Almizan :Wakilcin addini da al’ada a fima-fiman Hausa (2) ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 22 Zulkidah, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Rubutun musamman

Wakilcin addini da al’ada a fima-fiman Hausa (2)

Daga Nasiru Wada Khalil na kotun daukaka kara ta shari’ar Musulunci da ke Kano (Shari’a Court Of Appeal, Kano) (nasiruwada@yahoo.co.uk ).

CI GABA DAGA MAKON JIYA

WAKILCIN AL’ADA A FINAFINAN HAUSA

Kusan yawancin manazarta na cewa fimafiman Hausa ana yin sune da yaren Hausa, amma abin da yake cikinsu ba Hausa bace. Wasu kuma ba su yarda da wannan ra’ayin ba. Dukkan fimafiman Hausa kowanne yana dauke da wani sako, sai dai mai shiryawa ya zama bai san yadda zai isar da sakon ba. To daga nan sai abin ya sauya kama. Wannan kuma yana da alaka da rashin bincike wajen rubutawa da tsara fim din.

Akwai abin da yake da mahimmanci wajen wakilcin al’ada, ya kamata mutumin da zai wakilci al’ada ya zama dan cikinta, wannan zai sa ya yi kishinta, domin ya san duk abin da ya nuna abin yana wakiltarsa shi kansa. Ma’ana duk abin da ya nuna wa duniya to shi kansa haka yake. Wannan ce ta sa Bahaushe Musulmi ba zai sami wakilcin da yake bukata ba a cikin fim din Hausa. Domin kusan duk manyan jaruman da suke fitowa a cikin fimafiman ba Hausawa bane. Don haka maganar Bayarbe ko Babur ko Ibira ko Tangale ko Ibo su ba da wakilci gamsasshe ga al’adar Bahaushe ba ta taso ba ko kusa.

Akwai fimafimai da aka wakilci Bahaushe irin yadda yake, da gani babu tambaya misali: “ALJANNAR MACE” an nuna yadda hakuri yake a cikin bin aure da yadda bin iyaye yake da amfaninsa da tasirinsa a rayuwa. Fim din ya nuna tasiri da karfin uwa a rayuwar Bahaushe Musulmi. Ishak ya san mahaifiyarsa na takura wa matarsa, amma sai dai ya bai wa matar hakuri, amma bai taba ko da musu da mahaifiyar tasa ba. “TSAUTSAYIN TAKABA” an nuna illar bin mugayen abokai da muhimmancin alkawari da yadda Bahaushe ke zama da iyalinsa da makotansa. Inda Malam Sidi ya amince da mijin da ’yarsa Bebi ta kawo, amma daga baya ta kawo wani daban, shi kuma mahaifin nata ya ki amincewa domin ta sa ya amince da zancen wani.

Haka kuma, “AKASI” ya koyar da tsayawa a kan gaskiya da rashin tsoro da dattako irin na Bahaushen mutum. Fim din KUSURWAR DANGA ya bayyana zaman gidan haya na tarayya da rashin dacewarsa da rayuwar Bahaushe Musulmi. An nuna yadda matar wani ke shiga ban daki da safe mijin wata kuma na zaune da butarsa yana jiran ta. Lalle wadannan fimafimai da wasu makamantansu, kamar NAMSHAZA da GASHIN KUMA da KALLO YA KOMA SAMA suna wakiltar Bahaushe ta fuskar al’adarsa.

Akwai fimafiman da ake magana a kansu wadanda yaren da aka yi su Hausa ce, amma abin da yake ciki ba Hausa bace ta kowacce fuska. Misali, “KUGIYA” inda aka nuna mutum ya mari surukinsa, wanda ya saba wa Bahaushiya kuma Musulmar al’ada. A cikin shirin “TUBALI” an nuna mutum babba da kaninsa da matansu da ’ya’yansu suna waka. Abin mamaki shi mutumin an nuna mai gaskiya ne da sanin ya kamata. Kowa ya san yadda alakar wa da matar kaninsa a rayuwar Hausawa, amma sai ga su suna waka tare a cikin fim din TUBALI da KUDURI. Kuma ba abu ne mai sauki ba mutum ya tsaya a kan mahaifinsa yana taka rawa, amma duk an nuna hakan a cikin TUBALI. Fim din KHUSUFI, mutum Bafilatani ya turo ’yarsa ta zo birni daga ruga kawai don ta zama mawakiya, kuma shi ma ya dauko duk iyalinsa suka dawo birni suka watsar da duk al’adarsu a cikin watannin da ba su fi uku ba.

Idan aka kalli fim din “GUDA” za a ga yadda miji da matansa guda biyu suka sako wanduna suka zo titi suna wata mummunar rawa, wanda babu wani mutum Bahaushe da zai amince matarsa ta auren sunna ta yi wannan shiga wani ya gan ta, ballantan har ta fito waje ta yi rawa. Babu wani Bahaushe da zai hada ’yarsa da saurayinta wai su tafi wani gari neman aiki, amma sai ga shi a cikin “KADAMI” mutum ya hada ’yarsa da saurayinta sun tafi wani gari neman aiki.

