Almizan :Batun adawa da bukin nuna tsiraici na Abuja Jinjina ga kungiyar Kiritoci ta CAN ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 24 Shawwal, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Daga I-Mail

Batun adawa da bukin nuna tsiraici na Abuja Jinjina ga kungiyar Kiritoci ta CAN

Daga Adamu Adamu

Kungiyar kiristocin Nijeriya, CAN, wacce take kamar lema ga duk kungiyoyin kiristoci a kasar nan ta cancanci yabonmu da addu’armu. A kan gaban dukkan kungiyoyin addinai da dukkan sarakunan gargajiyar kasar nan, CAN ta fito fili ta bayyana adawarta ga bukin Abuja Carnival 2005, wani bukin kwanaki uku na nuna tsiraici da maguzanci da aka shirya soma wa a babban birnin tarayyar kasar nan kimanin makonni biyu daidai daga yau (ranar buga wannan mukalar).

Sakataren CAN, Mista Samuel Salifu ya ce tuni wata wasikar neman a soke wannan bukin tsiraici, sun aike ta zuwa ga Ma’aikatar al’adu da yawon shakatawa, “Coci na adawa da nuna mata tsirara a kan tituna ko kuma nuna su a kafafen watsa labarai saboda illolin yin hakan da ba su da iyaka,” ya ce. “Coci na yi wa bukin kallon wani bala’i da ke dauke da wani bala’in, kuma a bayansa wasu bala’o’in.”

A hakikanin gaskiya kalmomin nan sun yi daidai da abin da jagoranci ya kamata ya kunsa, don haka ya kamata a yaba wa CAN saboda cika alkawarinta ga Ubangiji da mabiyanta. Kodayake shugabanni na addini suna da hakkoki da yawa da ke kansu, amma mafi girma da muhimmanci wanda ke bukatar tabbatarwa cikin gaggawa shi ne kiyaye dabi’un jama’a.

Bugu da kari dole a taya CAN murna saboda bajintar da ta nuna na fitowaili ta sha bambam bainar jama’a da matakin Shugaban da ake ganin na kusa-kusa da ita ne. Ta tabbatar da cewa ba ta fama da matsalar da kan hana sauran kungiyoyin addini yin abin da ya kamace su na kiyayya da manufofin gwamnati marasa kyau. Wannan wata dabi’a ce da ya kamata a karfafa.

A irin wannan hali abu ne mawuyaci a zaci cewa kungiya kamar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ko Majalisar koli ta addinin Musulunci (NSCIA), za su iya fitowa fili su yi adawa a bayyane ga Shugaba mai ci, musamman idan shi musulmi ne, ko da kuwa yana take dokokin Ubangiji.

In ma har sun yi adawar, to za ta zama shawara ce ta sirri. Amma shawarar sirri kuwa ya kamata a ce ana yin ta ne kawai a kan kauce hanyar da ya shafi dabi’ar mutum a kashin kansa. Amma shi wannan buki wani abu ne da aka shirya shi don ya lalata tarbiyyar jama’a. Bai kamata su bar duk wata kara ko dabi’ar girmama shugabanni ta hana su aiwatar da hakkokin da ke kansu na jama’a ba. Wannan kasa bai kamata ta kasance tana nuna kara ga shugabancin da ba ya girmama kansa balle talakawansa ba.

Yau, kai ka ce ’yan Nijeriya na kwarai masu mutunci wadanda sune majoriti ba su da wakilci a Majalisosin kafa dokoki na kasar da kuma gwamnati. Ba wanda ke maganar abin da mutanen wannan kasar nan ke bukata ko kuma ma dai abin da ya kamata a ce yana aukuwa. Shugaban kasa ya dage sai ya kawo tsiraici na zamani ga Nijeriya, kuma dole kowa ya bi shi a haka.

Ina Sanatocin da suka yi kamfen na neman kuri’un jama’a da sunan Ubangiji? Ina membobin majalisar Wakilai ta tarayya da suka yi imani da Allah da ranar karshe? Ina ministoci da manyan jami’an gwamnati da kyawawan dabi’u na jama’a wani muhimmin batu ne a wajensu? Me ya sa dukkaninsu suka yi watsi da jama’a?

