Almizan :Malama Zeenatuddeen ta ziyarci Suleja ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 24 Shawwal, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Rahotanni

Malama Zeenatuddeen ta ziyarci Suleja

Daga Magaji Alhaji Idi Zariya

H

A ranar Lahadi ne 12/10/1426 (13/11/05) ne aka kammala taron Mu'utamar na kwanaki biyu da ’yan uwa mata na garin Suleja suka shirya.

Bukin rufe Mu’utamar din, wanda ya sami halartar ’yan uwa masu yawa na yankin, Malama Zeenatuddeen Ibrahim ce ta albarkaci rufe shi.

Cikin jawabinta a wajen taron, Malama Zeena ta fara ne da karfafa wa ’yan uwa gwiwa a kan Harkar gwagwarmaya, da kuma nuna musu cewa ko da mutum ba shi, to za a yi Harka.

Malama Zeenatuddeen Ibrahim ta ci gaba da cewa “in ka dubi wadanda ake wannan Harka da su duk gaba dayammu, to wadanda aka fara Harka da su na tun farko ba su fi a kirga ba. Saboda wasu dalilai da suka faru a cikin wannan Harka, ko dai mutum ya gaji da wannan tafiya ya bullo da wata matsalar da zai dogara da ita ya gudu, ko kuma saboda wasu jarabawowi da suka faffaru. Ka ga wasu ta cinye su, wasu kuma ta kasa cinye su, sai kawai ka ga ya sulale daga Harkar.”

Malama Zeenatuddeen, ta kawo misali da ’yan Zuhudu, wadanda ta ce “su da suka gaji da Harkar sai suka bullo da wani irin tunani na cewa irin su fankan nan, da su darduman nan, ballantana irin su wadannan balan-balan da muka hura duk haramun ne.”

Haka kuma Malama Zeenatuddeen ta jawo hankalin ’yan uwa a game da mujahada ta bangaren addu’o’i. “Duk abin da Malam (Zakzaky) zai koyar da kai, to sai shi ya dade da farawa tukuna. Domin akwai lokacin da Malam ya koya mani wata addu’a a daidai wancan lokaci, shi ya shekara 10 da fara wannan addu’ar,” in ji Malama.

Haka kuma Malamar ta ci gaba da jan kunnen ’yan uwa a game da mayun imani, mashaya jini, masu janye ’yan uwa daga hanya, musamman saboda hassada. Malama Zeenatuddeen ta kawo misali da Iblis inda ta ce: “Iblis ya san Allah, Ya zauna da Mala’iku, Ya yi magana da Allah, Amma saboda hassada ga kakanmu Annabi Adamu (AS) sai ya yi jayayya da Allah. Haka kuma kafiran Kuraishawa ba komai bane ya sa suka ki yin imani da Manzo (S) illa tsabar hassada.”

Haka kuma Malamar ta kawo misali da Amirul MumininaAli (AS), inda a nan ma ta ce tsabar hikidu ne ya hana wasu daga Sahabbai yi wa Imam Ali (AS) mubaya’a.

A karshe Malama Zeenatuddeen Ibrahim ta kawo daya daga cikin mu’ujizar Manzo (S), inda ta ce “duk da tsabar bakin duhun kai, da bakin jahilci, da dabbanci, da dakikancin Larabawan zamanin Manzo (S), amma a kasa da shekaru 30 kacal Manzon Allah (S) ya canza tunaninsu gaba daya. Wannan ba karamar mu’ujiza bace,” in ji Malama Zeenatuddeen Ibrahim.

Mu kaurace wa kayayyakin Yahudawa

Shawarata a nan ita ce don Allah in har da hali ku rinka buga mana sunayen kayayyakin da ya kamata a ce ba ma amfani da su kamar yadda kuka buga a can baya, kamar su ‘coca-cola’ da sauransu. Wato kayan da Yahudawa suke yi ko suke da hannu a ciki.

In da son samu ne, da sai in ce duk sati. To ko da a bayan sati biyar ne sai a rika buga mana.

Don Allah ’yan uwa mu ba zuciyarmu magana, mu kaurace wa kayan Yahudawa. Domin dukkan Musulmi dan uwan juna ne. Wannan ko mutum ya gane ko bai gane ba. Sannan kuma duk inda kafiri yake yana taimakon dan uwansa ne. To mu ma menene zai sa ba za mu taimaki ’yan uwanmu ba? Don haka nake kira ga dukkan Musulmai da su ji tsoron Allah su rika kauce wa irin wadannan kaya.

Ina rokon Allah (S.W.T.) ya saka wa Malam Zakzaky da alheri ya cika masa gurinsa, ya bar mu a tare da shi har abada, albarkacin Iyalan Gidan Manzon Allah (S).

