Almizan :Ina hukuncin yin kayan aure, wanda gidan amarya suke cewa sai mai neman ’yarsu ya yi? ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 24 Shawwal, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Tambaya da amsa:Tare da Shaikh Ibrahim Zakzaky

Ina hukuncin yin kayan aure, wanda gidan amarya suke cewa sai mai neman ’yarsu ya yi?

SHAIKH ZAKZAKY
Malam Ibraheem Yaqoub Zakzaky H.
Ya na amsa tambayoyinku

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Mutum zai iya yin azumi ya ce ya sadaukar da ladan ga Fadimah (AS) ko wani Imami, musamman a lokacin Maulidinsu?

Daga Kabiru Abba Funtuwa mazaunin Wuse Abuja 08036116512

SHAIKH ZAKZAKY: Ayyuka da ake yi dai ma’asurai ne. kuma cikin abin da muka san ana yi salla ne bayan ziyara, a ce Allah ya kai ladan zuwa ga wanda aka ziyarta. Amma ba mu san akan yi wasu ayyukan daban ba. Saboda haka mutum ko mene zai yi, ya lizimci wadanda aka ruwaito su ake yi.

TAMBAYA: Assalamu alaIkum. Malam, menene hukuncin wanda yake aikin gwamnati, yake aiki a ‘finance’, sai ya cire kudin gwamnati ya je ya yi karatu da shi, ba tare da izinin shugabansa ba, domin ba shi da wata hanyar samun kudi? Kuma karatun da ya je ya yi za a karu da shi a ‘finance Dept’ din.

Daga Yusuf As-Sadik alsadik67@yahoo.com

SHAIKH ZAKZAKY: In na fahimce shi kila kudin zai sata kenan. Idan yana nufin ya yi aro ne zai biya, sai mu ce ba laifi, kila ma a yafe masa in an gano. Amma in yana nufin zai yi sata ne, ba zai halatta ba.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam wa ke da hakkin sanya lokacin da za a yaye yaron da aka haifa, uwa ce ko uba, ko kuma iyayen su biyun? Kuma wane lokaci ne Musulunci ya kayyade a yaye yaro? Idan ya zarce wannan lokacin an saba ne, ko kuwa sai dai lokacin da aka ga damar yaye shi?

SHAIKH ZAKZAKY: Cikakken yaye dai shekara biyu ne. Saboda haka idan iyaye ba su so cikawa ba, sun samu su tattauna su biyu. Kamar yadda yake tambayar uwa ko uba ko ko su biyun, sai mu ce su biyu ne za su yi shawara su biyun su zartar da cewa ana iya a cire shi a nono kamfin ya yi shekara biyu, kuma ana so ya zama an cire shi a nonon ne a lokacin da cire shin ba zai cutar da shi ba. Saboda haka ba a kayyade lokacin ba, amma abin da ya kama tsakanin shekara daya zuwa biyu ne in sun ga maslaha ne cire shin, amma in ya zama cire shi a wani lokacin zai zama ya cutu, ka ga shi ma an ci da nasa hakkin. Saboda haka a nan abin da za mu ce tunda a nan yana tambayar ko an saba ne? Sai mu ce e, to ba a ba yaro hakkinsa ba kenan. Kuma ka ga abin da ya fi zama maslaha shi ne a ba shi hakkinsa, kodayake in wani dalili ya kunno za a iya cirewa da wani abin da zai iya tsayawa a matsayin shayarwa, to ana iya komawa ga shi, babu laifi.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam na fara ramakon azumi ne na wata shekarar da ta wuce da yake zan yi ramakon tare da ciyarwa ne, yanzu kuma ba ni da halin ciyarwa, zan iya yin azumin alabasshi ciyarwa kuma daga baya, idan na samu halin ciyarwa na ciyar?

Daga Yahya Sa’idu Shendam jihar Filato 0803 052 1780

SHAIKH ZAKZAKY: Haka ne, tunda yake abin da ya hau kanka yanzu shi ne ramuwa da ciyarwa, saboda haka yin su a tare ko a daban-daban yana iya yin su duk yadda ya zo masa. Ya samu ya yi azumin, ran da ya samu hali ciyarwar kuma sai ya ciyar.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam ’yan fashi ne suka yi shiga gidan wani bawan Allah suka yi masa fashi kuma suka yi wa matarsa fyade, sai kuma Allah Ya sa ciki ya shiga. Ina matsayin wannan yaron kenan?

Daga 0803 689 5892

SHAIKH ZAKZAKY: Yana da uwa kenan. Da ma bayan wannan fyaden sai ta yi ‘istibra’i,’ ya zama mijinta ba zai zaike mata ba har sai ta yi idda. Idan ciki ya bayyana a lokacin ya tabbata kenan sakamakon wannan fyaden ne, saboda haka yanzu shi yaron sai a rike shi a matsayin dan ita wannan matar. Kuma tunda dai ba laifinta bane, ba laifin yaron bane, illai iyaka dai shi za a jingina shi ne zuwa ga uwarsa ne kawai.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam, ni Nurse ne, sai aka tura ni aikin hajji don in kula da lafiyar Mahajjata, sai na yi amfani da wannan damar na yi aikin hajjina. Shin yaya matsayin aikin hajjin nawa da na yi, ya inganta kuwa?

