Almizan :Dole ne Obasanjo ya sauka a 2007 ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 22 Zulkidah, 1426                 Bugu na 693                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Rubutun musamman

Dole ne Obasanjo ya sauka a 2007

In ji Shaikh Yakubu Musa Kafanchan


Daga Aliyu Saleh

Shaikh Yakubu Musa Hasan Kafanchan, Malami ne daga cikin manyan Malaman da Kungiyar Izalatul Bidi’a Wa Ikamatu Sunan take tinkaho da su. Ya yi suna ba kawai a tsakanin ’yan Izala ba, amma har a birane da kyauyukan da ke fadin kasar nan da ketare.

Saboda fede gaskiya ake masa lakabi da ‘Sautus Sunna.’ Saboda wa’azin da yake yi mai zafi ba tare da rufa-rufa ba, idan Izala ta shirya wa’azi ba a kira shi ya yi wa’zi ba, sai Izalawa sun nuna rashin amincewarsau a take a wajen, kamar yadda ta faru a Funtuwa a kwanakin baya.

Saboda fadar gaskiyar da yake yi ne, da kuma adawa ta zahiri da yake yi wa wannan gwamntin ne ya sa a farkon hawan wannan gwamnatin ta Obasanjo aka kame shi aka tsare na wasu kwanaki. Kuma lokacin da Obasanjo ya gayyaci Malamai da Sarakuna fadarsa ya ce bai yarda a je wajensa da “Dan Kafanchan mai zafi ba.”

Tun farkon hawan wannan gwamnatin suke fito-na-fito da gwamnatin jihar Katsina. Akwai lokacin ma da aka fara rade-raadin za a kore shi daga garin, musamman da yake wasu suna ganin shi ‘bako ne,’ zuwa ya yi. Sai dai saboda magoya baya da kuma tasirin fada-a-jin da yake da shi a cikin Izala ya sa ala tilasa aka janye wannan batun ba don ana so ba. Duk farin jini da yake da shi a cikin kungiyar tasu ta Izala, Shaikh Yakubu Musa Kafanchan, mutum ne mai saukin kai da tsantseni.

A karshen makon jiya ne suka kira babban taron wa’azi na kasa a garin Kaduna, domin nuna cewa har yanzu suna nan tare da kungiyar Izala, sabanin yadda wasu suke yadawa cewa sun yi wa kungiyar tawaye. Bayan kammala taron wa’azin ne, ALIYU SALEH ya zaunar da shi, inda ya tambaye shi matsayinsu game da shirin gyaran tsarin mulki da ake yi da ake jin zai bai wa Obasanjo damar zarcewa a 2007, musamman da yake wannan batun yana daga cikin bututuwan da ya tabo a wa’azin da ya yi a wajen taron. Abin da ke biyu hirar ce kamar yadda ALIYU SALEH ya rubuta mana.