Daga ’Yar uwarku a Musulunci Amina M. Ahmad Dankwaro, Karamar Hukumar Kafur jihar Kastina

Mu bubbude shafukan ‘Sakar Sama’

A watannin baya ne ina sauraron wani shirin gidan rediyon FREEDOM FM da ke Kano mai taken; “Mumbarin Malamai,” inda suka gayyato wani Malam Bashir Aliyu Umar ya gabatar da shirin mai taken “Intanet Da Duniyar Musulmi.” A cikin shirin Malam Bashir Aliyu Umar ya fada wa masu sauraro cewa da akwai wata sakar sama (website) da wani dan uwa ya bude mai suna www.ahlulbaiti.com domin yaki da wata akida da ta shigo wannan kasa!

Ina kan ‘Intanet’ sai na tuno da zancen Malam Bashir A. Umar na nemi ahlulbaiti.com . Da na budo shafin sakar saman (website) na sha mamakin yadda da gangan ake kokarin canza tarihi, shara karya, sharri, kazafi da kokarin ta da fitina.

A shafin nasu (ahlulbaiti.com) suna ta kokarin tunzura mutane a Nijeriya su dauki makamai su auka wa ’yan Shi’a da kiristoci. Ga adireshin shafin a nan, a bude a gani; http://www.ahlulbaiti.com/index.htm.

Don haka zan yi amfani da wannan damar in yi kira ga ’yan uwa su shiga harkar da’awah, musamman ta hanyar sakar sama domin bayanin menene Shi’a, ba wai a zuba wa masu adawa da Shi’a ido suna bayanin menene Shi’a ba.

Ina kira ga Jaridar ALMIZAN ta bude shafin sakar sama mai bayanin akidar Shi’a tsantsa, haka ma ga masu shafin sakar sama na Harkar Musulunci. Ina kuma kira da babbran murya ga kungiyoyin Shi’a a Nijeriya kamar su Ahlul-Bait (AS) Community, Gombe, Dar-Al-Thaqalyn, Rasulul Akram da sauransu da Mujallar AL-MAUZUUN, da ’yan uwa kamar su Shaikh Nura Dass, Shaikh Bashir Lawal Zariya, Shaikh Saleh Zariya, Shaikh Yakubu Ningi, Shaikh Hamza Lawal, Shaikh A.A Mubarak, Shaikh Hafizu Kano da masu kulawa da rubucen-rubucen Marigayi Shaikh Awwal Tal’udi da sauran ’yan uwa masu rubuce-rubuce da su bude shafukan sakar sama (websites) domin isar da sakon rubuce-rubucen da suka yi a kan Mazahabar Ahlul-Baiti (AS). ’Yan uwa kuma su daure su bubbude majalisu (groups) a intanet domin isar da sakon Ahlul-Baiti (AS) ga duniya baki daya.

Yanzu muna cikin wani yanayi ne mai ban tsoro, domin wasu mutane sun dage sai sun hana da’awar Ahlul-Baiti (AS) a wannan kasa isa kowane loko. Kwanakin baya aka kaddamar da ’Yan Hisbah har 9,000 a Kano. Shin kan manufar kafa su kawai za su tsaya ko kuwa, a’a? Domin kowa ya sani wasu daga cikin shugabannin Hisbah a Kano makiya ne na Mazhabar Ahlul-Baiti (AS) na ga-ni-kashe-ni. Kuma har yanzu Gwamna Shekarau bai janye kazafin da ya yi wa Mazhabar Ahlul-Baiti (AS) ba, balle ya nemi afuwar duniyar Musulmi, duk da kiraye-kirayen da al’ummar Musulmi suka yi masa. Daga Muhammad Sakafa Kano (muhammadsakafa@yahoo.com)

An kammala taron IVC cikin nasara

Isa Almusawi Gombi (musawiy@yahoo.com)

A kwanakin baya ne aka ya bikin rufe taron IVC karo na uku wanda Kungiyar Dalibai Musulmi ta kasa (MSS) reshen jihar Adamawa ta shirya aka yi taron a makarantar GMMC Ramat, Yola, inda aka kwashe kwanaki hudu ana yin taron.

Babban bako mai jawabi a wajen taron shi ne Alhaji AbdulRasheed Ibrahim na Savanna Sugar Company Numan, inda ya gabatar da jawabi mai taken: “Lalacewar dabi’u tsakanin al’ummar musulmi. Ina mafita?”

A cikin jawabin nasa, wanda ya yi tasiri sosai ga mahalarta taron, Alhaji AbdulRasheed Ibrahim, ya ce, al’umma ta lalace. Wadanda suka fi daukar wannan lalacewa kuwa sune masu kudi (mawadata); da masu ilimi (Malamai); da kuma masu mulki (mahukunta).