Ina Gwamnonin da suka sa Ubangiji a gaba a harkokinsu? Mu kaddara cewa CAN ta yi magana ne a madadin Gwamnoni kiristoci, zan so in tambayi Gwamnoni musulmi wasu ’yan tambayoyi kamar haka: Zan fara da Gwamna Alhaji Attahiru Bafarawa, wanda ya nuna rashin tsoron Shugaba Obasanjo a baya, ina ka shige ne ya kai mai girma?

Idan har za ka iya gaya wa Shugaban kasa gaskiya a taron Arewa Consultative Forum, kuma ka ci gaba da yin haka nan a wurare da dama, me ya sa kalmomin gaskiya suka kasa fitowa daga gare ka a yau? Ko ko kai da gwamnatin jihar Sakkwato suna shiri a hurumin Shehu Usmanu Dan Fodiyo, na nuna irin wannan buki na musamman? Kuma shin za ka bar Magajin Garin Sakkwato ya jagoranci mai martaba, Sultan na Sakkwato a zuwa wannan gidan tsiraici?

To kuma ina Malam? Ina farin jini da takawa da sadaukar da kan da aka san ka da su? Shin kana cikin bukin ko ba ka ciki? Idan har matsin lambar ta yi yawa da tilas sai Gwamnatin jihar Kano ta shiga bukin, to wane irin SAHU, Bala Muhammad yake DAIDAITAWA kenan? Kuma ga wane SAHU Makaman Kano zai jagoranci mai martaba San Kano? Yanzu ba abin kunya bane a ce shugabanninmu an kaskantar da su zuwa ga matsayi na tozarcin kyawawan al’adu?

Kuma ina Gwamna Abdulkadir Kure - daya Malam din? Idan a zazzafar siyasar 2003 kai kadai ka tsaya kyam a adawa da Obasanjo, to me ke faruwa a yau? Yanzu a zamaninka ne mai girma, Gidan Dendo za ta kwance zaninta na Zunye, ta yi rawa tsirara a kasuwa?

Rahotannin farko na nuna cewa Sarakunan gargajiyar Katsina tuni suka shiga sahun gaba a shirye-shiryen wannan bukin tsiraici. Allah ya sa dai wadannan rahotannin ba gaskiya bane. Don kuwa bai dace ba a ce gidan Dallaji ne suka shiga cikin wannan shirgi ba. Me wadannan shugabannin Katsinawa na yanzu za su gaya wa Wali Dan Marina in sun gamu da shi a Aljanna? In an bar su sun shiga fa kenan. Har ila yau ina Waziri M. Sani Abubakar Lugga? Shin ba wani babban abin kunya bane idan har Mutawallen Katsina, Alhaji Umaru Musa ’Yar’adua ya rasa inda zai jagoranci Mai martaba sai zuwa wannan dandanmali na sake dawowar bautar gumaka?

Kowa saboda tsoro, ya yi shiru, ya nemi matsuguninsa a cikin wadannan rukunin mutane guda uku. Na farko wadanda suke so wannan buki na tsiraici ya wakana, saboda suna ganin damuwa da al’amuran addini da kyawawan dabi’u a matsayin wani abu na ci baya. Na biyu wadanda ba sa son abin da ke faruwa amma suna tsoron a gan su suna adawa da Shugaban kasa. To wannan babban abin takaici ne.

Amma wadannan rukunoni na mutane guda uku ba su ke nan ba kawai, saboda akwai wadanda a shirye suke su yi adawa da wannan bukin tsiraicin, kuma in ta kama har da gwamnati a kan wannan batu. Matsalar ita ce ba su ma san cewa irin wannan mummunan buki zai auku ba.

Misali kwanaki biyu baya, daya daga cikin jigogin Jama’atu Nasril Islam da Majalisar koli ta addinin Musulunci ya gaya min yadda ya girgizu da ya ji cewa irin wannan mummunan buki zai auku – amma ya san haka ne kawai a ran da muka yi magana, wato kwanaki biyu baya. Amma duk da haka wuri bai kure ba na yin koyi da kyakkyawan misalin da kungiyar kiristocin Nijeriya ta bayar. Amma dai na san yin hakan ba abu ne mai sauki ba.

