Almizan :Sojin Amurka sun karkashe fararen hula ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 24 Shawwal, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Duniya Labari

Sojin Amurka sun karkashe fararen hula

Daga Hasan Muhammad

A ranar Litinn da ta gabata ne sojin mamaya na Amurka a Iraki suka bude wuta kan wata karamar bas makare da mutane kusa da garin Baquba, inda suka kashe mutum biyar ’yan gida daya, cikinsu har da yara kanana, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na REUTERS ya ruwaito.

Wani kakakin sojin Amurka ya fada cewa bas din dai ta ki tsayawa ne lokacin da aka tsayar da ita a wurin duba ababen hawa a garin na Baquba.

REUTERS ta ruwaito cewa mutanen motar na kan hanyarsu ne daga garin Balad,

mai tazarar kilomita 80 daga Bagadaza, inda za su je ta’aziyya a garin na Baquba, lokacin da sojin Amurka suka bude musu wuta.

Ahmed Kamel al-Sawamara, 22, wanda shi ne ke tuka motar ya fada cewa kwatsam ya ga sojin na Amurka a gabansa, kuma kafin ma ya yi wani abu tuni sun bude musu wuta.

“Kawai ji muka yi sojojin sun bude mana wuta ta kowane bangare,” in ji shi, yana mai cewa; “Na ma tsaya din, amma ba su daina harbin mu ba. Ina gani ana kashe min ’yan uwana daya bayan daya, sannnan daga baya motar ta kama da wuta.

Manjo Husain Ali, na sojin Iraki ya tabbtar da cewa sojin na Amurka sun kai hari ne kan motar.

Majiyar ’yan sanda ta ce mutum biyar ne na cikin motar aka kashe, uku daga cikinsu yara kanana ne. Haka kuma wadanda suka samu raunukan cikinsu mata biyu da yara biyu ne.

Tun dai lokacin da Amurka ta mamayi Iraki cikin watan Maris na 2003, ana ta samun rahotanni kan yadda sojin Amurka ke kashe fararen hula ba gaira ba sabat.

Sojan mamaya sun kwama da Hizbullah

Daga Hasan Muhammad

Sojojin mamaya na haramtacciyar kasar Isra’ila sun kashe dakarun Hizbullah uku a wani gumurzu da aka yi a yankin Sheba da ake takaddama a kansa ranar Litinin din da ta gabata.

’Yan sandan da ke bangaren iyakar Lebanon sun ce fadan ya barke ne da misalin karfe 3:00 na yammacin ranar, kuma an dauki tsawon sa’a biyu ana yin sa.

Rahotanni sun nuna cewa gumurzun ya biyo bayan wani hari ne da Hizbullah suka kaddamar a wani yanki da sojin mamaya suka yi tunga, abin da ya sa su kuma suka

mayar da martani.

Ganau sun shaida cewa akalla an samu rahoton wata fashewa mai karfi har sau 250. “Wadannan hare-haren sun yi sanadiyyar shahadar dakarun Hizbullah,” cewar

wata sanarwa da ta fito daga Hizbullah din, tana mai zargin sojan mamaya da laifin shiga

iyakar Lebanon.

Wata majiyar kuma ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta ce akalla Yahudawa biyar ne suka samu raunuka, yayin da aka umurci mazauna yankin da su nemi mafaka a cikin

rumfuna masu ba da kariya daga harin bam.

Sakamakon wannan harin dai da Hizbullah suka kai, sojin sama na haramtacciyar kasar Isra’ila sun mayar da martani a kan wurare kamar hanyoyi a kudancin Lebanon, in ji wani Kakakin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito shi yana fada.

Shi dai wannan hari na ranar Litinin shi ne mafi muni a yankin na Shebaa tun cikin shekara ta 2000 lokacin da sojin mamaya na haramtacciyar kasar Isra’ila suka janye daga kudancin na Lebanon.

Shi dai wannan harin har ila yau ya zo ne a ranar da Lebanon take bukuwan samun ’yancin kanta, sannan a daidai lokacin da haramtacciyar kasar Isra’ila ke fama da rikicin siyasa bayan da Faraministan, Aerial Sharon ya yi murabus daga jam’iyyarsa ta Likud.

