Almizan :Hanyoyin da Harka Islamiyya za ta sami kudi (2) ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 22 Zulkidah, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Tunatarwa:Tare da Shaikh Ibrahim Zakzaky

Hanyoyin da Harka Islamiyya za ta sami kudi (2)

SHAIKH ZAKZAKY
Malam Ibraheem Yaqoub Zakzaky H.

Mai karatu wannan ci gaba ne na jawabin da muka soma kawo maku a makon da ya gabata, wanda Malam Ibraheem Zakzaky (H) ya gabatar wajen rufe taron kara wa juna sani na kwana biyu, wanda ’yan uwa na ‘Resouce Forum’ suka gabatar a Fudiyya Islamic Centre Zariya. Musa Muhammad Awwal ne ya rubuto mana daga kaset. A sha karatu lafiya. Mai karatu wannan ci gaba ne na jawabin da muka soma kawo maku a makon da ya gabata, wanda Malam Ibraheem Zakzaky (H) ya gabatar wajen rufe taron kara wa juna sani na kwana biyu, wanda ’yan uwa na ‘Resouce Forum’ suka gabatar a Fudiyya Islamic Centre Zariya. Musa Muhammad Awwal ne ya rubuto mana daga kaset. A sha karatu lafiya.

Har ma manoma masu dukawa su yi aiki sosai a kauyuka, su ma suna sayar da mai. In ka ga mutane a gefen titi suna aiki a gona, in motarka ba mai ka tsaya ka ce barkan ku da aiki, akwai bayani? Za su ce akwai. Za a ce “Saleh dauke shi ku zagaya ta can.” Suna nan da mai a gona din. Kusan kowa yana sai da mai ne a kasar.

Sai ya zama sayar dai mai din ya koma kamar siyasa din. Sai ya zama ya tashi a ‘Business’ din ciniki ya zama irin kumbiya-kumbiya, irin yadda ake yi a salon siyasa. Ta haka nan sai ya zama ko da wani abu ne ma, in ake shige shi sai ya zama an maishe shi haka nan. Amma duk da haka dai ba za ka rasa ’yan wadansu abubuwa da ake iya zuba dan jari ba ko yaya, ko da ma irin sha yanzu magani yanzu ne. Na san Malam Abdullahi Hafiz ba irin wannan zai gaya maku ba. Zai fadi irin ba ni sha yanzu magani yanzu bane ko? Don shi ne mutane yanzu suka fi ganewa.

Kawai su tattara kudadensu, muna-muna, su kama haya su tafi Dubai ko Kwatano, in kwatano suka je su debo tsofaffin motoci. Yanzu tsofaffin komai ma ana sayarwa yanzu. Ana sayar da tsohon Firij, ko shi ma? Tsohon komai ma in zai iya samuwa, su kwaso su sassayar, shi kenan sai a sami riba. Wani lokaci kuma in tana iya daurowa a kwace kayan ko a kwace kudin. Haka kuma wadanda za su kama hanya su ma su je Dubai su kwaso tarkace su zo su sayar. Amma nan an yi magana a kan ‘Organised business’ ne ko? To Allah ya ba da sa’a.

Nakan dan sha mamakin cewa wadansu ba ‘Organised Business’ ne ba, sun dai yi kama ne. Kamar wanda shago ne mutum zai yi, ya dan sa allon sanarwa (signboard), ya ce ko ‘And Sons’ ko wani abu ‘Limited’; ba ma ‘Limited’ ne ba, Ventures, wani abu dai ga su nan dai. Sai ka ga su mutanenmu ba su iya yi ba.

Su dai ka bar su dai, in ka ga an sa ‘Okafor Chemist,’ to za ka ga da wani yana sayar da kaji suna kuyat-kuyat, to Saleh kenan. In can kuma ka ji an ce ‘Adebayo Photos,’ to za ka ga mai sayar da tumatur da albasa, to Tanko ne, shi kuma a kusa da shi. Su kuma irin wannan ne mutanenmu suka iya.

To ina ganin ko da ma irin ’yan wadannan din ne, ko da irin wadannan ’yan kananan abubuwa din, ba ma kananan ‘Ventures’ din ba kila, don su ma suna karyewa, don ya danganta da yadda za ka dinga lura da yanayin rayuwar mutane take ne, me yanzu aka raja’a ma? In an yi masa yawa, ya raguje, sai a koma wani. Haka kusan yanzu ake yi.