A sarari yake cewa ba karamin matsin lamba gwamnatin tarayya ta yi wa Gwamnoni ba, kuma ba karamin matsin lamba wadannan gwamnonin da suka firgita suka yi wa Sarakunan ba. Amma abin takaicin shi ne Shugabanninmu sun manta yadda ya kamata su ce ‘na ki’ ga masu mulki na wucin-gadi ko da kuwa iyakokin Ubangiji ne suke takewa da gangan.

Kodayake muna iya fahimtar halin da Sarakunan gargajiya ke ciki na rashin ikon aiwatarwa, amma ya kamata su gane cewa batun kyawawan dabi’u wani abu ne da mafi yawan al’ummar kasar nan a shirye suke su hau kan tituna don nuna rashin amincewarsu ga irin wannan mummunan al’amari da ba shi da goyon baya ko kadan. Kuma ya fiye musu su kasance tare da jama’arsu, domin a irin wannan al’amari gwamnati ba za ta iya yi masu komai ba. CAN fa ba ta da wani iko na aiwatarwa, amma dubi irin abin alfaharin da ta yi. Ya kamata su nazarci abin da CAN ta yi.

Dangane da abin da ya shafi bukin tsiraici na Abuja Carnival, muna iya cewa kungiyar kiristoci ta Nijeriya ta sauke nauyin kasar nan da ke kanta. A guna, Dk. Samuel Salifu shi ne mutumina na wannan makon. Yanzu Jama’atu Nasril Islam, Majalisar koli ta addinin Musulunci a Nijeriya da Majalisar Malamai, da Sarakunanmu aka sa wa ido a ga abin da su kuma za su ce kan haka.

Adamu Adamu sanannen marubuci ne a jaridar Daily Trust. Kuma an buga wannan mukalar ce a ranar 11 ga Nuwamba, 2005. Editanmu ne ya fassara.

Abin da ya kamata al’umma ta sani game da ‘Abuja Carnival’

Daga Malam Muhammad Turi

Daga jiya Alhamis ne (lokacin mun shiga dab’i) ake sa ran fara wasannin al’adun gargajiya da ake masa lakabi da ‘Abuja Carnival.’ Ganin yadda gwamnati ta jajirce a kan lalle sai ta yi wannan taron, duk da kuwa kwatan jama’ar kasar nan suna Allah wadai da shi ne, ya sa Wakilanmu Aliyu Saleh, Hasan Isiyaku da Ali Kakaki suka nemi jin ta bakin Malam Muhammad Turi game da taron. Ga kuma abin da ya ce.

ABIN DA AKE NUFI DA ‘ABUJA CARNIVAL’

Da farko dai yana da muhimmanci al’umma ta gane cewa shi wannan taro an kira shi da suna ‘Abuja Carnival.’ Idan aka ce ‘Carnival’ akwai abin da ake nufi. Akwai ka’ida kamar yadda muka sani, masu magana suna cewa; ‘bambancin sunaye, dalili ne na bambancin ma’ana.’ Saboda haka duk taron da aka ambace shi da suna kaza, to wannan yana nufin akwai abin da ake nufi a aiwatar a wajen taron mai yanayi iri kaza. Abin da ya kamata al’umma su gane a nan shi ne duk taron da aka ce masa ‘Carnival,’ duk wanda ya san wannan ma’anar ya san cewa taro ne na fitsara da tsiraici da rashin mutunci; wannan shi ne mana’ar ‘Carnival.’ Kuma akwai tarurruka shahararru a duniya wadanda ake cewa ‘Carnival.’ Daga cikin wadanda suka fi shara akwai na Barazil, wanda ake yi a Rio de Juneiro a cikin watan Fabarairu, duk shekara ana yi. A wajen wannan taron miliyoyin tantirai ne suke haduwa duk shekara su yi ta shaye-shaye da fasadi iri-iri, wannan sanannen abu ne a duniya.