Gidan talabijin na ALMANNAR, mallakar dakarun Hizbullah, ya labarta cewa motocin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila tara ne, cikin su har da tankar yaki aka kai wa harin lokacin da Hizbullah suka jefa makamai masu linzami a wannan yankin.

Sojin na haramtacciyar kasar Isra’ila suka ce makaman na Hizbullah sun sauka ne a yankin Kiryat Shmona, Metula da kuma Kibbutz Snir.

A bayan wadannan hare-haren ne dai jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka shiga kudancin Lebanon, duk da cewa akwai takunkumin Majalisar Dinkin Duniya da ya haramta musu yin hakan.

Harin na haramtacciyar kasar Isra’ila ya shafi wurare uku ne na Hizbullah, wato Ghajar, Kudu maso Gabashin birnin Tyre mai tashar jirgi da kuma garin Khiam.

Haka kuma wadannan hare-haren sun zo ne bayan da haramtacciyar kasar Isra’ila ta harba makamai a wannan yankin da ake takaddama a kansa.

Haka kuma yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke ikirarin cewa haramtacciyar kasar Isra’ila ta janye daga Kudancin Lebanon, kuma duk da cewa Shebaa yankin Siriya ne da haramtacciyar kasar Isra’ila ke mamaye da shi, Lebanon da Siriya kuma sun dage a kan cewa har yanzu yankin na Lebanon ne.

Shugaban Iraki ya kai ziyarar aiki Iran

Shugaban kasar Iraki, Jalal Talibani, ya kai wata ziyarar aiki Jamhuriyar Musulunci ta Iran, inda kuma ya samu damar ganawa da manya-manyan jami’an kasar, ciki har da Jagoran juyin-juya halin Musulunci na kasar, Ayatullah Khamna’i.

A lokacin ganawarsu, Ayatullah Khamna’i ya yi karin haske kan yadda kasashen biyu, Iran da Iraki suka yi tarayya cikin al’adu da bangaren addini da kuma tarihi.

Haka nan kuma Jagoran ya kara jaddada cewa lalle Iran tana goyon bayan ganin tabbatar aminci da kuma kwanciyar hankali a baki dayan Iraki, sannan ya bayyana cewa Iraki ta al’ummar Iraki ce, kuma sune ya kamata su yi wa kansu zaben abin da zai jagorance su.

A wani bangare na jawabinsa a lokacin ganawar, Ayatullah Khamna’i ya nuna bakin cikinsa kan yadda ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula, musamman ma na baya-bayan nan a kasar Iraki.

A nasa bangaren, Shugaban kasar Iraki ya bayyana farin cikinsa ne kan yadda Iran take ba su goyon baya wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar, sannan kuma ya tabbatar da cewa tuhume-tuhumen kasashen waje kan hannun Iran wajen kawo tashin hankali a Iraki ba shi da tushe.

Shugaban kasar Iran, Dakta Mahmud Ahmadinajadi ma ya halarci ganawar da aka yi a gidan Jagoran da ke birnin Tehran.

Zaben Masar: ‘Ikhwanul-Muslimeen’ ta samu nasara

Rahotanni daga Masar suna nuna cewa sakamakon zagayen farko na zabubbukan ’yan majalisa da aka gudanar a kasar ya nuna cewa kungiyar ’yan uwa musulmi ta 'Ikhwanul-muslimeen' ta lashe akalla kujeri 33 na majalisar. Wannan kuma wata alama ce da ke nuna irin kara karbuwar da kungiyar ke samu tsakanin al'ummar kasar.

Haka nan kuma sakamakon da aka samu a wasu mazabu a karon farko tun ranar Talatar da ta gabata duk sun nuna irin wannan nasara da kungiyar ta 'Ikhwanul-muslimeen' ke ta samu.

Idan har sakamakon karshe na za`en ya tafi a kan haka, kuma hukumar zabe ta tabbatar da wannan abu, to kuwa a wannan karon kujerin kungiyar 'Ikhwanul-muslimeen' din za su nunnunka wanda ta samu a zabubbukan baya.

Tun a shekarun baya ne dai gwamnatin kasar Masar ta haramta wannan kungiya, amma Hukumar zabe ta kasa ta yarda ’yan takara na iya tsayawa zabe a kashin kansu.

Kamar dai yadda aka sani ne tun bayan gudanar da zaben Shugaban kasa da aka yi a kasar, wanda tsohon Shugaban kasar, Hosni Mubarak ya lashe, ake ta samun korafe-korafe daga ’yan hamayya wadanda suke nuna cewa lallai an tafka magudi.