Kusan abin da nake kokarin in ce shi ne lalacewar tattalin arzikin kasa (economy) shi ya shafe mu. Shi ya sa kuma ayyuka (Projects) da yawa da muka sha hankoran mu yi, sai mu kasa yi. Wani lokaci da dadewa mun taba sawa aka yi bincike (feasability study) na Sakandare da dawainiyar da za mu dauka, za mu dauki gidaje biyu na haya, daya ya zama azuzuwa, daya ya zama wurin kwana (Hostel). Za a biya kaza, har an ma sami gidajen. Kuma aka yi kiyasin (estimating) albashin malamai a shekara da abincin dalibai da bukatar gudanar da makaranta da sauransu. Aka yi dan lissafi, lokacin kudin zai isa. Amma (by the time) da aka tattara kudin, sai ya zama wannan kudin ba zai iya yin wannan aikin ba kuma. Sai ya zama kawai ya bi ruwa. Ina jin wajen shekara 15 kenan ko? Da aka tattara kudin sai ya zama ba zai yi ba, muka yi hobbasa lokacin aka ce kowa ya kawo Naira dari-dari, lokacin Naira dari kudi ne.

Da aka tattara Naira dari-dari din, sai muka sami wajen dubu 15. Sai ya zama lokacin da za mu fara aikin, to ana bukatar kudin zai nunka haka nan sau uku. Sai ya zama ya wargaje. Kusan kuma yanzu kusan ma din dai haka din ne. Amma duk da haka kuma ban san ranar mafita ba saboda kasar dada lalacewa take yi. Kuma lalacewar yana gudu ne ba kadan ba. Amma a ce a haka nan kasar take din, kuma a haka ne mutane ke rayuwa.

Ko ba komai dai, alhamdulillah muna da kasar noma, kuma Allah (T) yana saukar da ruwa isasshe, kuma saboda haka nan ana samun abinci. Don haka mutane sunan suna rayuwa ba a fara watsewa ba. Amma kwararru kam suna ta arcewa, suna ta zubawa a guje suna barin kasar.

Na sha mamaki, ina kallo a talabijin a ‘South African TV’ suna bayani dangane da asarar (loses din) tiransifan kudi (Transfer of Payment) daga ’yan kasa da suke aiki a waje. Sai suka nuna ’yan Ghana da suke aiki a kasashen wajen suna yiwo tiransifa (transfer) din kudi zuwa gida. Har suka nuna yana jawo (Accounting for), ko nawa ne GP? Sun fadi ko wajen dala dubu 60 ne, shi wannan kudin yana jawo wajen dala biliyan 24; wani abu mai kama da haka nan.

To sai suka yi wani nazari (case Study) game da wata mata wadda ina jin danta ne ya rasu ya bar mata jikoki da yawa. To duk sai ta yi kokara ta koyar da su karatu dai, yanzu duk suna waje. Jikokin nata suna da yawa, amma wasu suna Turai (Europe) ne wasu suna Amerika. Kuma duk wata sai aka nuna yadda suke dan tunkudo kudade. Sai a nuna ta je ta karba a banki. Akwai wani daya jikan da ya zauna tare da ita sai ya karbo.

Nazari (Case Study) sosai suka yi. Sun nuna hoto, ga yadda yake karbo kudin. Shi jika daya yake tare da ita, sauran jikokin nata kamar guda 8 suna waje. To shi ke lura da harkkokin (Managing). In ta karbi kudin kuma sai ta je ta sassayo yadudduka a tuttura, a duddunka, ta shiga juyawa. Haka dai abubuwa suna tafiya lafiya lau.

To, sai na ji ana hira da wani Bature a London yake cewa, ’yan Ghana suna da yawan gaske a nan London, akwai lauyoyi, akwai Likitoci, akwai Injiniyoyi, kwararru dai, watakila ma Ghana ita ce kawai kasar da kwararrunta (Professionals) dinta a waje sun fi na cikin kasarta yawa. Sai na ce na dauka Nijeriya sun fi ai.

Domin kwararrun Nijeriya lallai sun fi yawa a waje fiye da a gidan. Don akwai wani lokaci da na karanta a wani wuri ake cewa a Amerika kawai akwai Farfesoshi 50,000 ya ce ’yan Nijeriya da suke koyarwa a can. To galiba wasu na rayuwarsu ne kawai su yi zamansu a can, ba rawansu da wani abu.

