Almizan :Shahadar Imam Musa Alkazeem (AS) ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 24 Shawwal, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Tunatarwa:Tare da Shaikh Ibrahim Zakzaky

Shahadar Imam Musa Alkazeem (AS)

SHAIKH ZAKZAKY
Malam Ibraheem Yaqoub Zakzaky H.

Masu karatu yau muna dauke ne da ci gaban jawabin da Malam Ibraheem Zakzaky ya gabatar a wajen taron Yaumu Shuhada na bana, wanda ya gabata a filin Kofar Shahidai (Doka) Zariya a kwanakin baya. In dai ana biye da mu yau muna mako na biyar kenan da soma kawo maku wannan jawabin. Mun dan dawo baya kadan don mai karatu ya ji dadin yin karatun yadda ya kamata. Kamar yadda aka saba, Musa Muhammad Awwal ne ya rubuto mana daga kaset. A sha karatu lafiya.

Ba ni da lokacin da zan yi maku dogon bayani a kan wannan. Ina so in yi maku bayanin cewa don mutum ya sani, in ma ya ga ana rikici tsakanin musulmi da musulmi, to ya tabbatar da cewa wannan rikicin, in ya bi diddiginsa ya bincika sai ya samo asalinsa daga Amerika da Isra’ila aka yiwo.

Kuma shi Bayahude burinsa shi ne ya ga ya kashe mutum, kuma yana jin dadin ya ga gawa. Ya zo a Hadisi cewa in kuka kadaita da Bayahude, daga kai sai shi, to abin da zai zo a tunaninsa shi ne ya zai yi ya kashe ka? Wato da za ku shiga tarago daya da Bayahude, in ka ga yana kallon ka, a zuciyarsa abin da yake tunani shi ne ya zai yi ya kashe ka? Wannan, hadisin Manzon Allah ya zo da wannan.

Shi yana jin dadin ya ga gawa ta musulmi. Yana kuma son ya kashe wani ma in da ba musulmi bane. Kuma bil hasali ma har a littafinsu sun rubuta suka ce wai ayar Allah ce a cikin Attaura, “ku kashe su duk cikansu, mazan ku kashe, matan ku kashe, har yaran ku kashe, duk dabbobinsu ku kashe, shanunsu ku kashe, awakinsu ku kashe, kajin ku kashe, har kwayayensu ku kashe.” Wai aya ce a cikin Attaura.

Kuma yanzu ma suna koya wa yaransu ’yan Firamare wakoki. In sun tashi daga makaranata za su koma gida, suna waka ne ana tafi. “Za mu kashe su, za mu kashe su, duk cikansu za mu kashe su, Larabawa za mu kashe su, za mu kashe su za mu kashe su.” Waka ake koya wa yaro dan karami in ya taso daga Firamare: “Za mu kashe su, za mu kashe su, duk cikansu za mu kashe su, Larabawa za mu kashe su, kowannensu za mu kashe su, jariransu za mu kashe su, matansu ma za mu kashe su, manyansu za mu kashe su, za mu kashe su za mu kashe su.” Wannan waka ake koya wa yaro.

Don ka sani in za ka zama karen Bayahude, jakin Bayahude, wanda zai yi amfani da shi ya kashe musulmi, to ka ba da kokari. Ka sani cewa ba mamaki wannan aya za ta yi aiki a kanka, domin makomarka za ta kasance tare da shi ne. Shi kuwa in ya shiga wuta ba zai fita ba. Ba a yi wuta domin musulmi ba, amma Allah(T) yana cewa “ku ji tsoron wuta wanda makamashinta mutane ne da duwatsu wanda aka yi tanadinta domin Kafirai.” Domin ba a yi tanadin wuta domin Mumini ba, amma idan mumini ya fandare shi ma sai ya bi kafirai a wajen shiga. An yi tanadinta domin su ne. Su dawwama za su yi, in suka shiga ba su fita.

To kai ka ji tsoron wannan wutar wanda aka yi domin su, in ka yi aiki domin su, ka koma makomarsu. Ka ci wuya biyu, nan kai sunanka mumini, gobe kiyama sunanka kafiri. Kuma ka fi su ma muni don sunanka munafiki. “Innal munafikina fiddarkil asfali minannari walan tajida lahum nasira.” Munafukai sune a kuryan karshe na wuta, ba kuma za ka sami mai taimakon su ba. Ba wanda zai ce, ai wannan ya yi salla ya yi hajji, ya ba da sadaka, ya taimaka wa jama’a, a ji tausayin sa. Ba wanda zai ce haka nan. Tunda ya yi aikin Yahudawa, ya taimaka masu, ya tafi makomarsu!

