Almizan :Yadda Ariel Sharon na Isra’ila ya kife ALMIZAN: Jarida don Karuwan Musulmi

Jarida don Karuwar Musulmi       Allah zai cika haskensa ko da kafirai sun ki

ISSN 1595-4471
Juma'a 22 Zulkidah, 1426                 Bugu na 697                                



 Tunatarwa |   | Tambaya da AmsaDandalin Siyasa | Hantsi A Takaice kai tsaye | Littafai | Duniya Labari 
Tattaunawa | Labarai
Duniya Labari

Yadda Ariel Sharon na Isra’ila ya kife

Daga Hasan Muhammad

Faraministan haramtacciyar kasar Isra’ila, Ariel Sharon, 77, ya kife bayan da ya samu wani bugun jini mai dan sauki da ya haifar masa da wata karamar shan-inna, abin da ya sa aka yi gaggawar kai shi asibiti a Jerusalem da yammacin ranar Lahadin da ta gabata.

Ariel Sharon, wanda yake fuskantar barazana daga yunkurin da yake yi na sake neman zarcewa a mukaminsa na Firaministan haramtacciyar kasar Isara’ila daga wasu gaggan ’yan siyasa da suka tilasta masa ficewa daga jam’iyyar Likud da ta kwashe sama da shekaru 30 tana jan saniyarta da abawa a siyasar kasar, an salleme shi daga asibitin a ranar Talata nan bayan da likitoci suka ce yana samun karin sauki.

“Gaskiya ne ya samu bugun jini, sai dai halin da yake ciki yana kara kyautatuwa,” in ji Yuval Weuss, mataimakon Daraktan a asibitin Hadassah, idan aka kwantar da shi. Ya ce, “yanzu yana magana da iyalansa da kuma jami’an ofishinsa.”

Kodayake wani Likitan da ke asibitin na Hadassah ya tabbatar da cewa Sharon yana cikin hakalinsa, amma da aka tambayi wani na daban ya tabbatar da cewa lalle Sharon ya sume, kuma ba ya cikin hayyacinsa a lokacin da aka kawo shi asibitin.

Likitan Faraministan na haramtacciyar kasar Isra’ila, Dakta Boleslav Goldman, ya karyata labarin da ke cewa Sharon ya rasa sanin halin da yake ciki. Ya ce Sharon ya san abin da yake yi, kuma yana ganawa da ’ya’yansa da kuma sauran jami’an gwamnatinsa.

Rahotanni sun bayyana cewa Sharon ya gaya wa likitocin da ke duba shi cewa yana jin dama-dama, kuma yana ganin zai wartsake nan ba da jimawa ba.

Rahoton tashar talabijin ta AL-JAZEERA daga Ramallah ya nuna cewa Sharon ya fara jin jiki ne jim kadan bayan wata ganawa da suka yi da Shimon Peres, tsohon Faraministan haramtacciyar kasar ta Isra’ila.

Wannan kifewar da Sharon ya yi, ta zo ne kwanaki uku kafin zaben da jam’iyyar da ya bari, Likud, ta yi, inda aka zabi tsohon Firaminisntan haramtacciyar kasar Isra’ila, Binyamin Netanyahu a matsayin sabon Shugabanta.

Sharon dai, wanda ya yi kaurin suna wajen kashe masu gwagwarmaya da kuma rusa masu gidaje, gami da kai masu hare-hare ta jiragen sama ba tare da la’akari da ina makamin zai fada ba, ya jadadda cewa ba a shirye yake ya sauka daga mukaminsa ba saboda wannan abu da ya faru da shi. Sai dai wasu suna ganin Isra’ilawa sun dawo daga rakiyarsa saboda tsufa da kuma rashin lafiya.

Mataimakin Faraministan haramtacciyar kasar ta Isra’ila, wanda kuma shi ne Ministan kudi, Ehud Olmert ne dai ya kamata ya rike matsayin Sharon in har ya kasa ci gaba.

Mai magana da yawun Sharon ya fadi cewa wannan abin da ya samu maigidansa nasa ba wani abu ne da zai sa a fara batun ya sauka daga kan mukamin nasa ba.

Sakataren gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, Israel Maimon da ’ya’yan Sharon biyu Omri da Gilad ne dai suka fara isa asibitin bayan an kwantar da shi da misalin karfe 8:00 na dare a gogon can.

Sharon, wanda zai cika shekara 78 a cikin watan Farabarairu na 2005, an yi masa aikin tiyata a shekarar da ya gabata sakamakon wani matsanannicin ciwo da ya samu a wani asibiti da ke garin Tel Aviv.

Yanzu dai ’ya’yasa biyu Omri da Gilad su suka fi kusa da shi sakamakon yadda Sharin din yake ta kara samun koma baya da kuma bakin jini a siyasar haramtacciyar kasar Isara’ila. Na ukunsu Gur ya mutu a watan Oktoba na 1967 bayan ya harbi kansa da bingidar babansa a lokacin da yake wasa da ita.