MANUFAR YIN WANNAN TARON

Ya kamata ya zama yana da wani takamaimen suna, da ya dace da abin da aka ce za a yi, amma idan aka ce ‘Carnival’ ai zance ya kare. Misali ba yadda za a yi a ce za yi kwallon kafa, sannan a ga ana karatu. Dole ya zama dama da akwai abin da ake so a cimmawa, ko da kuwa sun ce za su kawo batun al’adu na gargajiya da suransu, karshenta dai ba za ka rasa wadannan abubuwan na fitsara ba. Ta yiwu ma a yi abubuwa na tsiraici da sunan cewa duk dai ana nuna al’adun gargajiya ne. Idan ana so ne a yi taro na gargajiya ne, kuma akan yi daga lokacin zuwa lokaci daban-daban a fadin kasar nan. Amma shi wannan sun ce suna so ne su yi shi a yadda aka san shi a sauran kasashen duniya. Amma manufarsu shi ne su yi taro, wanda ya dace da irin rurrukan da ake yi a duniya. Makasudinsu wai shi ne a samu kudaden shiga, suna kuma so su jawo ’yan yawon bude ido na duniya. Abu ne sananne duk inda aka ce maka za a yi taro don jawo ’yan yawon bude ido, kowa ya san irin fitsarar da ake yi a wajen wannan abin da suke ce wa ‘Toursim.’

GWAMNATIN OBASANJO

Abin da ban takaici da ya zama ita wannan gwamnatin ta Obasanjo kullum sai abubuwa na rashin mutunci take kulla wa mutane a wannan kasar. A shekarun baya karfi da yaji suka nemi su dankara wa mutane batun taron sarauniyar kyau, mutane suka ce ba sa bukata. Yanzu ga shi sun sake bullo da wani abu kuma. Kullum ba sa yin abubuwan da za su amfani mutane da sauransu, sai dai kawai su yi ta yi wa mutane abubuwa marasa amfani. Halin da ake ciki yanzu abubuwan da ba su dace sun yi yawa, balle kuma a zo a kara karfafa su. Maimakon a je ana barnata kudade a kan abubuwa wadanda za su rusa tarbiyya, ya kamata a yi mafani da wadannan kudaden wajen gina makarantu da kuma sauran abubuwa na tarbiyya.

SAKO GA MASU SHIRYA ‘ABUJA CARNIVAL’

Sako ga su wadannan mutane ba zai wuce lalle wannan abu da suke yi su sani na farko ba dai suna yi ne ba da yawun al’ummar kasar nan. Abu na biyu kuma suna kara bayyana kawunansu a matsayin su marasa mutunci ne, a ce duk a duniyar nan sun rasa abin da za su shirya wa al’ummar nan sai tarurruka na shirme, rashin mutunci da rashin sanin ya kamata. Saboda haka ko ba komai su sani suna cikin mutane marasa mutaunci. Abu na uku kuma shi ne, wannan yana kara karfafa gwiwar mutane ne a kan su nuna masu rashin amincewa. Suna karfafa gwiwar mutane ne a kan lalle ya dace a yi masu bore. Abin da ya faru kenan a wancan karon lokacin da suka shirya gasar sarauniyar kyau, aka yi ta bayanai suka ki ji, amma da wasu matane suka nuna kin amincewa, suka yi masu bore, ba girma ba mutunci suka fasa shirya taron. Saboda haka wannan taron bai dace ba. Duk wanda yake da hannu a wajen shiri wannan taron na fitsara bai cancanci biyayya ko wata kima ma a cikin al’umma ba. Ba da yawun al’ummar nan ake shirya irin wadannan tarukan ba.

ABIN DA YA KAMATA A YI

Abu na gaba shi ne bai kamata ko da nan gaba ne a yi sha’awar shirya wani taron makamancin wannan na ‘Abuja Carnival’ din ba. Kuma a madadinsa a rika tunanin abubuwan da suke da amfani, maimakon ita gwamnati ta yi ta tsokanar mutane, ta yi ta tsokano abubuwa marasa amfani. Don ita wannan gwamnatin ba ta tunanin me mutane suke bukata, saboda haka suke shirya irin wadannan tarukan. Don da ana la’akari da me mutane suke bukata ba za a shirya irin wadannan tarukan ba. A koyaushe wadansu tsiraru sai kawai su yi ta izgili da tunanin al’umma, ba tare da la’akari da meye ya dace, maye bai dace ba. Suna ta kirkiro abubuwa marasa amfani don kawai suna bin son ransu. Ka ga wannan bai dace ba.

