon shekara 35, wajibi ne shugabancin kasar nan a shekarar 2007 ya kasance daga yankin Kudu maso Kudu, wanda bai taba shugabantar kasar nan ba. Ko kuma a ba yankin Kudu maso Gabas, wanda ya mulki kasar nan ne na tsawon watanni shida kawai.”

Shi dai wannan babban taron ya hada da Gwamnonin yankin, ’yan Majalisun jihohi da na Tarayya, Ministoci, Sarakunan gargajiya da kuma shugabannin siyasa da ke yankin.

Daga nan sai suka tabbatar da cewa kuma wajibi ne a ci gaba da batun da ake yi na sake duba tsarin mulkin kasar nan wanda ake kai a yanzu, kuma dole ne a kammala shi kafin nan da zaben 2007, wanda in ba a yi haka ba, to za su kauracewa zaben da za a yi a shekarar.

Taron, ya kuma nuna cewa kowane yanki ya rike arzikinsa don bunkasa yankinsa kamar yadda aka amince, in ba haka ba yankin zai hana a ci gaba da dibar arzikin da ke yankin nasa.

Saboda haka wannan matsaya tasu ta tabbatar da cewa su ba sa goyon bayan Obasanjo ya zarce a 2007, kuma suna adawa da dawowar mulkin zuwa Arewa, abin da suke bukata shi ne cewa wajibi ne a bar yankin Kudu maso Kudu shi ma ya dana, kamar yadda suka ce, shi ne yanki a kasar nan da bai taba shugabantarta ba.

A wata sabuwa kuma, wata wasika daga daya daga cikin jigi-jigan jam’iyyar PDP, kuma Shugaban kwamitin amintattu, Cif Tony Anenih ta tabbatar da cewa an yi yarjejeniyar cewa shugabancin kasar nan zai koma Arewa bayan Obasanjo ya kammala mulkinsa a 2007.

Wannan tsohuwar wasikar, wacce aka ci karo da ita, ya aika wa Shugaban jam’iyyar na lokacin ne, wato Cif Audu Ogbeh mai dauke da kwanan wata 5 ga watan Agustan 2002, inda ya nuna cewa wajibi ne a 2007 a bi ka’idar da aka tsai da na komawa da mulki Arewa.

Wasikar, wacce Cif Tony Anenih ya aika wa dukkanin shugabannin jam’iyyar PDP, ya gargade su da su tsare batun karba-karba don kare yiwuwar wargajerwar jam’iyyar. “Kamar yadda jam’iyyar ta bi tsarin shiyya-shiyya a zaben 1998/1999, akwai bukatar ta bi wannan ka’idar sau da kafa a zaben 2007.

Abin da jama’a ke ta korafi a kai shi ne cewa, ko me ya sa shi Tony Anenih yake neman karyata waccan yarjejeniya a yanzu?

Sannan kuma shi kansa Cif Obasanjo, a babban taron jam’iyyar PDP din da aka gabatar a kwanakin baya a Abuja, ya furta batun cewa babu shirin mayar da mulki zuwa Arewa a tsarin jam’iyyar.

A halin da ake ciki dai ana ta yawun baki ne tsakanin Kudancin kasar nan da Arewacin kasar, inda su Kudancin ke cewa dole su ci gaba da shugabancin kasar nan, sannan su kuma Arewacin kasar nan suna cewa wajibi ne shugabancin ya dawo Arewa kamar yadda aka yi yarjejeniya a baya.

In dai ba a manta ba Sanatoci, ’yan Majalisar Wakilai ta Taraayya da duk wani mai fada-a-ji a Arewacin kasar nan, sun yi taro a Kaduna, inda suke tabbatar da cewa, 2007 shekara ce da ya zama wajibi shugabancin kasar nan ya dawo Arewa.