Ya ci gaba da cewa, wadannan rukunan al’umma sune suka fi taka muhimmiyar rawa wujen lalacewar al’ummar. “Wani abin lura kuma shi ne Yahudawa da Nasara sun yi kokarin yaye hijabin da ke tsakanin jinsin maza da kuma mata. Wannan kuwa zai tabbata ne in ana bukatar ganin shaida shi ne sai a ziyarci makarantun bokonmu, abin da ya kama daga firamare, sakandare har zuwa makarantun da suke gaba da sakandare, inda ake ta bayyana wayewa ta hanyar nuna tsiraici da kuma cakuduwar maza da mata. Wannan dalilin shi ya yawaita zinace-zinace da luwadi da madigo a cikin da yawa daga cikin makarantun gaba da firamare na garuruwanmu.”

Alhaji AbdulRasheed Ibrahim, ya jawo hankalin matasa da su sa lura yayin neman abokiyar zama (aure), ta yadda za a samu zuriya ta gari.

Daga karshe ya yi kira ga masu iko da sukuni, musamman wadanda suka halarci wannan taro da su tashi tsaye wurin gyaran halayen al’umma.

Shi kuwa Honarabul Dahiru Ibrahim Barnoma, dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Yola ta Arewa, Yola ta Kudu da kuma Girei, a nasa jawabin jan hankalin matasa ya yi wurin yin hidima ga wannan addinin na Musulunci, musamman wurin gyaran hali ga wannan al’umma. Ya ce kuma ba wanda zai taimaki wannan addinin in ba matasa ba.

ALMIZAN ta tattauna da Amir din MSS (Adamawa Area Unit), Alhaji Abdullahi Ibn Hamman, inda ya bayyana godiya ga Allah saboda damar da ya bayar har aka gama wannan taro lafiya.

Kuma ya ja hankalin mahalarta wannan taro da su yi aiki da kyawawan dabi’un da suka koya daga wannan bita (taron). Ya yi fatan dalibai za su ci gaba da halartar makamantan wannan taron, wanda mahalarta tsakanin maza da mata suka kai adadin 560. Yana mai cewa tunda suka fara wannan taron nasu har suka gama ba su samu wata matsala ba.

An kama wani Malami saboda ya soki Yahuduwa

Ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar Austriya ta tabbatar da kame wani masanin tarihi dan asalin kasar Biritaniya, wanda ake zargi da laifin karyata tarihin kisan kiyashin da aka ce an yi wa Yahudawa, wato 'Holocaust' a lokacin yakin duniya na biyu.

An kame masanin tarihin; David Irvin ne a ranar 11 ga watan Nuwamba na wannan shekarar nan da muke ciki a lardin Styria na kasar Austriya, sannan aka kai shi gidan kaso na yankin Graz.

Kakakin ’yan sandan kasar Austriya, Rudolf Golia ya bayyana cewa an kame Irving ne karkashin dokar kasar ta shekara ta 1989 wadda ta haramta dukkanin wani nau’in nuna kin jinin Yahudawa wato ‘Anti-semitism’ a kasar.

Dama tun a wancan shekarar ta 1989 ne wannan masanin tarihin ya gabatar da wani jawabi a Vienna, wanda mahukunta suka bayyana da cewa lalle wannan jawabi nasa zai iya kawo kin jinin Yahudawa. In har aka tabbatar da laifin da ake zargin Irving da shi zai iya fuskantar dauri a gidan kaso na tsawon shekaru 20.

Dama dai a kasashe daban-daban na duniya, musamman kasashen Turai, an haramta dukkanin abin da zai iya kawo kin jinin Yahudawa, sannan kuma yanzu haka Majalisar Dinkin Duniya ta amince da a rika tunawa da tarihin kisan gillar da aka yi wa Yahudawa a lokacin yakin duniya a kowace shekara.

An sa ranar fara jigilar Alhazai daga Nijeriya

Ranar 17 ga watan Disamba mai zuwa ake sa ran fara jigilar Alhazai zuwa kasar Saudiyya don gudanar da aikin hajjin bana.

Shugaban kwamitin harkokin zirga-zirgar jiragen sama na kwamitin aikin hajji na kasa, Dakta Badmus Yusuf ne ya shaida wa manema labarai haka a Ilori a kwanakin baya.

Ya ce kwamitin ya riga ya biya kafin alkalamin da ake bukata don samar da masaukai ga daukacin Mahajjatan Nijeriya a biranen Makka da Madina, sannan kuma an kulla yarjejeniya tare da kamfanonin jirage uku da za su yi jigilar Alhazan kan za su bari a duba lafiyar jiragensu kafin su iso kasar nan don gudanar da jigilar.