RAWA DA WAKA

Rawa da waka shi ne abin da aka fi suka a cikin fima-fiman Hausa. Bahaushe ya dauki rawa da waka a matsayin sana’a, amma ba a matsayin wani mahadi na rayuwa ba. Mutum zai so a yi masa waka ko kuma ya saurara, amma ba zai so a ce shi ne mawakin ba. A kasar Hausa an dauki sana’ar waka a matsayin sana’ar wasu makaskantan mutane. A tarihin kasar Hausa ba a yi mawaki kamar Alhaji Mamman Shata Katsina ba, amma a hirar da mujallar Rana ta yi da shi a 1988 ya ce; ba zai so ’ya’yansa su gaje shi ba. Kuma duk mutumin da zai ce da kai rawa da waka al’adar Bahaushe ce, ka yi masa addu’ar dansa ya zama mawaki zai ce a’a. Magana daya, waka sana’a ce kamar kira ko saka ko dukanci a kasar Hausa domin gadonta ake yi. Su ma masu sana’ar ba ka ganinsu a gida suna yi wa iyalinsu waka.

Dukkan ’yan fim da suke da aure babu wanda ya taba fito da kaset din wakar da ya yi wa matarsa, sai kadan kamar su Ali Baba da Sadi Sidi Sharifai da Ado Ahmad Gidan Dabino, su ma a fim aka saya aka saka ba zuwa suka yi suka rera tare da matan ba. Gidan Dabino ne ma ya kai tasa wakar gidajen Rediyon kasar Nijar.

WAKILCIN ADDINI A ZAHIRI

Wakilci dai a zahirance shi ne tsayuwa kan matsayin abin da kake wakilta, saboda haka wakilcin Musulunci shi ne tsaya wa ga abin da yake nuna koyarwar addinin Musulunci. Wannan matsayi kuwa ya kunshi yanayin sa kaya, yanayin magana, yanayin zamantakewa da sauran ire-iren abubuwan da suke bayyanannu.

A nan idan muka ce za mu waiwayi yadda ake wakilcin addinin Musulunci a cikin fima-fiman da Musulmi Hausawa suke shiryawa, to wadannan abubuwa da muka ambata a sama su za mu duba mu ga yanayinsu, kamar yadda aka jero su a kasa:

1. Suturta Al’ aura.

A. SHIGAR MAZA

Shigar da Musulunci ya iyakance ga dan Adam shi ne na farko (ga namiji) “daga cibiya zuwa gwiwa.” Idan namiji ya fito da wadannan wurare da aka ambata to an fito da tsiraici. Amma za ka ga a fima-fiman Hausa kamar ga misali a fima-fiman Barkwanci za ka ga namiji ya tube zai yi ko kuma yana kokawa daga shi sai wando, ga shi kuma wandon bai kawo zuwa cibiyarsa ba. Saboda haka ya nuna tsiraicinsa, irin wadannan fima-fiman sun hada da:

1. AFANTAMA. 2. SHAFI MULERA. 3. HATSABIBI. 4. DANBALLOTA. 5. AMALALA

A nan za mu iya cewa wadannan mazan masu irin wannan shigar ba su wakilci shiga irin ta Musulunci ba, don babu bukatar ko larurar yin hakan. Kodayake yawancin shigar da maza suke yi a fim shiga ce da take mai ma’ana wacce ta dace ko ta wakilci shigar da Musulunci bai hani a kai ba. Wadannan fima-fiman sun hada da:

1. WATA RANA. 2. DACE DA MASOYI. 2. TAFARKI da sauransu.

SHIGAR MATA

Tsiraicin mace kuwa ba irin na namiji bane, domin ita “dukkanin jikinta tsiraici ne, ban da fuska da tafukan hannunta.” Ma’ana inda duk mace ta sake ta fito da wani sashi na jikinta kamar bayan hannuwanta, ko wuyanta ko gashin kanta da sauransu to ta fito da tsiraici. Don haka ba za a alakanta wannan shigar da Musulunci ba.

Mata a fima-fiman Hausa akasari ba su kiyaye ko kare tsiraicinsu sai ’yan kalilan, su kuma kalilan din nan wadanda shekarunsu suka yi nisa ne, domin duk wani sashi na sutura irin ta Musulunci an canza shi ta koma ta wani abu daban. Misali:

RIGA: Rigunan da suke sawa akasari marasa hannu ne, hasali ma rigar ta samo sunan ta ne daga wata riga da wata mata da ake kira Stella take yawan sawa. Saboda haka za ka ga kasangalalin hannuwansu a waje yake, ga ta da fadin wuya yadda har rabin kafadunsu da allon kafadarsu ana kallo. Misalin shiga da irin wannan riga za a same ta a fim din KUGIYA da Hafsat Shehu ta yi.

Bayan wannan akwai kuma wata riga ita ma kamar Stella din ce, to amma hannunta yana da tsawo, sai dai a yage yake yadda in an daga hannun za ka ga ya zama tamkar fukafuki. Ita wannan riga ana kiranta ‘Saima Style,’ ma’ana ta samo sunanta ne daga wata jarumar wasan Hausa mai suna Saima Muhammad, wacce ta saka wannan rigar ne a cikin wani fim mai suna KAMALA suka yi wata waka da ake cewa da ita Dokin na Malaitu. Sunan fim din ya yi gabas shigar jarumar ta yi yamma.

Za mu cigaba insha Allah.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International