Almizan : A Takaice kai Tsaye: Na M.M Awwal, Ta GSM,0803 451 4693 ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 24 Shawwal, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
A Takaice kai Tsaye: Na M.M Awwal, Ta GSM,0803 451 4693

OBASANJO ALLAH YA SO MU

Kudin talakawan Nijeriya da ’yan kwallon kafa na Super Eagles za su tafi su kashe a Jamus ba tare da yin abin kirki ba, to sai ga shi Allah ya sa ba za su je ba. To sai a fito mana da su a saya mana magungunan a asibitocinmu da takin zamani, da kuma fatan Allah ya yi ta maimaita mana haka daga nan har zuwa illah masha Allahu.

Daga 0802 310 4109

ALMIZAN ALLAH SAKA DA ALHAIRI

Assalamu alaikum. ALMIZAN Allah ya saka da alhairi, domin yanzu kowane mako muna samun ALMIZAN a Yola.

Daga Abubakar A.M.B Yola 0802 672 1893

DANGOTE KA ZIYARCI DANGOTE CEMENT

Assalamu alaikum. Alhaji Aliko Dangote ya kamata ka ziyarci ‘Dangote Cement’ da ke NPA na Fatakwal, idonka ya nuna maka irin cuwa-cuwar da ake yi.

Daga Muhammad Bello Maiduniya Lafiya 0806 245 0055

RANAR TALAUCI A DUNIYA

Ranar 17/10/2005, za mu iya kiran ta da sunan ranar PDP, don Majalisar danne talakawan duniya ta kira ta da ranar abinci ta duniya. Amma a Nijeriya PDP ce ta talauta mu, don ita ce ta saka mu cikin talaucin da ba mu taba gani ba. Saboda haka daga yau har zuwa karshen mulkin PDP a duk lokacin da wannan rana ta zagayo, za mu kira ta da ranar PDP ta duniya, don ita ce ta saka mu a talaucin da muke ciki.

Daga 0802 310 4109

KOBON WUSHISHI KA YI RAWAR GANI, AMMA…..

Assalamu alaikum. Kobon Wushishi ka yi rawar gani da ka gayyaci Shaikh Dahiru Bauci don bude masallacin da ka gina a gidanka fisabilillahi, haka ake so masu kudi su rinka yi. To sai dai ina kira gare ka da ka rinka tausaya wa talakawa masu haya a gidajenka. Ta haka ma za ka zama mai taimakon jama’a na gaskiya.

Daga Muhammad Ali Kademi, Kaduna. 0804 494 2398

TAKEN TAFSIRIN BANA

Taken tafsirin bana; “raba kan musulmi.” Allah wadaran naka ya lalace.

Daga Ummar Abbas Buhari No.18 Gidan Dogo, Unguwar Bishar, Zariya. 0803 587 6715

IZALA ADDINI CE?

Assalamu alaikum. Zuwa ga ma’aikatan ALMIZAN, ra’ayi na shi ne, kai mai cewa Izala ce jirgin tsira, to Izala addini ce? Ka yi addini shi ya fi maka.

Daga Sabo Laji, Bididan. 0803 364 8598

MALAMAI A YI KOYI DA MALAM ZAKZAKY

Assalamu alaikum. Ina so in yi kira ga Malaman Izala da Darika masu tafsiri cewa su yi koyi da Shaikh Ibraheem Zakzaky a wajen tafsirinsu. A rinka karanta aya ana fassarawa, tare da yin bayanai masu amfani ba tare da batanci ga wani musulmi ba. Su kuma ’yan Shabbabu masu neman fada da musulmi, su sani yanzu zamani ne na fada da kafirci ba Musulunci ba.

Daga Musa Aminu Kurerya.

SAKONA GA MALAMAN NIJERIYA

Sakona ga Malaman Nijeriya shi ne cewa ba batanci ga Shi’a ne sauke nauyin da ke kanku ba. Ku yi wa gwamnati wa’azi ta wadata al’umma da abinci, ruwan sha da sauransu.