Ya ci gaba da cewa; “domin kauce wa abubuwa marasa dadi da suka faru a baya, “za mu je mu duba lafiyar jiragen a wuraren da suke kafin a kawo su Nijeriya.” Ya ce, hadarin jirgin sama na baya-bayan nan da aka yi wani hannunka mai sanda ne ga masu tafiyar da aikin hajji a kasar nan, “don haka dole ne mu yi duk abin da ya wajaba don kare lafiyar Mahajjata.”

Ya yi gargadi game da makaro kaya fiye da ka’ida da Alhazai ke yi, inda ya ce, akwai bukatar kowane Alhaji ya kasance mai da’a tare da ba kwamitin aikin hajji na kasa hadin kai, “ba za mu lamunci wani ya dauko kaya fiye da kilo 40 da aka kayyade ba.”

Dakta Yusuf ya ce, daukacin filayen jiragen sama za su kasance cikin hada-hada lokacin jigilar Alhazan. Kuma filayen jiragen da za a kwashi Alhazan a bana sun hada da na Abuja, Ilori, Kano, Kaduna, Maiduguri, Legas da kuma Fatakwal.

Ya ce rufe karamin ofishin jakadancin Nijeriya da ke Jeddah ba zai kawo matsala ga tafiyar da aikin hajjin ba, domin a suna ne kawai aka samu sauyi, amma akwai matsakaicin ofishin jakadanci yana nan zai ci gaba da aikinsa.

Editocin jaridu da mujallun Hausa sun samu kungiya

Wasu Editocin jaridu da mujallun Hausa kamar guda takwas sun hadu a babban birnin jihar Zamfara, Gusau sun kafa wata kungiya mai suna Tarayyar Editocin Hausa a ranar Litinin din makon jiya.

Editocin da aka yi zaman farko na kungiyar da su sun hada da na jaridar Gaskiya ta fi kwabo, Gamzaki, Jagora, Dillaliya, Hantsi, Almizan, da kuma na mujallar Fim da Garkuwa.

Kafa wannan kungiya, kamar yadda Shugaban kungiyar na riko, Malam Tukur AbdulRahman na jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ya bayyana, ta biyo bayan tuntubar juna da kuma tattaunawa da Editocin suka yi tsakaninsu na tsawon lokaci, inda suka amince da bukatar haduwa a karkashin wata inuwa guda don ciyar da aikinsu gaba.

Manyan manufofin kungiyar kamar yadda Shugaban rikon ya ce, sun hada da nemo hanyoyin da za a inganta aikin jaridu da mujallu da harshen Hausa da kuma kara yawansu a kasar nan. Haka nan kuma wannan kungiya za ta sanya ido wajen tabbatar da cewa, masu rubutu a jaridu da mujallun Hausa suna bin ka’idar aikinsu, in ji shi.

Ya kara da cewa, kungiyar za ta yi iyakar kokarinta na ganin sauran editocin jaridu da mujallu da ba su halarci taron farko ba sun shigo cikin kungiyar ta yadda za a wayi gari ana ba jaridun Hausa irin kimar da ake bai wa na Turanci.

Editocin sun amince da zaben Alhaji Lawal Maikudi na jaridar GAMZAKI a matsayin Sakataren riko, yayin da suka aje Kaduna a matsayin cibiyar kungiyar. Taken kungiyar shi ne “kowane tsuntsu kukan gidansu yake yi.”

’Yan uwa na Bichi sun gabatar da muzaharar Kudus

Daga Muhammad Sakafa Kano (muhammadsakafa@yahoo.com)

Kamar yadda sauran al’ummar musulmin duniya suka amsa kiran Imam Khumain (RA) na gabatar da muzaharar Kudus a duk Juma’ar karshe ta watan Ramadan, su ma ’yan uwa almajiran Malam Ibraheem Zakzaky (H) na garin Bichi a jihar Kano ba a bar su a baya ba, domin sun amsa kiran wajen gabatar da muzaharar ta Kudus ta bana a garin na Bichi, wanda Wakilin ’yan uwa na garin Malam A. Yusuf ya jagoranta a ranar Juma’ar bayan salla 10 ga Shawwal da ta gabata.

Muzaharar ta fara ne da misalin karfe 2;30 na yamma bayan idar da sallar Juma’a daga babbban masallacin garin na Bichi, inda aka ratsa manyan titunan cikin garin.

