Almizan :Kasar Iraki: Fagen jihadi ko dandalin wasan kwaikwayon siyasa (5)? ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 24 Shawwal, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Tattaunawa

Izala tana fada ne da rarrabuwar kan Musulmi

In ji Shaikh Husaini Zakariyya


Daga Aliyu Saleh

Bayan kammala taron yunkurin sulhunta kungiyar Izala da Dakta Ahmad Gumi ya kira ranar Juma’a 10-10-1426 (11-11-2005), wanda aka yi shi a asirce da nufin dinke barakar da ke cikin kungiyar, wadda ta jaza suke jifan junansu da kaulasan ne, ALIYU SALEH ya nemi ganawa da shi Daktan, amma saboda yadda jama’a suka yi masa yawa, sai ya hada shi da na hannun damansa, SHAIKH HUSAINI ZAKARIYYA don ya wakilce shi. Inda suka tattauna da shi kan taron da aka yi da kuma irin nasarorin da taron ya samu.

A gaban Wakilinmu a ranar Litinin din nan, Dakta Ahmad Gumi ya bar Nijeriya domin komawa kasar Saudiyya, inda yake karatu. An ce zai dawo bayan an yi hajji don ya ci gaba da aikin da ya faro na sasanta kungiyar da Mahaifinsa ne ya yi sandiyyar samuwarta a cikin rubu’in karni. Ga dai hirar kamar yadda take.

MATSAYINA A KUNGIYAR IZALA

Sunana Husaini Zakariyya. Muna cikin ’ya’ya ko in ce lokacin da aka haifi Izala muna kanana a wancan lokacin. Iyayenmu sune suka kafa kungiyar. Saboda haka, muna cikinta, kuma mun girma a cikinta, tamu ce, kuma muna fata har mu koma ga Allah (T) ba za mu kauce daga manufar da aka kafa ta ba. Shi ne tabbatar da Sunna da kuma kankare bidi’a.

ABUBUWAN DA MUKA TATTAUNA A TARON

A gaskiya ba kwanan nan Dakta Ahmad ya fara wannan yunkuri ba. Ya fara magana da Malaman kungiyar Izala na bangare daban-daban shekaru masu yawa, wato tsawon zamansa a Saudiyya. Amma abin bai dame shi sosai ba sai ’yan shekara biyu da suka wuce. Wanda yake bara bayan ya zo ya yi wa’azi ya fara tunanin cewa, lalle ya kamata a dinke barakar da ke tsakanin Izala.

Bai kamata a ce ’yan uwa suna fada tsakaninsu ba. Kuma an so a yi taron Malamai din gaba dayansu a Makka lokacin aikin hajjin bara, amma hakan bai samu ba. Domin daga cikin Malaman, akwai wadanda ba su samu tafiya ba. Amma duk da haka ya yi kokari ya sadu da Shaikh Sani Yahya Jingir a Mina lokacin Hajji, kuma ina wurin suka tattauna kan matakan da za a bi wajen dinke wannan baraka. Su ma (bangaren Jos) sun nuna cewa abin yana damunsu sosai. Kuma yana daga cikin burinsu, kuma yana daga cikin fatansu su bayar da gudummawa a dinke wannan baraka.

Ya bayar da matakai kamar guda biyar wadanda yake ganin in an bi su za a cimma nasara. Daga cikinsu akwai cewa, Malam Ahmad Gumi ya ziyarce su idan ya zo Nijeriya. Kuma an yi ta rubuce-rubucen wasiku tsakaninsu, kuma nine kusan masinjan da ke aikawa da wasikun. Wanda Malam ya aiko ni nake kai wa. Su kuma in sun rubuta, ni suke aika in kai masa, har Allah Ya kawo zuwansa.

Yana zuwa ajiye jakarsa ke da wuya, ya kira ni ya ce, in zo mu tafi Jos, don cika alkawari. Muka tafi aka yi sa’a lokacin suna babban taron shekara na bangarensu a Jos, muka zauna aka yi budewar farko da mu. Sannan cikin dare muka yi taro da su, muka tattauna matakai da matsalolin hadewar Izala. Kuma sun goyi bayan a hadu, amma akwai sharudda da suka kawo wadanda bangaren Kaduna za su yi.