Daga 0802 469 3262

MUTUWAR STELLA OBASANJO

Ta rasu a Spain wai ta je kwaskwarimar jikinta. Dole ta je kwaskwarima mana tunda suna danne dukiyar talakawa.

Daga Bala Ahmad Mariri Lere LG 0803 601 5040

RIBADO KA KAWO ZIYAR GOMBE

Nuhu Rabado ya kamata ka kawo ziyara a jihar Gombe don a bai wa talakawa hakkinsu. Kwangilolin wuru-wuru da ake yi na jawo koma baya a jihar baki daya.

Daga Musa Dadin Kowa Gombe 0802 574 3265

YAZIDU YA KA SA GAMAWA DA SHI’A

Haba Babayo Musa ina son ka sani cewa zancen Izalatul Shi’a, su Yazidu ma sun yi ba su yi nasara ba.

Daga Murtala Salihu Kano 0802 692 5682

LA’ILAHA ILLALLAH AKA SA BA SHI’A BA

Ya kamata Malam Babayo Musa ya gane cewa Hakeem Raji fa, La’ilaha illallah ya ce, ba wai Sha’a ba a jikin jirgin tsiran da ya yi, kuma ita muke so Allah ya tabbatar da mu a kanta ba wata kungiya, ko wata mazahaba ba.

Daga Yusuf Ibn Musa Markaz Bauci Motar Park Jos 0803 593 6498

A JIRGIN SAMA MA BA A TSIRA BA!

To masu gudun shiga mota suna hawa jirgin sama saboda munin hanyoyi, ko gudun ’yan fashi, to saman ma ga yadda ta zama. An guduje wa mutuwa, an fada kabari. Saman da kasan duk a Nijeriya daya ne, domin barayi da gafiyoyi su ke rike da madafu a kasar nan. Sai dai mu roki kariya a wajen Allah.

Daga Idris A. Bajoga. 0806 526 9509

JAMA’A MU HADA KAI

Jama’a a shirya a hada kai kafin Amerikawa su zo.

Daga Adamu Azare 0806 526 9883

SHEKARAU A YI HATTARA

Gwamna Ibrahim Shekarau ka yi taka-tsantsan da wadanda ba sa son zaman lafiya a Kano kada su zuga ka. Domin da yawansu ba ma ’yan Kanon bane, balle ma su damu da zaman lafiyarta. Da zarar wani abu ya taso tserewa za su yi su bar ka. Allah ya la’anci masu ta da fitina. Allah ya sa ku gane, amin.

Daga Haruna M. Haruna Kano 0803 687 5702

’YAN UWA MU DAGE DA ADDU’A

Assalamu Alaikum. Ina kira ga ’yan uwa musulmi mu tashi tsaye da addu’a.

Daga 0803 788 5899

A INA KA SAMO WANNAN?

Assalamu Alaikum. Malam Babayo a ina ka samo cewa wasan kwallo ko buga labarinsa haramun ne a Musulunci?

Daga 0803 469 0159

’YANTO KUDUS WAJIBI NE

’Yan uwa mu sani fa cewa ’yanto Masjidul Aksa shi ne ’yanto duk masallatai. Kasancewarsa a hannun Yahudu shi ke nuna cewa sauran ma su ke rike da su.

Daga 0806 548 2850

MU CIRE HASSADA MU BI GASKIYA

Assalamu Alaikum. ’Yan Nijeriya ya kamata mu kawar da hassada mu binciki wasiyyar Danfodiyo na zuwan Mujaddadin wannan karnin, ko ma sami mafita daga halin da makiya Allah suka sa mu a ciki. Wassalam.

Daga Shehu Maraban Jos jihar Kaduna 0806 561 8170

ALLAH YA CIKA WA SHUGABAN IRAN BURINSA

Allah ya cika wa Shugaban kasar Iran, Dakta Ahmadinajad burinsa, mu wayi gari mu ga an shafe kasar Isra’ila daga bayan kasa.