MATSAYIN IZALA GAME DA TA-ZARCE

Dama dai Izala matsayinta shi ne a tabbatar da gaskiya da adalci da rikon amana da alkawari. Abin da su suka rubuta da kansu a tsarin mulki shi ne shekara hudu sau biyu, kuma tsarin mulkin nan ba taba cewa a gyara ba. Sannan kuma su ’yan siyasa suna cewa sun yi alkawari idan dan Kudu ya yi dan Arewa ma zai yi, mu kuma Kungiyar Izala matsalolinmu biyu ne. Na farko dai saboda akidar addininmu, da kuma matsayin al’ummar Musulmi a Nijeriya, kuma an ce dimokuradayya ake yi. Don haka adalci shi ne lalle mulki ya tabbata a cikin al’ummar Muuslmi, kuma a Arewa. Mu a jiye maganar Arewa gefe guda, muna magana ne a kan Musulunci da wadanda ba Musulmi ba, wadanda suke fada da mu, wadanda Allah ya ce makiyanku ne, kuma makiyana ne, mu a Musulunci dama mun fadi cewa, Musulunci bai yarda ka jefa wa wanda ba Musulmi ba kuri’a ya zama Shugaba, ko da kuwa a unguwa ce, amma abin da suka yi har shi wannan Shugaban kasar ya hau mun riga mun yi bayani, kuma mun fassara shi da cewa fashi ne suka yi da mukami da makami a lokaci guda, amma akwai dubban ’yan jami’yyarsa yau sun fito suna bayyana cewa ba zaben dama ya ci ba, kuma ba mai rikon amana bane, kuma bai yi adalci ba, bai tsare gaskiya ba. A wannan bangaren idan muka koma kuma a dimokradiyyance an ce dimokradiyya ce, kuma na ce akwai tsarin mulki, sannan kuma a shekarun baya ba su yi maganar a gyara tsarin shugabancin ba sai yanzu, sannan kuma muna jin maganar ta-zarce-ta-zarce yana fitowa daga bakunan wadanda suke ya kamata a yarda da maganrsu, bayan sun san wadannan shekaraun shida da wani abu da aka yi an rushe al’ummar Musulmi masu yawa daga aikin soja, daga ’yan sanda, imagireshen, kwanstam, da manyan sakatarori da wasu ma’aikata masu yawa, ta kai ga a yanzu babu wani Musulmi mai bakin fada-a-ji a cikin tsarin tafiyar da gwamnati a Nijeriya, wannan ya sabawa dimokradiyya, kuma ya sabawa shari’a ta Musulunci. Yanzu a zo a ce za a gyara tsarin mulki domin wannan gwamnati ta-zarce, a kara shekara biyu, daga nan kuma sai ta-zarce zuwa shekara hudu, wannan wani abu wanda al’ummar Musulmi ba za su yarda da shi ba, haramun ne mu yarda da shi, kuma ba za mu taba yarda da shi ba. Hasali ma duk mutumnin da yake tunanin cewa ya kamata mu yi shiru mu yi ta addu’a kawai yana so ne ya karya sunnar Allah, da kawai a yi shiru ne a yi ta addu’a ne, da Manzanni ba su yi yaki ba, saboda haka dole ne mu fito mu yi magana, mu kuma tashi a aikice mu yi aiki, idan wannan gwamnatin ta-zarce wani bala’i ne da za a iya kwatanta shi da manyan manyan masifu da suke sauka a cikin al’ummar Musulmi, don haka dole ne mu gaba dayanmu maza da mata yara da manya ta hanyoyin da ya kamata a isar da sako don mu tabbatar da cewa ba mu yarda wannan tsarin na ta-zarce ya ci nasara ba, in kuwa aka ce sai an yi sai inda karfinmu ya kare. Kuma mu tanadi abin da za mu yi wa duk wani da yake neman mu yarda da wannan ta-zarcen. Duk wani dan siyasa da yake cewa a yarda, mu tanadi duk wani abu na walakantarwa a gare shi da suka hada da baragurbin kwai, tumatir da ruwan ‘Pure Water’ mu yi ta jifan su da shi idan sun shigo inda muke, domin idan muka bar su bala’in da za mu jefa kanmu a ciki, ba mu kawai zai shafa ba har zuriyarmu bala’in sai ya je ya same su.

