Almizan :Abin da na ji game da Saddam Husaini ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 24 Shawwal, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Hantsi

Abin da na ji game da Saddam Husaini

Har yanzu ina tuna abin da ya faru ga Saddam Husaini kamar jiya ya faru, kuma zan iya zayyana shi daki-daki. A wata safiya na gama shirina tsaf na zuwa makarantar firamare, sai na je dakin Mahaifina don in yi masa bankwanan na tafi makaranta, sai na same shi kishingide, rediyo a gabansa yana sauraro. Daga cikin rediyon sai na ji mai labaran na fadin cewa; “makaman da aka jefa sun fada a cikin wata kasuwa ne inda ake hada-hada, gawawwakin yara da mata, ga su nan birjik!” Ban san kowace tasha ce Baban nawa ke ji ba, amma har na isa ‘School’ ina tunanin an jefa makami ya kashe yara da mata haka nan?

Shaikh Hasan Saffar

Na kwana uku wannan abu na ci na. A rana ta hudu ina aji Malaminmu na mana darasi, (Malam Ishak, Allah ya saka masa da alheri kan koyarwar da ya yi mana), Malam Ishak Malami ne da yakan dau aji baki daya in yana koyarwa, ya shahara da suna a Katsina. Saboda iklasinsa har yanzu tauraruwarsa na filfilawa a Katsina. A ajinsa kana iya tambayar kome a kowane darasi, idan dai tambayar mai amfani ce. Sai na daga hannu na ce na ji a rediyo an ce... Sai na kowa abin da na ji.

Malam Ishak ya kawo mana labarin juyin-juya-halin da aka yi a Iran a takaice da yadda ya yi tasiri a siyasar duniya da daukaka tutar Musulunci. Sai ya ce, Saddam ana amfani da shi ne domin wannan haske a dusashe shi a hana wasu kasashen kwaiwayonsa, a katse lagon duk wasu masu yunkuri da suke niyyar tasowa. In hali ya yi a ci Iran da yaki a sake mata masu mulki. Wadanda za su rika amsar umurnin Turawa.

A lokacin na ga hoton Donald Rumsfeld, wanda shi ne Sakataren tsaro na Amurka a yanzu a wancan lokacin a fadar Saddam Husaini. Na karanta yana fada wa Saddam cewa Amurka da kawayenta na bayansa a wannan fada da yake yi da Iran, ya jaddada masa cewa Amurka da kawayenta a shirye suke su ba shi duk goyo baya na kudi, makamai da daurin gindin siyasar duniya a kan wannan yakin.

Na ji Saddam na cewa kama birnin Tehran magana ce kawai ta wani lokaci kankani. Na ji yana fadin suna da kwararrun dakaru da za su iya yaki ba dare ba rana, suna kuma da kudin da za su iya yin komai.

Na ji yana yi wa Iran gorin cewar juyin-juya-halinsu ya sa duk suka kashe janarorinsu, wasu kuma sun gudu sun bar kasar. Na ji yana cewa, a ta mummunan bakinsa, “Iran yanzu zindikai ke rike da ita.”

Na ji a lokacin yakin ya rika samun fasahar makamai da sanin sirrin hari daga Yammacin duniya, tare da daurin gindin difolomasiyya. Na ji su kuma kasashen Larabawa sun rika ba shi kudaden daukar dawainiyar yakin da kuma tura masa makamai da mara masa baya a kowane hali.

Na ji kafofin watsa labaran duniya sun zargi Saddam a lokacin yakin da cewa shi bai kare dokokin yaki wurin kula da hakkin fararen hula. Na ga suna nuna hotunan ire-iren wuraren da yake ba da umurnin a kai hari. Na ga wurare ne wadanda suke cunkushe da yara da mata da kuma tsaffi masu dogara sanda in suna tafiya.

Na ji kowane hari aka kai za ka ga kan mutane, ga kokon kai, kwakwalwar dan Adam nan watse. Na ji duk gawawwakin ba masu sanye da kakin soja bane, wadanda suka kai minzalin daukar bindiga, yara ne da tsaffi. Na ji sai matan da ke wa tsaffi jagora kuma suke rike da hannayen ’ya’yansu domin su rako su a shiga gari ake kashewa.

Na ji ’yan jarida idan suka ga abin sukan ce lamari ne da za a iya rubutawa, ko kuma a kyale a zuciyarsu. Na ji dalilin da ya sa kenan suke yadawa suna fantsama hotuna, tare da nanata cewa Saddam Husaini a wannan yaki na Iran da Iraki shi ne bai kare hakkin yaki, kuma yana nuna rashin sanin darajar wadanda ba ruwansu a yakin. Na ji sau 640 ’yan jaridan duniya na kuka da Saddam da cewa ba yaki yake da Iran ba, sai dai wadanda ba su ji ba, ba su gani ba ake kashewa kawai.

Na ji kungiyoyin mata na duniya ma kala-kala suna kokawa da cewa harin da Iraki ke kai wa a kan Iran kamar kuduri ne na a ga bayan matan Iran kawai. Na ji suna cewa jiragen yaki da mizayalolin Iraki ba suna nufar sojan Iran bane, wadanda suke aikin shiga da shirin yaki kuma suke a fagen daga ana fafatawa da su ba, amma suna nufar wurin haduwar mata da yara ne zalla.