Ganin fuskokin wasu mutane da ake masu kallon ’yan amintattun Obasanjo ne da suka hada da Cif Tony Anenih, Kema Chikwe, Ojo Maduekwe, Cif Femi Fani-Kayode da Mista Frank Nweke (jnr) ne a wajen taron na Enugu, ya sa jama’a da dama da ma a Arewacin Nijeriya, ciki har da Shugaban ACF, Cif Sunday Awoniyi da Alhaji Gambo Jimeta, Shugaban sabuwar kungiyar MDD/MRD suke ganin an shirya ne don a kada wa Obasanjo kugen ta-zarce. Suka ce abubuwan da taron ya cimmawa babu mamaki, “domin dama abin da muka zata za su fitar kenan.”

Sai dai kuma a wani abu mai kama da kare kai, fadar Shugaban kasa ta fito fili ta bayyana cewa babu shirin cewa wannan gwamnatin na shirin zarcewa a 2007.

…An yi yarjejeniyyar dawo da shi

In ji Audu Ogbeh

Daga Musa Muhammad Awwal

An bayyana cewa akwai kwakkwarar yarjeniyar dawo da mulki zuwa Arewacin kasar nan a shekarar 2007 a wani zama da shugabannin jam’iyyar PDP suka yi a 1999 da kuma 2002 cewa ’yan Arewa su yi hakuri ’yan Kudu su shugabanci kasar nan har na tsawon shekara takwas, daga nan mulkin ya dawo hannunsu.

Tsohon Shugaban PDP na kasa, Mista Audu Innocent Ogbeh ne ya tabbatar da wannan yarjejeniyar a lokacin da yake gabatar da jawabi a matsayin babban bako mai jawabi a taron da ‘Arewa Media Forum’ ta gabatar a Kaduna ranar Asabar da ta gabata.

Mista Ogbeh ya kara tabbatar da cewa duk da yake an yi kuskure ba a yi wannan yarjejeniya a rubuce ba, amma mutum 47 na kusoshin PDP da ke a wancan taro sun amince da wannan yarjejeniya na dawo da mulki a Arewa bayan shekara takwas, mutum biyu ne kawai suka hau kujerar na ki, wato 47 da 2.

Daga nan ne sai tsohon Shugaban ya ce; “sai ga shi yau abin mamaki muna jin wata sabuwar magana abin da ba a tattauna a wancan taron ba, wani mutum yana son ya canza waccan yarjejeniyar da aka gabatar. Muna jin ana cewa ba za a yarda mulki ya dawo Arewa ba. Wannan abin mamaki ne.”

Mista Ogbeh daga nan sai ya jaddada cewa su a matsayinsu na ’yan Arewa ba za su amince da duk wata dabara da za a fito da ita don a kauce wa waccan yarjejeniyar ba. Domin a cewarsa, ya lura cewa wannan gyaran da aka neman a yi wa tsarin mulkin kasar nan, ba wani abu ake so a yi ba illa a sama wa Obasanjo mafita na ya zarce a 2007. “Ba za mu taba amincewa da wannan ba sam, don ba haka aka yi a yarjejeniyar ba,” ya ce.

Daga nan ne sai tsohon Shugaban ya nuna takaicinsa na ganin yadda a wannan mulkin aka mayar da yankin na Arewa saniyar ware ta yadda har tattalin arzikinta yana neman ya karye, domin yanzu masana’atu da manyan tashoshin bayar da wutar lantarki duk an tara su ne a Kudu, baya ga ’yan kudade kalilan da ake bai wa jihohin Arewa daga arzikin kasar.

Audu Ogbeh ya ce, wadannan take-take na Obasanjo ba abin da za su haddasa sai fitina wacce ba a san yadda za ta kare ba. Ya ce kuma in kasar nan ta yamutse, to ina za a je gudun hijira, “Nijar ko Chadi, wadanda su ma suna fama da kansu?” in ji shi.