Daga S. Ahmad FGGC Minjibir Kano 0804 546 8310

ALLAH YA JA ZAMANIN IRAN

Assalamu Alaikum. Dakta Ahmadinajad ka burge ni. Allah ya ja zamanin Jamhuriyyar Musulunci ta Iran.

Daga Sagiru Mai Kayan Karfe Suleja 0804 343 4275

HADIN KAN MUSULMI NE MAFITA

Assalamu Alaikum. Malamai ku yi hattara kada ya zama kuna yi wa Yahudawa aiki. Don na ga ba ku da abokin fada sai musulmi dan uwanku. Ku ce wane ba daidai yake ba, ku ke daidai. Ko wani ba musulmi bane, kune musulmi, saboda bambancin fahimta, don ba a rabu a kan tushe ba, kai ko a kan rassa ba a rabu ba. Ku nemi hadin kan musulmi shi ne mafita.

Daga Mas’ud Mai Sabo, Katsina 0802 559 4697

MALAM SHEKARAU A YI A HANKALI DAI

Ina so in sanar da Gwamnan Kano cewa, muna sane game da ziyarar da ya kai ga Shugaban Amurka Bush a kan fada da ta’addanci, wato fada da Musulunci. To ka yi a hankali dai, domin kafin ka yi, wasu sun yi ba ta yi masu da kyau ba. Idan kuma ka ki ji, to……

Daga Abu Ubaida, Kazaure jihar Jigawa 0804 497 5313

DAN MAJALISA KA BURGE NI

Dan Majalisa mai wakiltar Bosso da Paiko cikin Jihar Neja, ka yi wa Unguwar Kanawa alkawari ka cika masu, sai maganar ta-zarce kawai!

Daga Bashir Duna da Bashir Ustaz Unguwar Kanawa Bosso, Minna jihar Neja 0802 787 1944

ALLAH YA KARE MANA SHUGABAN IRAN

Allah ya kare mana Shugaban kasar Iran da ire-iren su, domin su kadai ne za su yi maganin annobar duniya, har su sa Amurka da Isra’ila su firgita.

Daga Kaita 0802 572 1317

GA MAGANIN ISRA’ILA

Assalamu Alaikum. Musulmi mu taya Dakta Ahmadinajad addu’a domin kuwa shi ne maganin Yahudu. Malam Zakzaky kuma maganin azzaluman Nijeriya.

Daga Yusuf Isma’ila 0803 689 3831

MU GA JIRGIN TSIRANMU

Babayo Musa Jos ka sani mu Kano ba a yayin Izala; daga Darika sai Shi’a. Kuma ka sani mu jirgin tsirarmu sune Muhammad (SAW), Aliyu, Fatima, Hasan da Husaini (AS). Kai kuwa ka je Izalarka ta cece ka.

Daga Ado NEPA, Kurna Kano. 0802 437 9973

KULENKU MALAMAN NIJERIYA!

Kulenku Malaman Nijeriya! Malam Zakzaky ya ce babu gwamnati sai ta Allah. Alkur’ani da Sunnar Manzon Allah kadai su ya kamata su yi iko da musulmi, amma ku kuma ba ku yarda da shi ba, kun ce Shi’a ce. Amma ku kuma kun ce a bi fajiran shugabani, a yi siyasar kafirci.

Daga Muhammad Kofar Guga Katsina. 0803 692 0810

AKWAI GYARA A FUNTUWA

In har makarantar share fagen shiga Jami’ar ABU (SBRS) da ke Funtuwa don ’yan Arewa aka yi ta, to akwai gyara kuwa.

Daga Buhari Umar Abbas, Fidan Dogo Unguwar Bishar, Zariya. 08033607068

AKWAI KUNGIYAR ALKA’IDA KUWA?

Wai don Allah da gaske ne akwai kungiyar Alka’ida kuwa? Kuma wai da gaske ne su ke kai hare-hare a Iraki? Idan haka ne, to wa suke yaka? ’Yan mamaya ko mutanen Iraki? Idan har akwai su kenan. Idan kuma su ke tayar da bama-bamai a Iraki, to Musulunci suke yi wa aiki, ko Amurka da Yahudawa? Allah ya tona asirin mabarnata, ya gaggauta kawo karshensu, amin.