Goshin muzaharar ya fara hawa kan titin mahadar Unguwar Hagagawa ne, inda aka bi ta kofar gidan Hakimin garin, sai aka ratsa ta Unguwar Ciciya, sai aka bi ta Unguwar Zango ta jikin gefan masallacin Abdullahi Farar Hula, aka fito ta kofar Sidi Ahmad, aka hau kan titin Kano/Katsina aka fado Unguwar Sabon Gari aka kitse hancin muzaharar a Tsohuwar Tasha.

Muzaharar, wadda aka kawata ta da hotunan Malam Ibraheem Zakzaky da na Imam Khumini ta kayatar ainun, inda ’yan uwa suke taku irin na Hizbullah idan sun fito kwami da Yahudawa, suna silogan kan kwato Masallacin Kudus, tare da tsinuwa ga uwar shidanu Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila da sauran ’yan barandarsu.

Wakilinmu, wanda ya yi tattaki har garin na Bichi don ganin yadda za a gudanar da wannan muzaharar, ya rawaito mana cewa, muzaharar ta kayata fiye da yadda aka zata, inda ya ji jama’a da dama suna fatan alheri ga ’yan uwan, tare da yi wa Malam Zakzaky addu’ar Allah ya saka masa da alheri, kai wani wani mutumin da ya je kallo har cewa yake; “Allah ya kai mu ran da za a je ’yanto Masallacin Kudus. Wallahi da mu za a je,” in ji shi.

Bayan kare muzaharar ne sai Wakilin ’yan uwa na Bichi Malam A. Yusuf ya gabatar da jawabin rufewa, inda ya jawo hankalin mutane kan mahimmancin kwato Masallacin Kudus, inda ya ce; “shi wannan Masallaci na Kudus shi ne Masallaci na uku a daraja a wajen al’ummar musulmi, amma abin takaici yanzu yana hannun Yahudawa, duk da cewa kwato shi ya zama wajibi,” in ji shi.

Malam A. Yusuf ya kara da cewa; “kuma su wadannan Yahudawan suna ta kashe musulmi a duniya, misali bom din da aka tayar a Jordan, amma aka ce wai musulmi ’yan Alka’ida ne suka tayar da shi. To wannan mun san karya ne.”

Daga nan ’yan uwa sun kona tutar haramtacciyar kasar Isra’ila da ta Amurka, sai Malamin ya rufe da addu’a aka watse.

Bayan sallar isha’i kuwa, ’yan uwa sun shirya wa’azi a kofar gidan Malam A. Yusuf, Wakilin ’yan uwa na garin, wanda shi da kansa ya gabatar da jawabi a wajen, kan Masallacin na Kudus.

A wajen taron, shahararren mawakin nan na gwagwarmaya, Malam Gambo Dankaka ya yi wakoki masu tarin yawa, inda su kuma ’yan uwa suka yi ta lika masa kudade. ’Yan uwan da suka hada da maza da mata ne suka taru a wajen majalisin.

’Yan fashi sun farmaki Farfesa Ibrahim Ayagi a gida

A karshen makon da ya gabata ne dai wasu ’yan fashi da makami suka kai wani hari gidan babban masanin ilmin tattalin arzikin nan da ke Kano, Farfesa Ibrahim Ayagi a gidansa da ke rukunin gidajen Gwale a birnin Kano, inda aka bayyana cewa sun ji masa rauni, amma ya tsira da ransa bayan sun awon gaba da wasu kudade.

Daya daga cikin iyalan Farfesa Ibrahim Ayagi, wanda yake tare da shi a lokacin da ’yan fashin suka kai masa harin, ya tabbatar da cewa lokacin da ’yan fashin suka kai harin sun nemi a ba su kudade, sai dai Ibrahim Ayagi ya ki amincewa da bukatun nasu.

Shi dai gidan Farfesa Ibrahim Ayagi da ke rukunin gidaje na Gwale, yana kimanin nisan mita dari ne daga ofishin ’yan sanda na Unguwar.

Ya zuwa lokacin da muke rubuta wannan rahoton dai Farfesa Ibrahim Ayagi yana samun saukin raunukan da ya samu sakamakon harin da ’yan fashin suka kai masa. Sai dai har ya zuwa yanzu ba mu samu labarin ko an kama wani da ake zargin yana da hannu a wajen kai wa wannan masanin na tattalin arziki hari ba.

A wani labarin kuma, babban Editan jaridar DAILY TRUST, Alhaji Kabiru Yusuf, ya tsira da ransa lokacin da ya ci karo da wadannan fataken daren a kan hanyarsa ta komawa Abuja daga Kaduna, inda ya je domin yi wa Malam Mahammad Haruna, wanda shi mashahurin marubuci ne a jaridar ta DAILY TRUST jajen harin da ’yan fashin suka kai masa a gida farkon shekaranjiya.