A irin wannan, da so samu ne, da mun zauna musamman saboda jajanta abin da ya faru ranar Laraba da ta wuce a Kazimiyya (a lokacin da Malam yake wannan bayani). Wanda Yahudancin duniya, wanda Amerika ke wa jagoranci suka dira a kan musulmi ta hanyoyi daban-daban. Na farko, hanyar harba bama-bamai daga bayan gari, wanda muka san ba wanda zai iya harba wannan in banda Amerikawa, don su suke mamaye da kasar, kuma su suke yawo da motoci da igogi a cikin garin.

Suka harba a cikin masallaci da dandazon mutane. Mutane suka fito, ana fitowa a firgice, don bama-bamai na dira a kan mutane, ana gudu, sai kuma aka bi ta gada, gadar kuma saboda turmutsutsu har ta karye kuma aka shiga harbi. Ana cikin wannan ma sai aka harba Katuhsha, wato mizayil din Katuhsha. Wanda yake za mu tabbatar sun yi amfani da wannan ne da gangan, don Katuhsha Rasha ke kerawa, kuma ’yan Hizbullah sun sha amfani da shi a kan Yahudawa. Saboda haka Katuhsha yakan ba su tsoro, kamar yana alamta cewa abin da musulmi ke harbin su da shi kenan. Amma su makamansu na MOSSAD da na Amerika wani abu ne daban, amma ran nan sai suka harba Katuhsha a kan musulmi, wato kamar mun rama, mun harbe ku da Katuhsha. Amma su Katuhshan Hizbullah ana harba ma mayakan Isra’ila ne wanda suke yakan al’ummar musulmi. Su kuwa Katuhsha din su sun harba a cikin masallaci ne a dandazon mutane masu AZA na shahadar Imam Musa (AS).

Ana cikin wannan kuma bayan wasu sun dira sun fada ruwa, gada ta karye ta zubar da wasu, sai kuma aka je asibiti aka lura wasu na mutuwa. Kuma sai aka lura cewa an ba su abinci ne mai guba, ko ruwa na sha ko wani abinci suka ci da guba, wanda yake nufin Yahudawa sun zo kenan.

To da yake aikinsu a duk sassan duniya ne, kuma tuntuni sun sa wa kasar nan ido, ba mamaki da muka ma ga yanzu ana gargadin mutanen da suka halarci wannan taro cewa su yi hankali, an ga wani karamin munafuki, kare, ya sa wai fiya-fiya, inda na gane cewa lallai ba daga Isra’ila aka kawo biredi din ba, a nan ne, ‘made by Munafikin.’ Wani ya samu ya zuba wani abu. Shi kila in da zai ji labarin wasu sun mutu a nan zai yi murna, ya ce ‘yawwa, mun kashe su.’ Sai kuma can magidantansa su ce ‘yawwa tunda biredi mai fiya-fiya ya yi, nan gaba a aika da wadansu abubuwan da suka wuce haka nan.’

Alhali na san da can in ana Muzahara, har Inyamurai sukan ba ’yana uwa ruwa suna sha. Su ajiye ruwa a Firij ya yi sanyi su bayar. Kuma suna bayarwa su a zuciyarsu da cikakken goyon baya ne. Kuma ’yan uwa sukan ta sayen kayan mutane ma na sayarwa, abincin sayarwa na mutane, ba don komai ba domin su taimaka masu ma, don wasu daga nan jarinsu kan mike har su yi ta samun albarka. Saboda za su ga sun yi wo kayan abinci duk an saye. Don wani zai zo ya ce duk abincin da kake sayarwa na nawa ne? Akwai wani zai daga abincin ya ce na nawa ne? A ce na kaza ne, ya biya kudin ya ce a raba wa mutane fisabilillah. Su yi ta murna, su yi ta sa albarka.

Wato kila wannan yana ba su takaici, bari su bullo da wani ra’ayi su yada jita-jita cewa in aka raba abinci aka ci za a mutu, ya zama mutane su daina ciniki din. Kun san ko ba komai su irin masu saye da sayarwar nan su suna amfana da irin tarurrukan nan, tunda sukan zo da abincinsu su sayar. Kila shi ma wannan yana bakanta masu rai. Alhali ba ’yan uwa ne suke yin abincin ba, mutanen gari ne. Mutanen gari su yi abincinsu, kuma suna sayarwa in an yi wani taro, har ma sukan ce a gaya masu in za a yi taro saboda su yi abinci mai yawa.

Har (’yan tawayiyya) ma, mayu ma, sun taba yin taro, sai wasu suka ga taron, sai suka dauka ’yan uwa ne, sai suka je suka yiwo tuwo mai yawan gaske, sai aka bar su da kwantai. Suka ce, a’a ya suka ga mutane ba su taru da yawa ba? Sai aka ce, ai wadannan masu zagin su ne, ba sune ’yan uwan ba. Suka ce ‘Allah ya tsine masu!’ Sun bar su da kwantan tuwo.