Saboda haka da muka tashi washegari, ba mu tsaya ko’ina ba sai Sakkwato, domin su ma lokacin Izalar Kaduna suna nasu taron na shekara-shekara a Sakkwato. Muka je musu da wannan sako na mutanen Jos. Muka isar da abin da aka aiko mu, suka tashi suka fadi abin da ake so su fada, suka ce sun yarda su hadu gaba dayansu, kuma babu wani sharadi illa idan an hadu a ci gaba da aiki kamar yadda aka faro.

To, da muka dawo daga Sakkwato da sakon mutanen Kaduna, sai muka aika da kaset din bidiyon abin da muka tattauna da kaset na rikoda muka ce ku saurara kuma ku kalli abin da mutanen Kaduna suka fadi game da sakonku, na cewa, sun bayyana cewa, su ma suna son a hade. Aka kai musu wannan sako, suka ce za su yi nazari a kan abin da aka fada, kuma za su mayar da jawabi ga Dakta Ahmad Gumi kan nasu ra’ayin da fahimtarsu da matakan da suke so a bi wajen hadewar gaba daya.

Duk wadannan abubuwa an yi sune a asirce gaba daya, babu wanda ya sani tunda manufar yardar Allah (T) ake nema. To, da azumi ya zo har aka fara azumi, alkawarin kwana biyu da suka yi ba su aiko da jawabi ba. Mako guda (babu jawabi), mako biyu (babu), lamari yana ta ta’azzara, ga lokaci yana kurewa, ga shi kuma babu jawabi. Don haka sai Dakta Ahmad ya bayyana wannan kuduri lokacin da ake tafsiri.

Tunda an ba kowa damar ya fadi abin da yake so ya fada, ko kuma matakan da za a bi wajen daidaituwar an kasa cimma wannan burin, to shi bari ya yi amfani da tasa manufar don cimma burin hadewa da dinkewar wadannan bangarori guda biyu.

Wannan shi ne ya kai mu taron yau na (10-10-1426) bayan Hijira, wadda ya zo daidai da Miladiyar Annabi Isa (AS), 11-11-2005 kuma a wannan yini mai albarka kamar yadda ya fada lokacin taron.

KOWANE BANGARE YA ZO WAJEN TARON

Shugabanni da yawa sun taho. Sai dai ba sun zo bane a kan shugabanni kamar yadda Malam ya fada lokacin tafsiri. Sun zo ne a kan masu yi wa addinin Musulunci hidima da kuma dawainiya wajen karantar da shi ga Musulmi din.

Malam Alhasan Sa’id ya zo, Malam Abubakar Jibril, Limamin Farfaru ya zo, Malam Ja’afar Adam ya zo daga Kano, Malam Rabi’u Daura ya zo, da ire-iren wadannan da yawa daga cikin shugabanni na kasa. Wadanda ba ka gani ba, wasu ba su dawo daga Umura bane kamar su Malam Yakubu Musa.

BAN SAN ABIN DA YA HANA SU SHEIKH YUSUF SAMBO ZUWA BA

To, ba ni da labarin ko sun yi taron ko abubuwan da suka tattauna. Amma a ba kowa uzuri, in ba a gan shi ba a yi masa kyakkyawan zato.

AKWAI WADANDA SUKA ZO DAGA BANGAREN JOS

Akwai wadanda suka zo daga bangaren Jos. Su ma sun zo ne a matsayinsu na ’ya’yan kungiyar don an ce duk wani dan kungiyar da aka kafa kungiyar da shi daga cikin Malamai da attajirai ko ma’aikata, an gayyace shi. Saboda haka wadansu sun taho ba a san ma sun taho ba, saboda ganin yadda wajen ya cika.

TARON YA CIMMA NASARA

Alhamdu lillahi Rabbil alamin. A ce an kira taro, kuma har a zo taron, wata manuniya ce cewa, jama’a suna kan wata gaba ta neman wani ya jawo su ya fitar da su daga abin da ya dami kowa, shi ne rarrabuwar kan Musulmi, kowa ya kama gabansa, maimakon a kama manufa daya ta ilimantar da mutane addininsu, wanda da shi suke bauta wa Allah.

Zuwan kansa ko da ba a yi magana ba, ko da ba a zauna ba, ya taimaka kwarai da gaske, domin akwai wadanda suka yi shekara wajen 14 ba tare da sun hadu ba, wato tun rabuwar Izala. Sai ga shi yau an hadu. Sannan wasu kuma sun balle gaba daya kamar ’yan Salafiyya. Yau ga shi su ma sun dawo, sun ce sun yarda a tafi da su gaba daya. Ka ga wannan taku ne na farko wanda daga nan ne za a yi gini har a cimma buri.