Kamar yadda Alhaji Kabiru Yusuf ya bayyana, ’yan fashin sun tare shi ne a garin Jere da ke da nisan kilomita 80 daga babban birnin Tarayya, Abuja, inda suka bukaci da ya ba su makullin motar da yake ciki da kuma duk abin da ke cikin motar, bai yi taurin kai ba ya mika masu motar suka tafi da ita.

Fashi da makami dai a Tarayyar Nijeriya ya zama wani ruwan dare game duniya ta yadda yake babu wanda yake kwanciya gidansa cikin aminci, ko a halin tafiya. Da yawa na ganin daya daga cikin illar yaduwan fashi shi ne irin tsananin rashi da ya addabi al’umma, alhali wasu tsiraru na cikin wadata ta fitar hankali, ga kuma rashin wadataccen tsaro a cikin kasar.

Me ya jawo boren da fursunoni suka yi a Sakkwato?

Daga Abu sumaiyya

A ranar Lahadi 20, ga watan Nuwamba 2005 ne fursunoni a gidan yarin Sakkwato suka tayar da bore a daidai lokacin da Shugaban gwamnatin farar hula ta Nijeriya, Cif Olushegun Obasanjo yake ziyara ta kwanaki biyu.

Boren, wanda mafi yawan masu yin sa fursunoni ne masu jiran shari’a da ake zargi da laifukan fashi da makami, da kuma kisan kai, ya jawo rasa ran mutane uku, lalata dukiya da kuma ji wa da dama rauni.

Shi dai wannan boren an fara shi ne da misalin karfe 7:00 na marecen wannan

ranar. Bayan fara wannan boren ne kuma ’yan sanda, tare da ma’aikatan gidan yarin suka zagaye gidan suna luguden barkonon tsohuwa tun karfe 7 na yamma har zuwa karfe 1:00 na dare ba tare da sun iya samun nasarar kwantar da tarzomar ba. Daga nan ne fa sai wasu fursunoni suka shiga kunnawa wasu wurare wuta, kamar shagon koyon dinki, wasu ofisoshi da kuma dakin ajiyar abinci, inda suka fasa shi suna kwasar abinci zuwa

dakunansu.

Ganin yadda wutar boren ke kara karfi ne ya sanya aka bai wa ’yan sandan kwantar da tarzoma izinin shiga cikin gidan yarin, inda suka rika luguden harsashe har na

tsawon kusan awa daya kafin a karshe su iya samun nasarar kwantar da boren.

A bangaren ’yan uwa musulmi da ake tsare da su a cikin wannan gidan yarin da yawansu ya kai mutum 70, sun samu yabo da sanya albarka daga ma’aikatan gidan, da kuma wasu fursunonin, ganin yadda ’yan uwa suka taru a daki daya suka rinka yin zikiri a daidai lokacin da ake wannan boren ba tare da sun fito ko da daga dakin da suke ba.

Wannan yabon ya kara fitowa fili ne a kashegarin ranar da aka yi boren lokacin da Kwamishinan ’yan sanda da Shugaban SSS da Shugaban gidan yarin, tare da wasu manyan ma’aikatan tsaro suka shiga a cikin gidan yarin suna zagayawa a kowane daki domin zakulo wadanda ake ganin suna da hannu a wannan boren da aka yi.

A lokacin da suka zo dakin da ’yan uwa suke, sai Shugaban gidan yarin ya ce, “a wuce wadannan, banda su a ciki. Allah ya yi maku albarka, kun nuna tabbas ku addini kuke yi. Mun gode maku kwarai.”

Bakuna dai sun rarrabu a kan musabbabin tayar da wannan boren. A bangaren jama’ar gari suna ganin cewa wannan wata makarkashiya ce wadansu suka hada ta hanyar yin amfani da fursunoni domin janyo wa Gwamna Bafarawa bakin jini ga sauran ’yan Najeriya. Yayin da bangaren fursunoni kuwa suke cewa sun yi wannan boren ne domin su nuna bacin ransu ga irin yadda ake tsare da su shekaru shida zuwa goma ba tare da an yanke masu hukunci ba. Suna kuma zargin cewa ba a ba su abinci kamar yadda doka ta tanada. Sannan suna zargin ma’aikatan gidan yarin na Sakkwato da sace suga da kuma shinkafar da aka bayar a cikin watan azumi domin a raba wa fursunonin.

Sai dai a bangaren ma’aikatan gidan yarin, kamar yadda wani daga cikinsu ya shaida mana; suna ganin wannan boren da fursunonin suka yi, sun yi ne domin tabbatar da wani ikirari da suke yi na cewa babu doka a gidan yari bayan karfe 6:00 na yamma.