Hausa da Hausanci a karni na 21: Kalubale da Madosa

Daga Abdalla Uba Adamu (auadamu@gmail.com)
GABATARWA

A duk fadin kasar nan, babu al’ummar da ta fi ta Hausawa samun kalubale a kan salsalarta da rayuwarta. Ba wani abu ne ya janyo haka ba illa albarkar da Allah Ya yi wa Hausa da Hausanci, ya zamanto ko ka ga mutum wanda ba Bahaushe ne ba ya yi gogayya da Hausawa, ya iya Hausa, to shi kam zai dauki kansa ne a matsayin Bahaushe. Wannan ya saba da yadda shi Bahaushen yakan dauki kansa, domin komai jimawar da ya yi a wani wuri, to shi har abada a matsayin Bahaushe zai dauki kansa, ba don mazauna wurin ba.

Abin da ya janyo haka kuwa shi ne ganin yadda kasar Hausa ta zama dadaddiyar cibiyar ciniki tsakanin bakaken fatan Afrika na Sudan da kuma Larabawa, wanda ya sa kasar Hausa ta zama wajen zaman mutane da kabilu da yawa domin cinikayya. Su kansu Hausawan ba mazauna waje daya bane; daga Kano zuwa Gwanja, zuwa Salo da Kamaru da Kwango, duk babu inda Hausawa ba su ratsa sun kafa sansani ba. Amma tushensu kasar Hausa, domin nan suke dawowa, komai dogon zangonsu. A dawowar ne suke dawowa da sababbin abubuwa na dabi’u da tadodin al’ummatan da suka hadu da su, suke narkar da wadannan su zama nasu, har ma ta kai a dinga kokwanton ko akwai Bahaushe na asali.

Sannan kuma Hausa (yaren), Hausawa (masu yaren) da kuma Hausanci (akidar masu yaren) sun samu wani babban kalubale a wannan karni na 21 da muka shigo, ba don komai ba sai don ganin yadda igiyar sauyin halayen al’umma suka shafi gundarin rayuwar Bahaushe. Wannan igiyar kuwa ta taho ne da hanyoyin sadarwa na zamani wanda sukan kawo mana salo da yanayin rayuwar wadansu al’ummatai na duniya wadanda wani lokaci muka ga kamar akwai kamanceceniya a salon rayuwarsu da namu.

A kokarin kwaikwayon wadannan al’ummatan ne ake samun babban kalubale a rayuwar Bahaushe ta zamani ta hanyar fimafimai, domin wannan ita ce babbar hanyar da ake haskaka rayuwar al’ummatai kuma ake wakiltar su.

Bugu da kari, nazarin Hausanci sai ya bambanta da nazarin rayuwar al’ummatai (Anthropology) ta yadda kusan kullum an fi karkata ga yaren Bahaushe, maimakon sauran fannonin na rayuwarsa. Sannan kuma ko a nazarin zamantakewarsa, an fi damuwa da haihuwa, rayuwa, mutuwa da bukukuwansa, wato tadodinsa, amma ba akidarsa, wato al’adarsa ba.

A wannan jagoran bayanin, zan yi kokarin in fayyace salsalar Bahaushe da kuma fito da gundarin akidarsa domin fahimtar yadda Bahause yake, da kuma yadda ya kamata a wakilce shi ta kowace hanya in ana son a yi masa adalci.

BAHAUSHE, DAGA INA HAKA?

Babban abin da za a fara tambaya a nan shi ne, wai shin wanene Bahaushe? A nan tambayar tana da ban mamaki, domin ganin cewa babu wata kabila da ake tantamar salsalarta a Nijeriya. Misali, idan aka ce Yarabawa, an san wadanda ake nufi. Amma da zarar ka ce Hausawa, sai a fara musu, domin ana ganin yawan gaurayar al’ummatai, da kuma iya yaren Hausa na mutane da yawa ya sa ba ma za a iya cewa ga Bahaushe ba.

Wannan tunani ya karfafu a bisa nazarin wani mai nazarin harshe da ake kira Joseph Greenberg, wanda ya rasu a Amurka ranar 7 ga Mayu, 2001 yana dan shekara 85. A turbar nazarin da ya gina, Greenberg ya jagoranci ra’ayin cewa babu wata kabila Hausawa, domin su kansu Hausawan, a wajensu kalmar “Hausa” tana nufin yare – misali za ka ji mutum ya ce “ba na jin Hausar wancan mutumin” – wato a nan, Hausa yare ce kenan.