Daga Bilyaminu Kiru. 0802 309 7766, 0806 566 6555

ALMIZAN TA WUCE MATSAYIN JARIDA A YANZU

Yanzu ALMIZAN ta wuce matsayin jarida, sai dai mu dauke ta a matsayin wani kundi mai kunshe da fannonin ilmomi, wanda ke fitowa kowace Juma’a. Buda ta mana ka gani.

Daga Amiru Mu’azu Muhammad Funtuwa jihar Katsaina (profnomagic@yahoo.com)

’YAN FIM DIN HAUSA HAKA AKE YIN WA’AZI?

Suna lalata addini, suna gurbata al’adummu masu kyau wai da sunan ci gaba, ko kuma ka ji an ce wai wa’azantarwa suke yi. Babu abin da ya fi ba ni haushi dangane da al’amarin masu shirya fimafiman Hausa sai cewa da suke yi wai su masu wa’azi ne. Haba Malam haka ake wa’azi, yarinya budurwa ta fito da ’yar matsattsiyar riga duk sifofin jikinta sun bayyana da dan karamin buje tana tikar rawa tsakanin baligai maza, ba kunya ba tsoran Allah, sannan a ce wai tarbiyya ake koyarwa? Wace irin tarbiyya ake koyarwa kenan? Sai dai tarbiyya irin ta Yammacin duniya, amma ba dai tarbiyyar Musulunci ba. Don haka a gaskiya ni kam ina adawa da irin wadannan fimafiman muddin ba gyara aka yi ba aka maido da martabar addininmu da kyawawan al’adummu na Hausa ba.

Daga Hamza M Djibo Jamhuriya Nijar (djibohamza@yahoo.fr)

NASIHA GA MA’ABOTA TSARIN KAFIRCI

Wannan nasiha ce ga dimukuradiyyawa na su daina gwama ayoyin Alkur’ani, hadisan Manzo (SAW) da hayaniyarsu ta dimukradiyya. Abin da kuke yi a watannin nan, musamman a Kano, izgili ne! Idan addini za ku yi, to ku tafi Zariya ku yi mubaya’a, idan kuma na Amurkawa za ku yi, to, ku kyale mana Alkur’ani da hadisi.

Daga Awwal Sulaiman, G. Dutse, Kano (awwalusuleiman@yahoo.com)

KU DAWO MANA DA FILIN WASA KWAKWALWA

Assalamu alaikum. Don Allah Edita ina so ne na ba ku shawara, ya dace ku dawo mana da filin wasa kwakwalwa da kuke yi a wannan jaridar a da. Domin dawo da filin zai kara wa ’yan uwa da yawa ilimi. Ku huta lafiya.

Daga Mujahid Unguwar Azara Gwagwalada Abuja 0806 571 9146

ME KATSINAWA SUKA YI MAKU KUMA?

Assalami alaikum. ALMIZAN me Katsinawa suka yi maku kuma? Don na ga ba ku sa hotunan muzaharar Kudus da suka yi a cikin jerin hotunan muzaharar Kudus da kuka sa a bayan jaridar ALMZIAN ba.

Daga M. L. Z. 0802 741 9285

Malam M. L. Z. dalilai biyu ne suka hana mu sa hotunan na muzaharar Kudus ta Katsina a kan lokaci. Na farko ba su iso wurinmu a kan lokaci ba. Na biyu kuma lokacin da suka zo, sai muka samu matsala da injin da ke yi mana ‘sikanin.’ Amma da yake yanzu mun dan shawo kan matsalar, a wannan makon ga hotunan nan.

-Editan shafi

DAMA IZALA BA KUNGIYAR MUSULUNCI BACE?

Assalamu alaikum. Wai don Allah dama Izala ba kungiyar Musulunci bace, jam’iyya ce da ke kan godaben siyasar dimokradiyya, don na ji suna cewa 2007 sai Dan Izala.

Daga Dauda Mai Leda Kaduna 0803 287 3662

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International