To ina ganin kila ma da irin wannan ne ma, za a fara dan tserewa din a rinka fita ana ingizo kudade. Don ko da ma wadanda tattalin arzikinsu ke da karfi suna yin wani abu mai kama da haka nan. Kamar ’yan Lebanon, ba laifi da kasar, amma duk ’yan Lebanon sun watsu a duniya ko’ina suna ‘business’ suna aikowa da kudade. Har ma akwai lokacin da aka taba kama wasu ’yan Lebanon a Amerika (USA), aka ce wadannan mutanen ba su yi laifi ba, amma dai an san cewa suna aikawa da Hizbullahi kudi ne. Su suna sayar da taba ne. Ba su shan taba din, amma tunda Ba’amerike yana sha, kuma da riba, sai su sayar masa da taba din ya zuzzuka abinsa, su tura ribar gida, a sami na gwagwarmaya.

To shi ne, irinsu ne aka kama aka ce an lura cewa ribar taba din suna aika wa Hizbullahi ne. Kodayake, kamar yadda suka ce, kuma ba su yi laifi ba, tunda bisa doka (legally) suke aikinsu, kuma ‘Transfer’ din kudin shi ma bisa doka ne tunda za aika gida ne. Amma dai su abin da suke tunani shi ne ya za su yi su gurgunta wannan? Wanda kuma yake ba yadda za su yi da irin wannan.

To kila irin wannan ne, yanzu wannan shi ke dan kankaro wadansu wurare da yawan gaske haka. Don ba an dinga zama a haka nan bane. Ko Ghana din ma da tattalin arzikin nata ya fara canzawa, da dai ita ma ai lalacewar nata ya yi kama da na Nijeriya. Kodayake bai kai na Nijeriya (lalacewa) ba. Na Nijeriya kam matsala (Case) ce da babu irinta duk duniyar nan.

A takaice dai abin da na so, kila su Malam Abdullahi sun riga sun yi bayani yadda ya kamata, kila a tattara ‘Resources’ ko? Yadda ya kamata a shigar da yadda ya kamata a yi aiki.

To, ni kila da abin da ya kamata in ce, in kyale ku da wadannan, yadda za a yi wadannan din. Ni in fadi ayyukan da za a yi in san sami kudin. To amma na san ba kudin. Ga ayyuka da yawa wadanda ya kamata, su kuma wadannan ba masu kawo kudi bane sam-sam-sam, wanda za a kashe kudi ne, wanda kuma wani lokaci na yi magana da ’yan ‘Resource Forum’ da aka fadi wadansu nasarori (Achievement) da aka yi, aka ce an sa shafi (site) a intanet, an yi mene, an yi mene. Sai na ce, to ina fata in an zo badi kuma za a fadi cikin nasarorin a ce kuma ga shi nan an yi jarida ta Ingilishi, kuma ga shi nan an sa tasha (Channel) a Satalayit. Ban san ko ina aka kai ga batun jarida da tasha (channel) ba. Jarida kila an tattauna. Amma yanzu kwarai-kwarai, akwai bukatar tasha, Canaloli din. Don yanzu mutum in yana duba satalayit, yana ganin Canaloli barkataitayi, ga su nan iri-iri. Har da wadansu kungiyoyi ’yan kanana; sai mutum ya sha mamakin cewa ni ban ga dalilin da zai sa ba za a iya yin tasha (Channel) din ba.

Saboda wadansu na da Canaloli da yawan gaske, kuma ina tsammanin abin yana da dan sauki. Lallai mu zai dan yi mana wahala, amma ya kamata shi ma mu yi wani hobbasa. Alal misali kar mu dauka kawai mu rinka kallon Canaloli din mu dauka wani kayan gabas ne.

Don akwai wani da yake da Channel, mutum daya ne, kirista ne, yana wa’azin kirista, kodayake yana warkar da mutane, yana ‘miracle’. To yana da ‘Channel’. To sai wani yake ce mani ba kuma wadansu kayan aiki (gadgets) ne masu yawan gaske ba. Kamarori yake da shi da wadansu ’yan mashin. Na ce ai dama kayan ‘Transimission’ bai wuce a sa su a mota ba. Kuma za a iya watsawa (Transmission), har ma kai tsaye (live) da shi. Bai wuce a sa shi a mota ba.

Za mu ci gaba insha Allah.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International