Almizan :Wasiyyar iyaye ga ’ya’yansu yayin da za a aurar da su ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 22 Zulkidah, 1426                 Bugu na 697                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Hantsi

Wasiyyar iyaye ga ’ya’yansu yayin da za a aurar da su

A yau na yi niyyar in ba da aron filin nan ne ga wata Malama mai suna Malama Barira Musa Katsina, Shugabar makarantar Liwa’ul Islam Sabuwar Unguwa Katsina. Na yi niyyar karama ta da wannan fili ne domin in jinjina mata a kokarinta na yawon wa’azi domin fadakar da mata a iya tata fahimtar.

Shaikh Hasan Saffar

Malama Barira ta yi fice a Katsina a wajen shiga gidan manyan mutane tana wa’azi, ko jawo hanlinsu a yi wa’azi mai maimakon sharholiya a yi wa’azi mai mamakon sharholiya da bidi’o’in da suka wuce iyaka a lokacin bikun aure ko suna.

Tana da makarantar Islamiyya wadda Malamar na kokari sosai a wajen kulla da karantar da yaran da gina su a bisa tarbiyya ta kwarai.

Malama Barira har tafsiri take yi a duk cikin azumin watan Ramadan, wanda tafsirinta ne mafi girman wanda aka sani mace ke yi kuma mata na halarta.

Wannan takarda ta gabatar da ita ne tare da jawabi a wurin walimar daurin aure na gidan Alhaji Bala Saulawa wanda aka daura tsakanin Angwaye, Muhammad da Hadiza. Allah ya sa in an karanta za a amfana, amin.

1. WASIYYAR DA AKE WA MATA

An so a yi wa mace wasiyya idan za a kai ta gidan mijinta. An ruwaito daga Anas ya ce Sahabban Manzon Allah (S) sun kasance idan za su kai mace gidan mijinta sukan umurce ta da yin hidimar miji da kula da hakkinsa.

2. WASIYYAR UBA GA ’YARSA LOKACIN AURE

Abdullahi bn Ja’afar bn Abi Talib ya yi wa ’yarsa wasiyya, inda ya ce; “kashedinki da nuna kishi, domin kuwa shi ne mabudin hanyar saki. Kuma kashedinki da yawan zargi domin yana gadar da kiyayya, kuma ki rika sanya kwalli domin shi ne mafi kawar dukkan kwalliya, mafi tsaftar dukkan tsafta, shi ne ruwa, (wato ki rika wanka da wanki).

3. WASIYYAR UWA GA ’YARTA

Wannan wasiyyar da Amamata bn Harith ta yi wa ’yarta Ummu Iyas bn Aruf Muhallim Ashshaibani, ita wannan tana bayyana harsashin kyakyawar rayuwar aure, tare da abin da ya wajaba a kanta na hakkin mijinta. Ga wasiyyar da ta ce: “Ya ke ’yata! Ita wasiyyar da ana barinta saboda darajar mutum, to da ban yi maki wasiyya ba, to amma ita wasiyya tunatarwa ce ga barin rafkana, kuma taimakawa ce ga mai hankali.

“Kuma da za a ce mace na iya barin yin aure saboda wadatar iyayenta da kuma yadda iyayenta ke tsananin kaunarta, to da kin fi kowa wadatuwa ga barin aure. To, amma mata an halitta sune saboda maza, su kuma maza an halitta sune saboda mata. Ya ’yata lalle kin rabu daga yanayin da kika fito daga cikinsa, kuma kin rabu daga gidan da kika saba cikinsa zuwa wani gida wanda ba ki san shi ba. Da wani aboki wanda ba ki saba da shi ba, zai wayi gari shi ne da mulkinki. Saboda haka ki zamo kamar baiwa a gare shi, shi kuma zai zama bawa mai biyayya a gare ki. Ki kiyaye masa wasu halaye guda goma, sai ki samu biyan bukatunki duk lokacin da kika waiwaye shi:- 1-2

Biyayya a gare shi ta hanyar godiya ga dukkan abin da kika samu daga gare shi, da kuma kyakykyawan sauraro gare shi da kuma yin da’a.

3-4 Ki kula da abin da yake so ya rika gani, ki nisanci duk wani abu na kazanta mai wari, kuma kada ki yarda ’yan uwansa su hangi wani abu maras kyau daga gare ki, kada kuma hancinsa ya shaki wani abu daga wajenki idan ba mai kamshi bane. 5-6

Ki kula da lokuttan barcinsa da na cin abincinsa. Kisan dadewar yunwa tana jawo damuwa, haka kuma tauye barci yana jawo fushi. 7-8

Ki kula da dukiyarsa da kaddarorinsa da kuma iyayensa, ki yi kyakkyawan tsari game da iyalinsa.

9-10 Kada ki saba wa umurninsa, kuma kada ki tona masa asiri. To idan kika saba wa umurnisa, to kin fa shiga cikin fushinsa, kuma in har kika tona asirinsa, to ba za ki amintu daga matsalarsa ba. Kuma kashedinki daga yin farin ciki a gabansa lokacin da yake cikin damuwa. Kuma kada ki bayyana farin cikin ki lokacin da yake cikin bakin ciki.”

4. WASIYYAR MIJI GA MATARSA

Abu Darda’u ya ce wa matarsa; “in kin gan ni na yi fushi to ki lallashe ni, ni ma in na ga kin yi fushi zan lallasheki. In kuwa ba haka ba to ba za mu daidaita ba.”

ABUBUWA SHIDA DA SUKA WAJABA A KAN MAZAJE GA MATAYENSU

1. Ciyarwa, tufatarwa da ba su wajen zama. 2. Adalci tsakanin abokan zama (kishiyoyi) da makwafta. 3. Kada ya kauracewa matarasa, ko ya cuce ta ko ya rike ta ko ya wulakanta ta. 4. Kada ya rike ta don ya azabatar da ita, ko ta hanyar hana ta hakkinta, ko wulakanta ta. 5. Shiryar da ita da koya mata addini don ta san yadda za ta bauta wa Allah da biyyyaya ga Manzonsa da kuma mijinta wajibi ne a kansa. 6. Kada ya hana ta ziyarar iyayenta ko danginta (na jinni), ko wajen neman magani.

ABUBUWA TAKWAS DA SUKA WAJABA A KAN MATA GA MAZAJENSU

1. Biyayya ga miji idan bai saba wa shari’a ba. 2. Tsabtar kanta da gidanta da ’yan’yanta. 3. Kiyaye kanta da yaranta game da abin da zai zama abin assha gare ta da kuma mijinta. 4. Kyautata gida kamar shirya girke-gireke da sauransu. 5. Kada ta kallafa wa mijinta yin abin da ba zai iya ba, kamar ta sa shi sayen abin da ya fi karfinsa. 6. Kada ta yarda ta shigar da wani mutum a gidansa wanda mijinta ba ya so. 7. Kada ta fita ba tare da izininsa ba. 8. Ta zama mai ba mijinta shawara ta gari in ta ga ya shiga wata matsala.

ABUBUWAN DA SUKE WAJABA KAN MAZA DA MATA GABA DAYA

Ladabi tsakaninsu da kwantar da hankalin juna. Nisantar abin da zai ta da hankalin juna. Hakuri tsakanin junansu don zama wuri daya. Jawo abin da zai faranta zuciyar juna.

Malam Barira Musa Katsina ita ce Shugabar makarantar Liwa’ul Islam Katsina

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International