SANARWAR ’YAN JOS BAI HANA WA TARON CIN NASARA BA

A’a, inda kowa ya ji abin da suka fada, ai da kenan babu wanda zai zo, amma tunda ga shi an zo, kuma zuwan ya kai inda ya kai, don tunda aka gina masallacin nan (Sultan Bello) bai taba ganin jama’a haka ba, ko ranar bikin bude shi. Muna godiya ga Allah. Sannan shugabanni sun goyi bayan taron. Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Maccido ya nuna shi dan Izala ne (masoyinta), kuma ya goyi bayan Izala, ya aiko wakilinsa. Sarkin Zazzau haka, sauran Sarakuna haka. Gwamnoni kowa ya aiko da wakilinsa. Gwamnan Jihar Jigawa, bayan turo jami’ansa daga farko, ya zo da kansa. Ma’aikatan gwamnati tsofaffi da wadanda suke kan aiki da masu kaki da marasa kaki sun taho. Wallahi don su amsa wannan kiran. To, wannan shi kansa nasara ce, ballantana kuma an samu wata matsaya wadda take an gano bakin zaren, ga yadda za a fara tufka.

MATSAYAR DA AKA CIMMAWA

Wannan shi ne aikin da kwamitin da za a haifar zai yi insha Allah. Wannan kwamitin zai yi aiki na wata uku zuwa shida, domin ya fitar da wata Majalisa (wadda za ta gudanar da zabe) wato kamar ‘electoral college’ a Turance, wanda zai gayyato duk sauran Malaman kowa ya zo a matsayinsa na Shugaban jiharsa domin fitar da shugabannin da za su amsu a wajen kowa da kowa don ci gaba da wannan aiki na wa’azi.

AN KAFA KWAMITIN DA ZAI YI WANNAN AIKIN

Bisa ga shawarar Sarkin Musulmi, an dora wa wadansu mutane masu amana da tunani daga cikin Malamai da shugabanni na siyasa da shugabannin sojoji da suka bar aiki da shugabanni na gwamnati da sarakuna za su hadu su tattauna domin haifar da wannan Majalisa wadda za ta dauki dawainiyar kafa dawwamammiyar Majalisar Kungiyar Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah. Za ta ziyarci kowane bangare a inda yake, kowa a ji abin da yake damunsa, kuma ya kawo gudummawa don cimma wannan buri. Ka ga kenan, alhamdu lillahi, an ci gaba. Da mutum guda ne Dakta Ahmad Gumi yake wannan aiki, ya fadi ya tashi, yau ga shi dubbai sun amsa, sun yarda su yi aikin ko da ba ya nan, tunda shi zai koma makaranta.

Yanzu an zabo wadansu jama’a ne da ba wanda yake shakkar imaninsu da gudummawar da suke bayarwa ga addinin Musulunci, sune yanzu za su ayyana wannan Majalisa ta riko wadda za ta tsara zaben da zai haifar da Majalisar dindindin don tafiyar da Izala. Wato kenan yanzu akwai matakai uku kafin a cimma wannan buri din. Wannan taro da aka yi, shi ne doron da aka taka domin isa ga ragayar tafiyar haduwar Musulmi.

ABIN DA DAKTA AHMAD GUMI YAKE NUFI

Dakta Ahmad Gumi bai ce duk wanda ya taho za a tafi da shi, wanda kuma bai zo ba a tattaka shi a wuce ba. Abin da ya ce shi ne, ko ba su zo ba kujerarsu tana nan duk ranar da suka zo, su shigo su zauna. Don Musuluncin nan na bukatar aikin mutane da yawa. Mu ba mu kori kowa ba, kuma kofa da taga suna nan bude, duk wanda yake so ya shigo a tafi da shi, ya shigo. Dukkansu ’yan uwanmu ne, kuma kowannensu kokari yake yi ya yi kira zuwa ga Sunna.