Sun saba in an yi taro a nan, duk wani mai sayar da shayi, mai sayar da burodi, mai sayar da gasasshen nama, mai sayar da kifi, duk su kam lallai tsaf, ‘Business’ zai yi kyau sosai. Wala’alla ka ga suna kokarin in an yi wannan, a sa wa mutane tsoro kenan, ya zama shi kenan ba dama a kawo abincin.

Abinci kam za mu ci, saboda dama dan Adam dole ya ci abinci. Amma za mu dauki matakin da ya zama cewa kenan kun yi wa wasu mutane masu yin ‘Business’ na wani abin tabawa hasara kenan. Saboda mutum zai zo ne bai ci abinci ba, bai sha ruwa ba? Sai ya sami amintacce. Kun ga kun yi wa mutane hasara, kila ku ji dadi. Don ba mu damu da wajen wanene muke saye ba, matukar dai shi musulmi ne. Kai ma idan dai ba yanka ne ko wani abu ba, kamar ruwan sha ma ana iya karba na kowanne. To amma yanzu kun yi wa wasu hasara.

To, irin wannan sun bayar da mamaki, kimanin mutum 50 aka kashe ranar Larabar da ta wuce a Kazimiyya a Irak sanadiyyar ba su guba. Kuma jimlar wadanda aka kashe yanzu adadinsu ya haura 1000.

IMAM MUSA YA SHA WAHALA, AN DAURE SHI DA SARKOKI

Da ma suna taron munasabar Shahadar Imam Musa ne (AS). To mu ma wannan taro namu, duk da asalin taron na farko da muka yi mun yi shi a watan Junairu ne 1992, amma ya dace da Rajab a lokacin. Don haka da shekara ta dawo wani Rajab din sai muka yi, amma sai ya zama a na 1993 din a Disamba ne. To tun daga nan sai muna yin shi a Rajab. Sai zuwa wani lokaci muka bayyana wa mutane cewa muna yin wannan taro ne daidai lokacin shahadar Imam Musa (AS), wato mukan yi ranar 25 ga watan Rajab ne. Dalilin da ya sa a wanan karon muka kawo shi yau 29 ga watan Rajab saboda ya dace da karshen mako ne don zai fi sauki ga masu zuwa, in ba don haka ba, da ma dai muna hankoron lokacin shahadar Imam Musa ne (AS). Kuma wannan tafarki ne dama na Shahidai, Limamanmu Shuhada ne. Shahidi bayan Shahidi.

Tunda akwai munasabar Shahadar Imam Musa, zan tunatar da mu kadan daga ciki. Imam Musa ya sha wahala, an daure shi da sarkoki, an dauke shi daga Madina garin Kakansa aka nufi da shi wani wuri kusa da Baghadad, aka tsare shi a kurkuku. Aka yi ta gana masa azaba, nau’o’in azaba a wannan lokaci.

Za mu ga cewa bayan Imam Ali da Imam Zainul Abidin sai Imam Musa a wajen addu’o’i, don wajensa ne aka sami addu’ar ‘Jaushan Sagir’ wadda a cikin wani hali da ya shiga ya karanta. Kuma wajensa aka samu addu’o’i da daman gaske, har da addu’ar 27 ga watan Rajab. Daidai wannan lokaci ne aka kama shi daga Madina aka nufi Baghdad da shi.

Kuma bayan an tsare shi ya dade a tsare, wani daga cikin almajiransa ya so ya gan shi, sai ya gaya wa mai tsaron sa a boye cewa in ya yarda ya kai shi a asirce ya ga Imam (AS), sai ya ce, to zai shiga da shi. Wato shi kamar ‘Wada’ ne, wato shi ne mai tsaron Imam din. Sai ya shiga da shi, har ya saka shi a cikin dakin da ake tsare da Imam Musa.

To sai ya ga domin sa ma Imam tunani na bakin ciki, a tunanin Sarkin wannan lokacin, Haruna kenan wanda ake ce masa wai Rasheed, don bayan an sa masa sarkoki a hannuwansa da kafafunsa da wuyansa, to kuma a dakinsa sai aka haka kabari. Da mutumin ya shiga sai ya ga Imam din ga irin halin da yake ciki, ga kuma kabari a gabansa. To sai ya shiga kuka. Sai Imam (AS) yake ce masa, kana kukan mene? Ba ka san mu sharri ba ya samun ba? Duk abin da ya same mu alhairi ne.

Za mu ci gaba insha Allah.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International