Na ji wani yaro ya yi zanga-zanga shi daya a birnin Birmingham ta tsakiyar London, saboda kullum ya dawo makaranta idan gidan talabijin na nuna yakin Iran da Iraki sai a nuna gawawwakin yaran da ake kashewa a Iran. Na ji yaron ya zana da fenti a jikin takarda; “Allah ya tsine wa Saddam da yake kashe yaran Iran.” Sannan ya fito kofar gidansu ya daga takardar. Na ji kafin ka ce me! Sai wurin ya cika da jama’a suna jinjina da amsar kiran yaron nan da fadin, “amin.”

Na ji nan da nan ’yan sandan Birtaniya suka zo suka tarwatsa taron suka kuma mai da yaron cikin gida suka gargadi iyayensa a kan su kula da shi. Na ji duk wadannan maganganun da ake yi a kan Saddam kasashen duniya sun yi gum, sun zama ba su ji, ba su gani ba, suna kuma saurare.

Na ji labarin wani gari mai suna Halabja, wanda duniya ta ga hotunan gawawwaki a kan titi kwance, kai ka ce an busa kaho ne. Gawawwakin ga su nan kowacce da irin siffarta, wata mai ita na tsakiyar tankade aka zare ran, wata yana tafiya ya fadi kasa ya mutu. Wasu ’yan makaranta ne da ‘uniform’ suna zumudin zuwa aji don daukar darasi, sai kawai suka fadi a hanya suka mutu.

Na ji cewa ganin wadannan hotunan suka sa wasu masu zuciyar imani suka yi ta kuka a duniya. Wasu hotunun mutanen uku ne da ake tsamanin kamar lamarin ya faru ne daya zai fadi kasa, sai daya ya kawo masa dauki, sai suka tafi kasa, can sai wani ya rugo da gudu don agajin gaggawa sai shi ma ya bi su. Na ji cewa hoton ya daga hankalin duniya.

Na ji an misalta abin da aka gani a Halabja kamar wani fim ne wanda sai an kashe kudade masu yawan gaske wajen shirya shi domin nuna rashin imani da ban tsoro, amma ba fim bane, da gaske ne. Na ji a nan ma duniya ta shiga iskar kau da kai, sun zama kamar suna a wani tauraro ne wanda ba kafar watsa labarai, kuma sako bai isa gare su ba.

Na ji masana sun ce a Halabja wata iska ce aka yi amfani da ita mai gubar gaske wadda tuni aka haramta amfani da ita a duniya a kowane yaki. Na ji ita wannan guba in za ta yi kisa tana yi ne a wani yanayi mai azabtarwa. An ce takan datse duk wata kafar iska da farko, ta yanke hanyoyin jini, sannan ta makure mutum ya mutu a hankali.

Na ji wanda ya shake ta kafin ya mutu dole ne ya yi gurnani da shure-shure, zai yi fatan ya mutu da wuri, amma muguwar iskar ba ta bari dole sai ta wahalar take kashewa. Na ji an yi ta muhawara a kan yawan mutanen garin da suka mutu a wannan hali a garin, Iran ta fadi nata adadin. Majalisa Dinkin Duniya ma ta fadi nata.

Na ji Iraki ta yi wuf a lokacin ta ce kazafi da karya kawai ake neman a yi mata da kuma zurmuke, yawan adadin da suka mutu ba su kai yadda Iran take fada ba. Na ji Saddam yana cewa gaskiya da kyar in mutanen sun haura dubu biyar, ya ce wai ai yawancin mutanen garin ba a cikin gari suke ba lokacin da aka fesa iskar a birnin, kuma ai duk ba su mutu ba. Na ji iskar idan ba ta kashe ba, to za ta lalata daya daga cikin muhimman sashen mutum. Na ji cewa musamman wajen rasa ji da gani da kuma karfin mazakuta, ko kuma ta raba mutum da hankalinsa kwata-kwata, mutum ya yi rayuwar da gara mutuwa da ita.

Na ji duk da kyale Saddam da kasashen duniya suka yi, a lokacin sun dan tanka da ’yan zantuttuka haka. Na ji Amurka na cewa wannan abin da aka yi a Halabja “ (Saddam) ka so ka yi kuskure.” Kakakin fadar ‘farin gida’ ya yi ta wasa da kalmar Turanci, sannan ya karkare da cewa an so a yi kure, amma kar a kuma kwatawa.

Na ji Saddam na kare kansa da cewa ta wannan hanyar ne kawai za a tilasta wa Iran ta yi biyayya. Na ji Saddam yana fadin yakin gaba da gaba ba zai taba cin Iran ba, domin sun cika taurin kai da zafin nama.

Na ji Saddam na isar wa da duniya sakon cewar in dai ana son a yi nasara a yakin dole sai an bi wasu hanyoyi da za a karya lagon tirjewa da kuma nausawar abokan gaba.

Na ji Imam Khomaini ya yi kuka da hawaye a kan ta’addancin, ya yi jimamin lamarin, ya kuma isar da sako mai kaushi. Na ji ya yi wa Saddam Husaini addu’a wadda a ciki yake cewa; “in Allah ya so karshenka zai zama mafi wulakanta daga rayuwar kowane dan Adam.”

Na ji a wata addu’ar da Imam Khomaini ya yi yana cewa; “in Allah ya so wadanda suka gina Saddam sune kuma za su yake shi.” Na ji a wata addu’ar Imam Khomaini yana cewa; “duk wanda ya mara wa Saddam Husaini baya, in Allah ya so wata ran sai ya zama babban makiyinsa.”

Za mu ci gaba insha Allah.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International