Da ma dai ana gudanar da zaben Masar ne a matakai uku, kuma mataki na biyu zai fara daga 20 ga watan Nuwamba, sannan sai mataki na karshe wanda zai soma daga 1 ga Disamba.

An tuna da ranar korar Imam Khumaini (RA) gudun hijira

Kimanin shekaru 41 da suka gabata, a ranar 4 ga watan Nuwamban shekara ta 1964 jami’an tsaron Sarki Shah na Iran da aka hambarar suka tafi birnin Kum, inda Marigayi Imam Khumaini (RA) ke zaune suka kama shi sannan suka fitar da shi daga kasar zuwa gudun hijirar farko kasar Turkiyya.

Tun cikin daren ranar 4 ga watan na Nuwamba ne dai jami’an tsaron na hambararren Sarkin kasar, Shah, suka tafi gidan Marigayi Imam da ke can birnin Kum, inda suka kama shi sannan suka nufi filin jirgin saman Mehrabad da ke Tehran da shi sannan suka saka shi a jirgi suka kore shi daga kasar.

Sarki Shah hambararren Sarkin na Iran ya tsorata ne kwarai da gaske kan yadda kiran Marigayi Imam Khumaini (RA) ya rika samun karbuwa a wancan lokacin tsakanin dukkanin bangarori na al’ummar kasar, saboda haka nan sai ya fara ganin babbar barazana ne kiran Imam zai kasance gare shi.

Babban abin da ya fi tayar wa Shah hankali a wancan lokacin shi ne irin yadda Marigayi Imam Khumaini ya yi wa shirinsa na kwaskwarimar mallakar filaye (Land Reforms) kule, don haka ya firgita ya ga cewa in dai yana son shirin ya tabbata, to dole ne sai Imam Khumaini ba ya kasar, kamar yadda yake zato.

Imam Khumaini a wannan shekara ya mai da babban ranar idi ta kasa da ake kira da 'noruz' a matsayin ranar juyayi, saboda juyayin irin yadda Shah ya mayar da kasar zuwa ga dogaro da kasashen waje.

An gudanar da manya-manyan gangamomi a dukkanin manyan biranen kasar saboda tunawa da wannan muhimmiyar rana ta tarihi a kasar Iran.

An sake samun rikici da jami’an tsaro a Rasha

A safiyar ranar Talatar makon shekaranjiya ne wani sabon rikici ya sake barkewa tsakanin bangarorin wasu mutane da jami’an tsaro a garin Nalchik da ke kudancin kasar Rasha.

Shi dai wannan rikicin ya zo ne mako guda bayan wata gwabzawar da aka yi a wani rikicin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 100.

Gwamnatin Rasha ta bayyana cewa ta tabbatar da cewa wadanda suka ta da wannan fitina suna da alaka da kungiyar ’yan a-ware na Chechenya.

Jami’an tsaro sun ba da sanarwar cewa jama’a su ci gaba da zama a gidajensu, sannan kuma an umurci iyaye da su kwaso ’ya’yansu ’yan makaranta daga makaranta zuwa gida.

Sai dai mutanen kasar na gani cewa harin da jami’an tsaro ke kaiwa ya fi daukar rayukan ’yan kasa wadanda ba su ji ba ba su gani ba fiye abin da wanda suke cewa ’yan tawayen na yi.

Haka nan kuma a halin da ake ciki yanzu fadan ya fara watsuwa zuwa wasu sassa na baki dayan kasar Rashan.

An yi taron tunawa da Ranar tona asirin Amurka a Iran

A daidai ranar 13 ga watan ‘Aban’ shekara ta 1358 Shamsiyya daidai da 4 ga watan Nuwamba shekara ta 1979, wato watanni bakwai bayan cin nasarar juyin Musulunci a kasar aka mamaye ofishin jakadancin Amurka da ke kasar Iran.

’Yan watanni bayan cin nasarar juyin Musulunci a Iran, bayan kafa gwamnatin rikon kwarya ta Mahdi Bazargan, Amurka a lokacin shugabancin Jimmy Carter, ta yi amfani da wasu munafukai a cikin Iran wajen yunkurin kifar da sabuwar gwamnatin ta Musulunci, saboda haka ya zama ofishin jakadancin Amurka a Tehran tamkar wani sansani na shiryawa da kuma aiwatar da makirce-makircen ta da fitinu a Iran.