Ya ce, yadda wannan boren ya fara, ya yi nuni da haka saboda fursunonin da suka yi boren sun fasa dakunansu a daidai wannan lokacin ne, sannan suka shiga fasa sauran dakuna domin sauran fursunoni su fito su shiga cikin su.

Zuwa lokacin hada wannan rahoton dai Hukumar ’yan sanda sun bayar da sanarwar mutuwar mutane uku a wannan boren, tare da jikkata wani adadi mai yawa.

Kazalika an kuma an ba da sanarwar samun nasarar fitar da fursunoni mata wadanda aka ce masu boren sun yi barazanar yi musu fyade.

Duk da sanarwar da Hukumar ’yan sanda ta bayar na adadin wadanda suka mutu, mutanen garin Sakkwaton na hangen cewa adadin ya fi haka, suna cewa yawan mutanen ya zarta haka nesa ba kusa ba.

Tun lokacin faruwar abin zuwa wannan lokacin an tsaurara tsaro a gidan yarin, inda aka hana kowa shiga sai ma’aikatan gidan da kuma jami’an bincike wadanda ke binciken wasu fursunoni da ke da hannu a boren.

Yanzu dai gawawwakin wadanda aka kashe da kuma wadanda aka raunata suna

asibitin kwararru da ke Sakkwato.

Mafi yawan mutane sun ido don su ga wane irin sakamako ne masu binciken za su fitar, da kuma irin matakin da gwamnati za ta dauka domin magance sake faruwar makamancin haka a nan gaba.

Malam Turi ya ziyarci Shehunan Malamai a Kano

Daga Ali Kakaki

A kokarinsa na ganin kan al’ummar musulmi ya hadu sun zama abu guda ta hanyar kusantar juna da sada zumunci, Malam Muhammad Mahmud Turi, Wakilin Shaikh Ibrahim Zakzaky a Kano, ya ziyarci wasu Shehunan Malamai wadanda suka hada da gidan Kadiriyya yayin rufe karatun Ashafa na bana da kuma Shaikh Isah Waziri, Wazirin Kano, da Shaikh Idris Kuliya, babban Limamin Kano.

Malam Muhammad Turi yayin da ya ziyarci gidan na Kadiriyya ya samu kyakkyawan tarbo da nuna matukar farin ciki daga Khalifa Karibullah da ’yan uwansa da sauran mabiyan darikar ta Kadiriyya.

Shi kuwa Shaikh Isah Waziri, Malam Turi ya ziyarce shi ne ranar Juma’a ta farko bayan sallar Edil-Fitr a gidansa da ke unguwar Tudun Wazirci a cikin birnin Kano.

Kuma a karo na uku ya ziyarci Shaikh Aliyu Harazumi da Shaikh Idris Kuliya, babban Limamin Kano.

A yayin ziyarce-ziyarcen, Malam Muhammad Turi ya rika bayyana ziyarar tasa da cewa a madadin harka Islamiyya da ’yan uwa musulmi ya yi domin cika umurnin Allah (SWA) da Manzo Muhammad (SAW) cewa "Mumunai ’yan uwan juna ne," a wani wurin kuma yake cewa"su kasance abu guda kada su rarraba."

Wakilinmu ya shaida mana cewa irin wannan ziyara da Malam yake kai wa ya biyo bayan Bikin Makon hadin kai da Shaikh Zakaky ya fara shiryawa a kasar nan a cikin watan Rabi’ul Awwal (Maulud).

’Yan sanda sun harbe wani magidanci a Kano

Daga Ali Kakaki

A ranar Litinin din da ta gabata ’yan sanda da ke aikin dare a ofishin ’yan sanda na unguwar Shagari Quarters da ke Karamar Hukumar Kumbotso a cikin jihar Kano suka

harbe wani bawan Allah, Malam Salisu Gambo (Majazubi) har lahira babu laifin fari balle na baki.

Yadda abin ya faru shi ne, shi dai Salisu Gambo mutum ne ma’abocin zikiri (Ambaton Allah), yana tsarkake zuciyarsa da su, har a wani lokaci a baya ya samu kansa

a wani yanayi na jazbah kamar tabin hankali har ya kasance sai da aka kai shi asibitin mahaukata na Goron Dutse ya rinka karbar magani yana sha.