BA ’YAN SIYASA NE KE AMFANI DA MU BA

Mu da muke wanann magana duk wani dan siyasa lalatacce ya san cewa cikin ikon Allah ya kare mu, ba wani dan siyasar da ya isa ya yi amfani da mu don mu yi wannan maganar. Wannan maganar muna yin ta tun kafin su ’yan siyasar ruwa ya kawo masu wuya. Tun 1999 da aka ce za a tsayar da dan takara, mun yi maganar, kuma ba mu taba barin ta ba har yanzu. Saboda haka idan ’yan siyasa za su yi amfan da mu, wadanne kenan? Mu kamar yadda muke cewa siyasarmu kullum ita ce Islam, a kanta muke, da yarda Allah a kanta za mu mutu, a kanta za mu yi fada, a kanta za mu yi ki yarda, a kanta za mu yi fushi, a kanta za mu yi jayayye, amma ba a kan wata jam’iyyar siyasa ba. Batun ANPP, PDP AD da surasu ba ruwanmu da su wallahi, amma in ana son a fahimci muna goyon bayan wane, a zo a nuna rashin adalci a wajen da Musulmi suke da rinjaye. Tun shekaru da dama da suka wuce Musulmi ke da rinjaye, sai yanzu a zo a ce dole ta karfin tsiya sai an dora wanda ba Musulmi ba a kanmu alhali an ce dimokradayya ake yi. Mu jefa kuri’armu a juye ta, idan aka ce za a yi mana haka, yanzu kam maganar uzuri ga kwanne Musulmi ta kare, wannan shi ne bayanin da muke yi, kuma a kansa za mu tsaya, wannan kuma shi ne ra’ayin da Malaminmu, Malam Abubakar Gumi ya bar mu a kai, wanda kuma ya kawo hujjoji ne da Alkur’ani da hadisi muka tsaya a kansu, wannan kuma shi ne matsayin Izala a lokacin da aka yi zabe tsakanin Shagari da Awolawo, bai canza ba, wanann karon ma a wannan zaben da aka ce an yi wa Obasanjo da Buhari shi ne dai matsayin Izala, kuma har abada wannan shi ne matsayinta. Domin matsayi ne wanda yake rubuce a Alkur’ani da Hadisi, duk wanda ya ce mu tashi daga wannan matsayin sai ya kawo mana aya a Alkur’ani ko Hadisi.

WANNAN BA ZAI KAWO TASHIN HANKALI BA?

Wace Hukuma? Hukumar da ta yi fashi? Hukumar da ba ta yarda da tsarin mulkin ba? Hukumar da ta yarda da ba ta yarda da dimokradiyyar ba? Hukumar da babu adalci a cikinta? Ita ce zan ji tsoro, kar ta ce za a kawo tashin hankali, ko wani abu? Ai tashin hankali shi ne a yi rashin adalci? Tashin hankali shi ne da karfin tsiya a ce za a canza a bin da ke rubuce a tsarin mulki don biyan bukatar wani. Tashin hankali shi ne a dauki abin da kamata a aza shi a idan bai kamata ba. Mu kiran adalci muke yi. Ba mu ce a kwace hakkin kowa a ba wani ba. Amma dole ne a tabbatar da hakkinmu a matsayinmu na Musulmi, a matsayinmu na ’yan Nijeriya tunda an ce dimokradiyya ake yi. Su suke cewa a ka’idar dimokradiyya ‘Majority Carry The Vote’ (mai yawa shi ke da rinjaye) ba. Su waye ‘Majority?’ A ‘Census’ (kidayar mutane kasa) da aka yi a 1963, an ce Musulmi muna da kashi 65, mu dauka ma ko da misali kashi 60 ne, ni din nan yanzu ina kalubantar kowanne kirista da yake da shekaru kama ta, ya zo mu yi lissafi da shi, a matsayina na mai wa’azin addinin Musulunci, a matsayinsa na mai wa’azin kirisanci, ya kawo min ’ya’yansa da matansa mu kirga, ni ma na kawo nawa. Ina da sama da ’ya’ya 25 yanzu, wane kirista ne da yake da shekaru kamar nawa zai ce yana da ’ya’ya 10? Babu. Kenan daga 1963 din zuwa yanzu idan za a yi lissafi, su wa ya kamata su karu? Su wa ya kamata a ce sun samu ‘Majority,’ amma kiri-kiri Obasanjo ya je ‘White House’ (fadar gwamnatin Amurka) ya ce 50-50 muke. Wannan rashin adalci ne, kuma mutanenmu da suke tare da shi suna ji sun ki karyatawa. Don haka idan za a yi rashin adalci babu wata maganar zaman lafiya. Idan za a yi rashin adalci babu maganar wani tsoron tashin hankali. Idan suna son a zauna lafiya da kwanciyar hankali, a tabbatar da adalci, sun ce dimokradiyya, a tabbatar da ita, sun ce dimokradiyya su tabbatar da tsarin mulkin nasu, kada a canza don biyan bukar wani mutum.