Ana cikin haka ne wasu dalibai na Jami’a wadanda suka kira kansu dalibai masu goyon bayan tafarkin Imam Khumaini (RA) suka shirya, kuma suka aiwatar da mamayar ofishin jakadancin, tare da kame jami’an ofishin har na tsawon fiye da shekara daya.

A wannan lokacin ne aka ci karo da dimbin takardu na asiri na irin yadda Amurka take aiwatar da ta da fitinu a kasar da kuma wasu kayyakin aiki masu karfi wajen sadarwa ta yadda suna iya daukowa da kuma aika dukkanin maganganun jami’an Iran.

Wannan ya kara gaskata irin abin da dadewa ake hasashe na cewa ofishin wata sheka ce kawai ta leken asirin kasar Amurka a Iran.

Marigayi Imam Khumaini (RA) ya yabi wannan yunkuri na daliban, har ma ya kira shi “juyin-juya-hali na biyu wanda ya fi na farko.”

Ta’addancin Yahudawa ya kai ga shahadar mutane biyu a Gazza

A ci gaba da ta’addancin Yahudawa a yankin Gazza, a ranar Talatar makon shekaranjiya ne, sojojin Yahudawan haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai wani hari a arewacin Gazza, wanda ya yi sanadiyyar shahadar wasu manyan jami’an masu fafatawa da Yahudawa guda biyu.

A wani hari na makamai masu linzami da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai ne a kan motar ‘Jeep’ da ke dauke da jami’an a sansanin ’yan gudun hijira a Jabaliya, ya kai ga shahadar mutane biyun.

Rahoton tashar talabijin na BBC, ya bayyana cewa; wasu mutane biyar ma sun jikkata a lokacin da aka kai harin.

Wannan dai shi ne karo na biyu da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai hari kan yankin na Gazza a cikin wannan makon.

Hasan Madhun, wani jami’i na kungiyar Aqsa Brigade, wanda dama jami’an haramtacciyar kasar Isra'ila ke nema suna tuhumar sa da shirya kai masu hari, yana cikin wadanda suka yi shahada a harin.

Fiye da shekaru 50 da suka gabata dai Yahudawan Sahayoniya suka mamayi Palasdinu, tare da taimakon gwamnatin Britaniya ta wancan lokacin.

Ayatullah Khamena’i ya gana da shahidai masu rai

Jagoran juyin-juya-hali na Musulunci a Iran, Ayatullahi Sayyid Ali Khamena’i ya yi wata ganawa ta musamman da Shahidai masu rai, tare da iyalansu wadanda suka sami raunuka a lokacin yakin kare kasa, yayin da suka kawo masa ziyara a gidansa.

Su dai wadannan Shahidan masu rai da suka gana da Sayyid Khamena’i suna cikin wadanda rauninsu ya kai kashi 70 cikin 100 na kimar da ake yi wa wadanda suka ji rauni a lokacin yakin.

Da ma dai a kasar Iran shahidai masu rai suna da darajoji daban-daban ne, akwai wadanda ake cewa kashi 10 cikin 100, akwai kuma wadanda suka fi haka, kowanne gwargwadon yadda raunin da ya ji ya lalata jikinsa ake ajiye shi.

A lokacin da yake gabatar da jawabi a lokacin ziyarar, Sayyid Ali Khamena’i ya bayyana cewa yana daga cikin manufofin tsarin mulkin Iran kariya da kuma taimaka wa Shahidai masu rai, kuma zai ci gaba da zama a haka har abada.

Ayatullah Khamena’i ya kara da cewa; Shahidai masu rai suna da wata falala wadda Shahidan da aka kashe ba su da shi, wannan kuwa shi ne su suna raye a wannan duniya, saboda haka in har suka ci gaba da hakuri da dauriya a kan bautar Allah, a kowane lokaci ana ci gaba da kara masu lada da daukakan daraja ne.

Da yake magana game da yadda iyalai, musamman ma matan Shahidai masu rai suke tarayya da masoyansu cikin dukkanin wahalhalun da suke ciki, Ayatullah Khamena’i, ya nuna cewa tabbas su iyalan za su yi tarayya da su cikin lada.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International