Sannan kuma kusan kowane Bahaushe za ka ji ya ce da kai ai shi ainihin iyayensa Fulani ne, Buzaye ne, Barebari ne, da dai sauransu. Amma kuma in ka tambaye shi ko yana jin wancan yaren na wadannan mutanen, sai ya ce da kai ba ya ji. Wannan shi ke dada dagula Hausa da Hausanci, a rasa ma wai shin wanene Bahaushen?

A wani hasashen an danganta samun kabilar Hausawa da auratayyar al’ummatai daga Afrika ta Arewa, inda zaunannun wadannan wurare suka gauraya da Buzaye, sannan aka samu Hausawa. Wannan kuwa ya faru ne a tsakanin 1050 da 1100. Amma kuma wani manazarcin ya kalubalanci wannan has ashen, inda ya ce babu wata tabbatacciyar hujja da ta nuna samun Hausawa bisa wannan auratayyar al’ummatan. A ganin wannan manazarcin, in an ce “Kasar Hausa,” to ana nufin yankin da ake magana da yaren “Hausa,” ba wai wata kabila ba. Sauran ra’ayin manazarta su ma sun ginu ne a kan wannan ra’ayin. Ta haka, misali, Niven ya ce kalmar “Hausa” asalinta ta Buzaye ce, domin da wannan sunan suke kiran duk wanda ya fito daga arewancin kogin Kwara.

A wannan nazarin, Hausa kalma ce wadda Buzaye ke kiran duk bakar fatar da ke inda Larabawa ke kira Sudan. Abin mamaki, ita wannan kalmar ma tana nufin mutanen Abyssinia, wato Habasha, wanda wannan ya kawo hasashen cewa Hausawa daga Habasha suke; yanzu kam mun gane cewa kiran Hausawa da Hausa, da kuma kiran Habashawa da Hausa, duk aikin Buzaye ne. Sannan kuma yin amfani da kalmar ma kaskanci ne na wariyar launin fatan da Buzaye ke yi wa duk wani baki.

Misali, tunda Hausa tana nufin Bahaushe da kuma Bahabashe, sai aka samu wata danganta ta yadda a harshen Habashanci, “Habshi” na nufin haushin kare. Saboda haka a wajen Buzayen wancan lokacin, duk wanda ke magana da wadannan yarurrukan to Bahabshi ko Bahaushe ne. A takaice dai an daidaita furucin Hausa da haushin kare, wanda kuma su ma Hausawa suna yin haka ga wadansu kabilun, inda in mutum ba ya jin Hausa, sai su ce, “bagware ne.”

Skinner kuwa cewa ya yi, kalmar “Hausa” ta fito daga mutanen Songhai (inda Mali take yanzu) ne, domin sune suke kiran duk kauyukan da ke gabas da su Hausa ko aussa, daga nan ne su “Hausawan” suka ari wannan kalmar suke kiran kansu da ita – wato kafin wannan ba su da wani suna da suke kiran kansu!

Sannan kuma manazartan tarihin kasashen Larabawa sun ziyarci kasar Hausa, amma duk a rubutunsu ba su ambaci kalmar “Hausa ba” a matsayi sunan kabilun da suka hadu da su. Marubuta kamar su Leo Africanus, wanda ya ziyarci kasar Hausa wajen karni daga 1513 zuwa 1515, bai ambaci mutanen da sunan Hausawa ba, sai dai ya ce “Mutanen Kano”, “Mutanen Katsina”, da sauransu. Yarensu kuma sai ya ce suna magana da yaren “Mutanen Gobir.”

Wannan ya nuna cewa jimlar kalmar “Hausa” a matsayin nuni ga wata kabila sabon abu ne wanda bai wuce shekaru 400 ba. Amma kuma akwai daulolin Hausawa da masarautun Hausawa da ake magana da harshen Hausa fiye da shekaru 1000 da suka wuce. Idan haka ne, ashe Hausanci ba a yaren ya tsaya ba, akwai kabila wacce take da salsala. Makala suna “Hausawa” a matayin masu magana da yaren “Hausa” abu ne wanda wadansu suka yi wa Hausawan, amma ba su Hausawan da kansu ba, kamar yadda Hausawa ke cewa da kabilar Igbo, “Inyamurai,” wanda kuma ba haka su Igbo suke kiran kansu ba.