Sharon dai yanzu ba shi da mata, tun lokacin da uwargidansa Lily ta mutu sakamakon cutar ‘Cancer’ shekaru biyar da suka gabata, ita kuwa kwanwarta Margalith, wace ake jin ya kamata ya aura, ta mutu tun a cikin 1962 a wani hatsarin mota da ya rutsa da ita.

Hafaffen Birtaniya a 1928, Sharon dai ya samu matsala da jam’iyyar ta Likud mai ra’ayin rikau tun bayan da ya fara shirinsa na janye matsugunan Yahudawa daga Gazza watannin 12 da suka gabata, inda ya ce ya kafa wata sabuwar jam’iyya a ranar 21 ga Nuwamba da ya kira Kadima don fuskantar zaben 28 ga Maris da ke fuskantarsa.

Sun kashe Bamisiren da suke garkuwa da shi a Iraki

Daga Hasan Muhammad

Wadanda suka yi garkuwa da wani Bamisire, Ibrahim Sayyid Hilali, 46,

da ke yi wa sojan mamaya na Amurka aiki sun fille masa kai kwanaki kadan bayan sun damke shi.

Wannan kisan da aka yi wa Bamisine ya zo ne ’yan a wanni bayan Jakadan Amurka a Iraki, ya yi kira ga dakarun mamaya na Amurka da su yi ruwan wuta a kan duk wani da aka gan shi yana neman ya kawo cikas ga zaben ’yan Majalisar da aka yi ranar 15 ga Disambar da ta gabata.

Shi dai wannan Bamisiren da aka kashe yana aikin fassara ne ga sojan mamaya na Amurka da ke aiki a garin Tikirt bayan da aka kama shi aka yi garkuwa da shi.

’Yan sanda sun sanar da ’yan jaridar cewa bayan an fille kan Ibrahim Sayyid Hilali, an jefar da gawarsa a bayan garin Tikirit, inda kuma suka gane shi daga katin shaidar da ke cikin aljihunsa.

Ibrahim Sayyid Hilali shi ne na takwas daga cikin mutane kasashen waje da aka kame aka yi garkuwa da su kuma aka kashe su, kuma aika da su barzahu bayan dan lokaci. Daya daga cikinsu shi ne wani dan kwangilar tsaro Ba’amerike, wanda tini aka fille masa kai kamar yadda wata sabuwar kungiyar masu fafutika a Iraki da ta kama shi ta bayyana.

Haka nan kuma wata sabuwar kungiyar masu fafutika da ba a san da ita ba a baya, da ta kira kanta ‘Swords of Truth’ ta bayyana cewa tana tsare da wasu mutanen kasashen waje hudu, da suka hada da Ba’amerike, dan Birtaniya da kuma wasu ’yan Kanada biyu, kuma har ta bayyana cewa ta aika da su barzahu bayan an ki cika mata bukatunta na sakin dubban ’yan gwagwarmayar da ke tsare a hannun hukumomin mamaya na Amurka a Iraki.

Kodayake dai kafin cikar wannan wa’adin gwamnatin Iraki ta sanar da sakin wasu ’yan gwagwarmaya 238 da ake tsare da su a kurkukun Abu Ghraib Camp Bucc, wasu wurere biyu da ake tsare da wadanda ake gani a matsayin baraza su sama da 14,000. Sai dai gwamnatin Amurka ta nace a kan cewa ba ta saki wadannan mutanen bane don a biya bukatar masu tada kayar baya ba.

Ko a tsakiyar wannan makon ma sai da Amurka ta saki wasu mutane masu yawa da suke aiki a tsohowar gwamnatin Saddam Husani, cikinsu har da wasu mata biyu da suka yi suna, musamman a kan makaman nukiliyar Iraki, wanda da shi aka fake waje mamaye kasar da kifar da gwamnatin Saddam. “Za mu ci gaba da sakin duk wani da muka tabbatar shi ba wata barazana bane ga tsaron kasar Iraki,” in ji dakarun Amurka.

An ba da labarin cewa tsohon Magajin garin Najaf mai tsarki, Adnan Zurfi, ya tsallake rijiya ba daya bayan wani harin bom da aka ake binnewa a gefen hanya, wanda ake jin an nufi tawagar motocinsa ne. Yayin da kuma a garin Mosul wani mahara suka bindige har lahira wasu ’yan takara biyu a garin.

Sojan mamaya na Amurka hudu sun kwanta hagu, bayan wasu jerin hare-hare uku da aka kai masu a kewayen garin Bagadaza a daidai lokacin da ake tsammanin raguwar karuwar hare-haren a kan sojan mamaya bayan kammala zaben ’yan Majalisa da aka yi a makon jiya.

Dubban soja da ’yan sanda ne dai suka bazama a kan titi don fuskantar masu ta da kayar baya yayin da ake gudanar da zaben ’yan Majalisar da aka yi cikin tashe-tashen hankula.

Komawa babban shafinmu         Komawa saman wannan shafin


 Shafin Gamji | Tafsirin Alkur'ani  | Hadisai | Crescent International