IZALA BA KUNGIYAR NEMAN KURI’A BACE

Hadisi ya ce idan mutum uku suka hadu, su zabi shugabansu. To, yaya mutum dubu za su hadu ba mai tafiyar da al’amarinsu? Gaba daya, tafiyar da al’amurran Musulunci ai siyasa ne. Amma siyasarmu ita ce Alkur’ani da Sunna, kuma duk inda Musulmi mutumin kirki yake, muna tare da shi. Dan siyasa ne ko dan kasuwa ko kowace harka yake, muna tare da shi a kasar nan ko ba a kasar nan ba. Wannan ce manufarmu.

Amma mu fito mu ce mu ’yan PDP ne, ko ANPP ko AD ko kowace jam’iyya, wannan ba namu bane. Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah ba kungiya bace ta neman kuri’a ko neman shiga a tafiyar da gwamnatin Nijeriya.

NASIHATA GA SHUGABANNIN IZALA

Wallahi ina fatan su ci gaba da aiki na alheri da suka fara, kada son zuciya ko wadansu da suke amfana daga barakar da ke tsakanin ’yan uwa guda biyu su hana su cimma wannan buri, su tsaya su nemi lahira wadda ita ce dawwamammiya, kuma su nemi yardar Allah (T) su guji neman duniya.

In wata kyautatawa ta duniya ta zo, to wannan bushara ce. Saboda haka Izala tana fada ne da rarrabuwar Musulmi, tana fada da bidi’a. Rarrabuwar Musulmi kafirci ne, haduwarsu kuma Musulunci ne. Wannan shi ne aikin Izala. To kuma kada kadin da ta yi daga abawa ta koma tana warware shi. Wannan ita ce nasihata ga shugabannin bangarorin biyu. Su kaunaci Allah, su nufi lahirarsu ta gyaru ba duniya kawai ba.

Su kuma mabiya su yi da’a ga duk wanda ya yi wa Allah da’a, su yi da’a ga duk wanda yake kira ga Sunna.

Kwankwaso ya yi wa kansa kafar ungulu a Kano

In ji Malam Sunusi Abdulkadir

A makon jiya ne aka yi gagarumin taro, don tunawa da ’yan uwa shida da suka yi shahada sakamakon kisan gillar da gwamnatin farar hula ta tsohon Gwamnan jihar Kano na jam’iyyar PDP, kuma Minstan tsaro na yanzu, Alhaji Rabi’u Musa Kwankwaso ta yi masu shekaru hudu da suka gabata jim kadan bayan kammala muzaharar Kudus ta wannan shekarar.

Taron ya hada da jawabai, fareti da kuma ziyarar makarbartar Shahidan da ke Kofar Mazugal, inda aka yi addu’o’in neman gafarar Allah ga mamatan da ke kwance wajen. Bayan kammala taron, wanda aka yi a Masallacin Fagge ranar Asabar din nan da ta gabata, Wakilanmu Aliyu Saleh, Hasan Isiyaku da Ali Kakaki sun tuntubi daya daga cikin wadanda suka jagoranci taron Malam Sunusi Abdulkadir don jin makasudin shirya shi. Ga hirar kamar yadda Aliyu Saleh ya rubuta mana. MAKASUDIN SHIRYA TARON

Da farko makasudin shirya wannan taron shi ne, tunawa da Shahidan Kudus, lakabin da aka yi masa kenan. Domin tun lokacin gwamantin Kwankwaso da muka yi muzaharar Kudus bayan salla, a wannan lokacin ne kuma jama’an tsaro a karkashin gwamnatin Kwankwaso suka bude wa ’yan uwa wuta, wanda a take a wurin mutane takwas suka rasu, shida dai mun tabbatar ’yan uwa ne, amma sauran biyun da alama ma ’yan kallo ne, wannan ya sababba duk shekara a lokaci ya wannan, muke haduwa, don tuna mutanen da wannan waki’ar ta kashe. Mana juyayin kisan gillar da aka yi wa ’yan uwa da suka yi muzaharar Kudus a lokacin. Duk wani da yake bibiyar abin da muke yi ya san a cikin shekaru hudun nan da aka yi muna tuna wannan ta’addancin duk shekara, muna yin irin wannan taron.