Sai kawai a ranar Litinin din da ta gabata, Malam Salisu Gambo ya sake fadawa cikin wannan hali na Jazbah. Da misalin karfe uku na dare ya fita daga gidansa a cikin irin wannan hali ya nufi ofishin ’yan sanda na Shagari quarters. Yana zuwa a cikin wannan halin na zikiri rike da Alkur’aninsa a hannu da tazbaha, sai kawai ’yan sandan da ke aiki a wannan daren suka yi masa tsawa, ya kI ya bari, sai kawai suka bude masa wuta, nan take ya fadi. Bayan ya mutu ne suka kai shi dakin ajiye gawa na Asibitin Murtala Muhammad.

’Yan uwan marigayin sun samu labarin rasuwar dan uwan nasu ne ta bakin wasu wadanda aka saka a sel safiyar wannan ranar. Kawo gawar marigayin cikin unguwar ta

Shagari ya ta da hankalin Jama’a kwarai da gaske, inda

wasu gungun matasa kimanin 2000 suka harzuka suka nemi kai hari ofishin ’yan sandan, sai da ofishin ya samu taimakon ’yan sanda kimanin motoci guda tara suna

gadinsa.

ALMIZAN ta halarci suturar marigayin a gaban gidansa da ke unguwar ja’oji. Bayan kammala suturar tasa ne kanin marigayin mai suna Alhaji Hamisu Gambo, wanda da ganin sa ka san yana cikin bakin ciki da tashin hankali na rasuwar dan uwan nasa, ya shaida wa ALMIZAN cewa gaskiya Salisu yana da tabin hankali. Su kansu wasu daga cikin ’yan sandan sun san shi, kuma sun san yana da tabin hankali domin yakan je ofishinsu su yi wasa da dariya da shi, amma suka kashe shi ta hanyar harbi har sau uku a jikinsa.

Shi kuwa Rufa’i Ahmad, wanda ya ga marigayin kafin a harbe shi, ya ce wajen karfe uku na dare ne ya ga Malam Salisu ya fito yana salati da tazbaha da Alkur’ani da

kuma Dala’ilu a hannunsa ya yi wajen ofishin ’yan sanda. “Sai dai kawai muka ji wai kawai an kashe shi.

Mutane da dama a yankin unguwar Shagari Quarters sun koka kwarai kan yadda ’yan sandan yankin suke kashe jama’a, inda a cikin shekara daya suka kashe mutane

Biyu, don a waccan shekarar, ana gobe sallah, a wani gida da yake kallon gidan su marigayi Salisu, wata mata da abokan hayarta suna wankin sallah, sai suka dan watsa wa motarta ruwan wanki, sai ta kira musu ’yan sanda. Ko da suka je ofishinsu sai suka yi ta dukan wani Malam Dauda da kulki a kai har sai da ya mut___

El-Rufa'i ya rushe kasuwanni a Abuja

Daga MSU Abuja

Yanzun haka daukacin kasuwannin da ke Unguwannin birnin Abuja da aka fi sani da ‘Corner shops’ sun zama sai tarihi bayan da jibga-jibgan katafiloli suka far musu yayin da suka share su daga samuwa bisa umurnin Hukumar FCDA karkashin jagorancin Ministan birnin Abuja, Mal. Nasiru El-rufa'i.

Tun kafin tsakiyar shekarar nan ne, Ministan ya bai wa kasuwannin sammacin kwashe kayansu a tsakanin watanni shida, wanda zai ba shi uzurin rushe kasuwannin.

Sai dai tun da fari mamallaka kasuwannin sun gurfanar da Ministan a gaban Kuliya, suna masu neman kotu da ta hana Ministan rushe musu kasuwanninsu. Sai dai Ministan ya yi nasara a kan su a kotun, inda ya tabbatar da lokaci rusau din; kuma tuni ya rugurguza daukacin kasuwannin.

Daga fitatun kasuwannin da aka rushe sun hada da rukunin kasuwannin Zone 4 da na Zone 6, Zone 7, Zone 1, da kuma Zone 3, duk a yankin wuse. Yayin da a yankin Garki tuni kasuwar Area 1, Area 11, da kuma Area 2, suka zama sai kufai.

A daidai lokacin da aka fara ruguje kasuwannin sauran ’yan kaasuwan da ba a iso kansu ba, sun yi ta rige-rigen kwashe kayansu tare da rufewar kasuwannin, kofofi, wunduna da duk abin amfani gare su.

Dubun-dubatan ’yan kasuwa ne a birnin Abuja suka shiga wani mawuyacin hali sakamakon rusau din.

Tuni dai wasunsu suka koma hamshakan kasuwannin da hukumar FCDA ta aminta da su, duk ko da dan karen tsadar da suke da shi.

Su ko wadanda suka ga abin ya fi karfinsu, tuni suka yar da kwallon mangwaro, inda suka yi sallama da birnin don zuwa wasu garuruwan, ko koma wa garuruwansu na haihuwa.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International