Daga 0805 361 5350

SHAIKH ZAKZAKY: Eh mana. Sai dai in shi aikin nata ba zai yiwu a yi shi tare da hajjin ba, sai ta ki aikin ta yi aikin hajji. Amma idan aikin zai iya tafiya tare da aikin hajji, riba biyu kenan.s

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Ina matsayin mutumin da yake yawan yin mafarki da Imamai (AS). Shin hakan ya nuna matukar son da yake yi masu kenan, ko kuwa?

Daga Yunusa Sulaiman Gangare Yankin Police Stations Jos jihar Filato.

SHAIKH ZAKZAKY: Shi mafarki dai kamar wani albishir ne, saboda haka tunda yake mai yiwu yana yawan tunaninsu, saboda haka sai yana yawan mafarki da su. Amma ba za mu iya daukar cewa wannan shi ne ma’aunin son sa da su ba. Sai dai illa iyaka mu ce wannan wani kyakkyawan albishir ne, sai ya kara kaimi wajen ‘tumassaki’ da tafarkinsu.

TAMBAYA : Assalamu alaikum. Ina hukuncin gina otal a wannan zamani namu, musamman ganin abin da ke gudana na badala a cikinsa?

Daga Zakariya A. Ibrahim Kano 0802 378 2851.

SHAIKH ZAKZAKY: Da yake otal yana ba da ma’anoni daban-daban, idan dai irin wanda ake yin masaukin baki ne da cin abinci, sai ya tabbatar da cewa duk abin da za a yi a otal din na wanda yake ya halatta ne, ya zama ya hana duk abin da ya haramta. Alal misali ba zai yarda miji da mace su kama daki alhali ya san su ba ma’aura ne ba. Kuma ba zai yiwu a zo a yi hayar otal dinsa a yi wasu ayyuka na fasadi ko a sha giya ko abin da ya yi kama da haka ba. A takaice mutum yana iya yin otal, ba lale otal yana nufin lalacewa ne ba, duk abin da ya zama ya saba wa shari’a ya tabbatar da cewa ba a yi shi a otal din ba.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam, ina hukuncin yin kayan aure da ake yi wanda gidan amarya suke cewa sai mai neman ’yarsu ya yi, idan bai yi ba kuma babu auren kenan?

Daga Naseer Mije Katsina 0802 791 3426

SHAIKH ZAKZAKY: Bisa shari’a dai abin da aka sani ana ba da sadaki ne. Kuma idan su wadanda za su ba mutum aure suka kallafa masa ya yi wani abu, baya ga sadakin, wanda kuma in bai yi ba ba za su ba shi ba, to ya halatta shi ya yi. Kodayake su bai halatta su bukace shi da ya yi ba. Saboda haka su abin da suka yi ne ya saba, amma shi in ya ga yana bukatar auren, kuma dole in bai yi ba ba za a ba shi ba, to yana iya yi.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam, ya halatta mutum ya je gai da marar lafiya wanda yake ba musulmi ba, har kuma ya roka masa Allah Ya ba shi lafiya?

Daga 0803 211 6375

SHAIKH ZAKZAKY: Ba laifi da wannan. In zaman aiki ko makwabtaka ta hada su zai iya ziyartar sa har ya yi masa fatan Allah ya samu lafiya. In ya mutu ma zai iya zuwa ya yi ta’aziyya, amma a nan ba zai roka masa gafara ba, sai dai ya ce Allah ya ba danginsa dangana.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam, ko ya halatta mutum ya yanke farcensa a bar wani sashi, misali yatsa daya ko biyu bai yanke ba?

Daga Ahmad Sa’id Ahmad Hizbullah 0803 619 4411

SHAIKH ZAKZAKY: Lalle wannan ya saba wa koyarwa sunna, sai dai in bisa wani dalili mai kamar na rashin lafiya. Amma a matsayin ado ya saba wa sunna. Sunna ita ce a yanke farcen gaba daya.

TAMBAYA : Assalamu alaikum. Malam, idan mutum yana bin Liman sallah, zai iya yin salawat a cikin zuciyarsa?

Daga Muhammad Erana

SHAIKH ZAKZAKY: Kila abin da yake nufi shi ne zai iya yi a asirce ba tare da ya bayyanar ba? Don haka sai mu ce in a asirce yake nufi, ya yi. Azkar ana furta su da baki ne. Idan ka bayyana murya, a bayyane kenan. In ka boye murya, a asirce kenan.

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malam, ni bakanike ne, sai wani mutum da muke aiki kusa da masallacinsa ya ce mu daina shiga masa masallaci domin muna bata masa shimfida. To ya za mu yi kenan, sai mu daina shiga ko kuwa tunda masallaci na Allah ne mu ci gaba da yin sallarmu?

Daga Muhammad Yusuf Kawo Kano

A biyo mu bashin amsar wannan tambayar da ma wasu a mako na gaba insha Allah.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International