Saboda haka ko da lokacin da Leo Africanus ya zo Kano, daular Kano ta yi fiye da shekaru 500 da kafuwa, kuma da Hausa ake tafiyar da ita. Ashe Hausanci ba yare ne ba, akwai kabila Hausa. A nan na fi karkata ga Muhammad Sani Ibrahim inda ya ce, Hausa suna ne da yake da ma’anar Harshe, da mutanen da suke magana da shi, da kuma kasar da ake magana da shi.

Saboda haka sai mu koma tambayar farko, shin wanene Bahaushe? Amsar a nan ita ce; duk wanda salsalarsa babu wani yaren iyaye sai Hausa, to shi ne Bahaushe. Idan a jerin iyaye da kakanni akwai wanda ba Bahaushe bane, to kai ma ba Bahaushe bane. Na aro wannan ma’aunin bisa cewa Hausanci kirar halitta ce, ba lafazi ba. Misali, a kasar Turawa, in a cikin iyaye da kakanninka akwai bakar fata, to ko ka fi madara fari a matsayin bakar fata kake.

A wannan ma’aunin, babu maganar zama a wata al’umma da kuma sanin yarenka, domin ka zama dan wannan al’ummar (a nan, kabilar). Misali, duk iya Larabcin bakar fatan da ya zauna a garin Makka, ba za a taba kiran sa Balarabe ba, ba wai kawai don akwai bambancin tsakanin fatar Balarabe na ainihi da bakar fata ba, a’a, kawai ba Balarabe bane, kuma shi ma ya san haka. Haka duk iya Turancin bakar fata a Ingila ba za a kira shi Ingilishi ba, sai dai dan kasar Ingila, domin Ingilishi (English) kabila ce a Ingila tare da Sikotawa (Scottish), Irishawa (Irish) da kuma Welshawa (Welsh), kuma duk wadannan Turawa ne, farar fata; babu baki a cikinsu. Su kansu a Ingila din, za ka ji mutum na alfahari da kabilarsa – misali, duk da cewa shi fari ne, amma zai ce maka shi Ba’irishe ne, ba Ingilishi ba. Saboda haka kamar Hausa, in ka ce English, to ana nufin yaren da kuma kabilar. Ta haka za a bambanta cewa; “wannan mutumin British ne, amma fa dan kabilar Welshawa ne”

Bari in dawo gida. Idan, misali wani Bayarabe da matarsa suka bar kasar Yarabawa fiye da shekaru 100 da suka wuce, suka yada zango a wata unguwa a Kano suka yi zuri’a, to komai nisan zuri’ar da wadannan iyayen zuri’a, duk a Yarabawa suke. Halin zamantakewarsu zai iya sa wadanda aka haifa daga baya ba su ma san yaren iyayen nasu na asali ba, sai Hausa. Duk da haka, Yarabawa ne, domin salsalarsu ce. Idan dole sai an dangantasu da Hausa, to a iya kiransu abin da na kirkiro da Hausawan Zamantakewa. Amma ba Hausawa bane, domin Hausa ta wuce yare, kabila ce, tare da al’adunta na musamman, da kuma dabi’o’inta. Mutum zai iya rungumar wadannan domin ya zama Bahaushen Zamantakewa, amma ba zai zama Bahaushe ba, kamar yadda mutum zai iya karbar rayuwar Larabawa domin ya zama dan, misali, Dubai, amma ba zai taba zama Balarabe ba, in ba shi bane.

Idan iyayen salsala sun ki su koya wa zuri’arsu yarensu domin suna son su bace su zama Hausawa (ko kuma mazaunan inda suka sami kansu), wannan ruwansu, amma wannan ba zai kankare musu Yarbancin ba. Mu danganta da cewa komai dadewar Bahaushe a Shagamu, ba zai taba tsammanin shi Bayarabe ne ba. Ta haka za a ga Hausawan Kamaru da Gana da Kwango, misali, wadansu ba sa jin Hausar sosai, ko kuma suna yin Hausar wata iri, amma kowanne daga cikinsu zai danganta salsalarsa da wani gari a kasar Hausa.

Wannan yana daga cikin ban mamakin albarkar da Allah ya yi wa Hausa da Hausawa – kullum wadanda ba Hausawa sai so suke a dauke su a matsayin Hausawa, duk da cewa suna da tasu kabilar – da akidodin – wacce ya kamata su daukaka.

Za mu ci gaba insha Allah.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International