Tsohon Shugaban bai kau da kai game da ayyukan da gwamnatin ta aiwatar na alheri ba, inda ya yaba mata matuka. Sai dai ya yi gargadi gare ta da ta yi abin da ya dace a 2007, kada ta yi abin da zai haddasa fitinar da za ta lalata ayyukan alherin da ta yi.

Shi ma daya tsohon Shugaban PDP din na kasa, Cif Solomon Lar irin wadannan kalaman ya yi.

Shi kuwa Dakta Olusola Saraki, kira ya yi ga ’yan Arewa da su hada kai domin dumfarar wannan kulen da ke gabansu, inda ya nuna cewa in ba a hada kai ba, to ba za a sami nasara ba.

Ya ce shi ya san ’yan Arewa ba sa son rigima, kuma ba sa yin rigima a duk lokacin da suke neman wani hakki nasu, amma ya ce wajibi ne a wannan karon ’yan Arewa su tashi su kwato ’yancinsu ta kowane hali.

Shi kuwa Tsohon Ministan Sufuri a zamani mulkin Shehu Shagari, Alhaji Umaru Dikko takaicinsa ya nuna game da yadda ake nuna wa Arewa son kai a fili wajen rabon arzikin kasar nan.

Ya ce, “abin mamaki sai ka ga an ba jiha daya ta Kudu kason kudi Naira biliyan 10, amma jiha daya a Arewa sai a ba ta Naira biliyar 1.5 ko 2. Jiha daya a Kudu tana karbar kusan duk kason da ake bai wa jihohin Arewa. Sam ba a yin adalci a rabon arzikin kasar nan,” Umar Dikko ya koka.

Cif Sunday Awoniyi, Shugaban Kungiyar tuntuba ta Arewa, ACF, cewa ya yi, wannan taro na kwanan nan da ya gabata na sake duba tsarin mulki, Obasanjo ya shirya shi ne don ya hada rikici a Arewa; “ya so ne ya tunzura ’yan Arewa su fice daga taron domin ya samu ya aiwatar da abin da ya so, in an yi magana sai ya ce ai sun fice daga taron ne, amma sai ’yan Arewa da ke taron suka ki ficewa. “Na gode maku da ba ku fice ba. Allah ya saka maku da alheri,” ya ce.

Cif Awoniyi ya ce, ko a zaben 2003 ai Obasanjo bai ci zabe ba, amfani kawai ya yi da ’yan sanda da sauran kayan gwamnati ya ba kansa shugabanci.

Shugaban na ACF ya ci gaba da cewa, mulkin Obasanjo bala’i ne ga ’yan Nijeriya. Ya ce saboda bala’in da ke cikin wannan mulki nasa ne ya sa ake ta samun bala’o’i kala-kala, hadarin jiragen sama da sauran hadurra.

Saboda haka sai ya yi kira da cewa wajibi ne ga duk wani dan Arewa da duk wani mai yi wa kasar nan fatan alheri, a yi duk abin da za a yi don ganin an taka wa Obasanjo burki a 2007.

A karshe ya yi kira da cewa wajibi ne a ci gaba da shirya zanga-zangar lumana da tarurruka don wayar wa da jama’a kai na ganin Obasanjo bai zarce a 2007 ba.

Shi kuwa Janar Buhari cewa ya yi, su Audu Ogbeh sun yi kuskure tun farko da ba su yi wacen yarjejeniya a rubuce ba. Ya ce, amma duk da babu ita a rubuce, ai wadanda aka yi a gabansu suna nan a raye, don haka dole a bi.

Ya ce wajibi ne a yi abin da zai zaunar da kasar lafiya wajen bin tsarin mulki yadda ya tanada.

Shugaban wannan Kungiya ta ‘Arewa Media Forum,’ Malam Muhammad Haruna cewa ya yi, sun shirya wannan taro ne don wayar wa da jama’a kai a harkar da ta shafi sha’anin siyasar kasar da makomar Arewa a wannan tsari na dimokradiyya da ake ciki.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International