GWAMNATI TA YI WA MUSULMI YANKAN BAYA

Ba mun bayyana matsayinmu ba, ba mun bayyana yadda aka yi mana (Musulmi) tun daga tsarin sojoji, ’yan sanda, manyan ma’akata da tsarin ministoci? Tunda kake a Nijeriya ka taba jin inda aka yi rashin adalci wajen rabon mukamai kamar wanda wannan gwamnatin ta yi? Tunda kake a Nijeriya ka taba ganin rashin adalcin da ake yi mana ana ta talauta mu? Ka yi tunani mana shekaru 30 da suka wuce, masaku kawai a nan Kaduna nawa ne suke aiki? Amma yanzu mutane dubu nawa ne suka rasa ayyukansu saboda matsalar wutar lantaki? amma kuma a Kudu babu wannan matsalar. Alhali kuma mu muka gina Nijeriyar da kudin audiga da kudin gyada, da kudin fata. Da kudin aikin mona ne aka gano man, aka kafa masana’antun tace man, duk da ba su yi wannan fadan ba sai yanzu. Akwai rashin adalcin da ya wuce wannan? Sannan kuma babban rashin adalcin duk da an ce dimokuradiyya ake yi, amma a zo ba a yarda a tsai da dan Arewa ba, ba a yarda a tsai da Musulmi ba, wannan wace irin dimokradiyya ce? A ce wai za a yi Kudu da Arewa. A ina aka samu wannan tsarin dimkradiyyar haka? Wannan ba rashin adalci bane a fili. Wadanda ma suke a nan Arewa suna Musulmi suka yarda da wannan, ai su yanzu su da kansu sun gano cewa sun cutar da addini, sun cutar da Arewa din.

A HADA HANNU WAJE DAYA

Kiran da muke yi wa duk wani dan Arewa shi ne, ya zo a hadu don a ga cewa an tabbatar da adalci, wannan mulkin nan ya dawo hannun masu shi. Nijeriya idan ka duba a tsarinta, wannan kogin da ya raba Nijeriya uku, shi da kansa ya tabbatar da tsarin Nijeriya, Kudu ta yamma (wajen Yarabawa) su ke da ilimi, Kudu ta gabas (wajen Inyamurai) su ke da kasuwanci, mu kuma Arewa (wajen Hausawa) mu ke da mulki. Idan ka ce za ka kwace wa daya ka mai da wa daya, ka yi rashin adalci. Wannan shi ne hakikanin abin da ake kai. Don haka duk wani wanda ya dibge a da, kudi ya rude shi, ko kujera mukaminsa a cikin ’yan siyasa, muna kiransa ya yi gaggawa ya dawo. Domin mulkin nan jinin iyayenmu, jinin malamanmu, jinin sarakunanmu nan, jinin shehunanmu, jinin almajiranmu, jinin sojojinmu aka ba da aka kafa wannan mulkin. Don haka wadannan ’yan siyasar mayaudar, maha’inta, maciya amana suka dauka suka mika shi har da ba da kudi, da kuma fito da dan takara, da cewa dole a zabe su, aka ba su kudi. Shi ne muke kiran su ’yan siyasar da kansu. Muna kiran dukkan sarakuna, (kuma za mu sa masu ido), dole su zo a hada kai. Muna kiran dukkan wani kwararre na kowanne irin bangare a nan Arewa ya zo ya kawo gudummawarsa. Lalle ne mu zo mu hada karfi da karfe mu tabbatar namu kason nan sai an tabbatar mana da shi, ba a ci gaba da yi mana rashin adalci ba. Wannan kuma ko mai zai faru ya faru, dole mu tabbatar da wannan. Kuma ina kira ga duk al’ummar Musulmi duk wanda ya ja gefe guda ya hade da wadanda suke so su cutar da mu a yi masa tawaye, a nuna masa kasawarsa.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


  | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International