TARON BA SHI DA ALAKA DA SIYASA

Da ma ita wannan siyasar da ake yi a wannan kasar tana da cikas dinta, an yi wannan taro, ko ba a yi wannan taron ba dama can dimokradiyyar wannan kasar tana da nata cikas din, saboda ba ta da wata nasara da za a iya cewa ta cimma, in banda munanan ci baya da ta jawo. Wannan abin da nake fada, hatta su kansu ’yan siyasar ko kuma ’yan dimokradiyyar na gida na da waje sun tabbatar da cewa babu wani abu da gwamnatocin farar hula da muke da su da suka haifar in banda cikas. Ina banda irin abin da Kwankwaso ya yi na kashe mutane, wanda yake idan da dimokradiyyar ake yi da gaske babu wani dalili don mutum ya fito yana bayyanar da ra’ayinsa, wani kuma ya zo ya hau shi da haribi. Alhali ba ganin sa aka yi ya kashe wani, ko ya kona kayan wani, ko ya yi wani laifi ba, amma sai aka bude masa wuta. Ka ga zancen cikas, dama tuni ita dimukradiyya ta yi wa kanta.

KWANKWASO YA YI WA KANSA KAFAR UNGULU

Shi Kwankwaso shi ma dai kamar yadda na fada a baya, da ma can kafarsa ta ungulu ce, ka ga ba batun wani ya yi masa kafar ungulu kenan, domin shi ya riga ya yi wa kansa. Kuma ni a ganina komai lalacewar Kanawa ba za su dawo da Kwankwaso ba, ban ce maka wani mutum ba, amma dai Kwankwaso dai komai lalacewar Kanawa ba za su yarda su dawo da shi ba, domin bai tsinana wa mutane komai ba, face kashe-kashe, wanda yake muna da jerin mutanen da ya kashe baya ga ’yan uwa a rikice-rikicen da aka yi. Sannan kuma ga mulki na kama-karya da nuna karfi a abubuwa da daman gaske. To ka ga ba wanda yake sha’awar Kwankwaso ya dawo ya maimaita irin wadannan abubuwan da ya yi a baya.

BA ZA MU MANTA DA SU BA

Ina ma shi da kansa Kwankwaso ne ya yi wannan maganar ya ce a manta da wadanda ya kashe a yi masu addu’a kawai, da ya ji abin da zan gaya masa. Amma da yake mu da shi ba mu ji ya yi wannan maganar ba, sai dai hasashe na cewa ta yiwu wasu su fadi haka, sai mu ce wa masu wannan has ashen, kuskure ne a kashe maka dan uwa bisa zalunci, ba laifi ya yi aka kai shi kotu ba, kotu kuma ta yanke masa hukuncin kisa ba, wani ne kawai saboda yana takama yana da gwamnati kawai ya kashe shi, ka manta da shi.

Da farko dai dole ne ka dauki darrusa daga kashe shin da aka yi, ya zamana wannan kisan da aka yi masa ya yi maka kaimi na ci gaba da dakewa a kan abin da kake yi. Wannan tunawar da za ka yi da shi zai sa ka tunatar da na baya da kuma abokan arzikin wannan mutumin cewa fa wane ne ya kashe masu dan uwa, kuma suna da hakki a kansa. Wannan kuma zai zo ne bayan ana yi masu addu’a kenan.

Don haka babu zance a manta da su a ci gaba da yi masu addu’a kawai. Amma ya za a yi a manta da su, alhali Allah (T) ma ba ya mantawa da ’yan ta’adda? Masalan wanda ya fara yin kisan kai a bayan kasa, ka ga Allah (T) bai manta da shi ba, kullum ana tunawa da shi a cikin Alkur’ani. Ka san a cikin ’ya’yan Annabi Adamu (AS) guda biyu din nan daya ya kashe daya, (kisan kan da Kabila ya yi wa Habila), wannan shi ne kisan farko da aka yi a doron wannan duniya, ka ga ai Allah (T) bai manta da shi ba.

KWANKWASO BAI YARDA YA YI LAIFI BA

Ai shi saboda giriman kan Kwankwaso bai ma yarda ya yi lafi ba. Ka san sai mutum ya yarda ya yi laifi ya tuba ga Allah (T), kuma sai ya yarda zai biya diyya, ko kuma ya yi kaffara ta azumi kamar yadda Allah (T) ya yi mana bayani a cikin Alkur’ani mai tsarki. Shi a nasa girman kan bai ma yarda ya yi kiskure ba, mutumin da bai ma yarda ya yi kuskure ba, ana ma tsammanin idan ya samu wata dama zai sake maimaita abin da ya yi, wace diyya kuma yake tunanin ya biya?

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International